← Book details Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 67

Sashe 59

Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga lokacinda Turaki yasani ta tabbata ko ganin Na'iman bazai Bari kowa yasake yiba sai ya nemar Mata lafiya,
Itakuma idan tabari ta warke sarai yanzu suna cikin gagarumar matsala sbd ba kudi a hannunsu sosai,
Komai nasu yayi qasa sbd wainnan fitintinun dasuketa faruwa
Komai tsaya Mata zaiyi.
##MAMUH#
*_Mamuhgee 52_*
A gidan zinat ta wuni tana saqa da warwara,
Ga Na'iman cikin baccin sai Dan fizgawa takeyi lokaci lokaci,
Kanta ya dauka zafi sosai ita kanta yanzu komai ya tsaya cikin kanta,
Na'iman takeson fara dawowa da ita saiti kafin tafara tunanin abin Yi akan Laylah tun kafin afara Ankara da halinda suke ciki.

Sai dare tabar gidan bayan tabawa siddika kyakkwan gargadi akan kula da Na'iman karta Bari ta fita idan ta farka.
*****Laylah ma a daki tayi wunin ranar idanuwanta sun kumbura iya qarshe sbd kukan datasha,
Gabaki daya kewa da kadaicin rayuwa takeji gashi ta kashe wayarta sbd Kiran da Abban keyi Mata cikin damuwar halinda take ciki sbd yakasa yarda da lafiyarta kalau...

Abinci ma kasa ci tayi Haka ta wuni cikin damuwa,
Gab da magriba Anne tadawo ta tadda wannan tashin hankalin sbd zazzabin gaske daya sauka ya rufe Laylah Dake dunqule a daki jikinta na rawa.

Fada sosai Anne taringa Yi Akan su halima Basu kirataba sun sanar da ita abun dayake faruwa ta dawo..

Ba Bata lokaci ko zama bataiba ta Kira dr Meenah tace ta taimaka tadawo tasake duba musu laylan.

Koda Dr Meenah ta iso da daddare jikin Laylan yayi tsanani sosai da zazzabin,
Magani aka Bata tareda tea Mara zafi Sosai
Dr Meenah na tafiya ta ringa zuba Amai a gabaice.

Damuwa sosai Anne tashiga ta Kira Turakin a waya ta sanar dashi yace a a shirya Laylan ta fito zasuje suga wani likitan.

Da Taimakon Ruky ta shirya suka fito ta kaita har jikin motar dayake zaune Yana jiranta da kansa zai ja motar Wanda rabonsa da driving bama zai iya tunawaba.

Dr Dawood sukaje ya dubata daqyau harda scanning yayi Mata ya tabbatar musu da lafiyan babyn kalau
Bp dintane kawai ya hau sai zazzabin sosai dayake damunta da rashin qarfin jiki na galabaitan datai.

Maganin bp na masu ciki yabata Suka fito Yana riqeda hannunta Suka dawo gida.

Yanayin da ake cikine kawai yasa yabarta Takoma bangaren Amma yanajin yanayinta a zuciyansa.

A Daren kusan dukkaninsu kowa kwanan damuwa yayi sbd Babu Mai cikakken dadin zuciya..

Washe gari tasamu saukin jikinta sosai saidai gabaki daya tashiga damuwa da sanyin jiki
Babu abunda takeso bayan zuwa gida ko zata samu kwanciyar hankali kafin tadawo idan mum ta sauko sbd tasan mum bazata taba Bari ahaka ba sai tayita kokarin Daukan mataki akanta shiyasa gabaki daya take cikin sanyin jiki da damuwa..

Qarfe goma na safe Anne ta nufa Sashen Na'ima sbd dubota dakuma magana da ita sbd tasan wannan Shirun nata bayan abinda yafaru bana lafiya bane.

Siddika ce ta tarba Annen cikin tsananin girmamawa tareda sanar da ita Ms Na'iman tana bacci magani Tasha sbd ciwon Kan data kwana dashi.

Kallonta Anne tayi cikin jinjina Kai tace"
Idan ta farka kizo ki Sanar Dani Zan dawo na dubata nakuma Yi magana da ita,
Allah ya sawwaqa yabata lafiya.

Amin" Siddika tace tana kokarin bawa Annen Hanya sosai ta wucewa.

Shigowar Haj Zinat yasa Annen dan dakatawa tana kallonta.

Cikin tsananin girmamawa Haj Zinat ta qaraso tana gaida Annen cikeda biyayya tana qarawa da cewa"
Na'iman ta tashi ne?

Aa Bata tashiba ance Bata jima da komawa bacci ba Tasha magani ne,
Cikin nutsuwa da bayyanarda Mahimmancin maganar da zatai da Na'ima idan ta farka Anne tace"
Zinat ki kula da Aminiyar taki sbd nasan halinta da zafi da fitina,
Tabbas akwai rashin kyautawa aciki Amma Kuma yanayin ne duk yazo ahakan sbd Babu Wanda yayi niyar cutatar da ita ko boye Mata komai,
Tun farko itace ta kawowa kanta rashin tsayawa fahimta,..

Turaki Bai boye Mata qarin aurensa ba, nikaina ban boye Mata ba saidai Kuma itace da kanta ta zabarwa kanta waye kishiyar tata
sbd azauna lafiya yasa ba'a sanar Mata ba Dan Babu Wanda ya dauka auren Mai dorewa ne tun farko
Saidai Kuma kaddara da rabo na ubangiji ba'a tsere musu,
Laifi dai anyi Mata na rashin fadar Dan Haka nakeson rarrashinta nabata hakuri duk wannan tashin hankalin zata sakawa kanta damuwane tunda bawa baya wuce qaddararsa....

Laylah Allah yayi dai Matar Turaki ce Kuma uwar yayansa........

Dan Allah kifara tausarta kafin nadawo
Ki Bata hakuri sosai sbd mum Mata laifi mun yarda Amma Inshallah za'a gyara komai....

Mutuwar tsaye Zinat tayi zuciyarta na neman Faso kirjinta tafado tsabar shiga tashin hankali da rudu
Amma dayake gwanace gurin riqe kanta sai Bata bayyanarba ta jinjina kai kawai sbd bazata iya magana ba bakinta rawa yake.

Anne na fita tayi wurgi da Jakarta da keys din motarta tareda dankwalin kanta tanajin kaman zata Ara hauka akaron farko.....

Wane mugun labari ne wannan takeji abakin Anne?

Kallon siddika tayi cikin tsananin tashin hankali tace"
Daidai naji Anne tace Laylah ce Matar Turaki???

Da sauri siddika ta gyada Kai cikin nata zallan mamakin da firgici Dan sai yanzu take sake tabbarda akwai masifa a kwance kenan idan Ms Na'ima ta tashi ta samu wannan sabon zancen.

Zama Zinat tayi tana fifita fuskarta da hannunta Dan wani zafi taji tanaji
Cikin shiga rudin tunani tace"
Tabbas Basu fada Mana cewan Sa'adah Matar Turaki shiyasa shegu tsinannu suka bar Na'iman ta tafi da Laylah wato takai Masa matarsa har gidansa......

Tun farko wane Dan burauban shegen ne Yafada Mana Sa'adahn ce Matar Turaki????" Tafada tana dago da jajayen Idanuwanta ta Dora Kan Siddika da jikinta yafara rawa tana neman zancen fidda Kai tana kokarin magana Zinat ta sauke Mata wasu kyawawan Marika guda biyu tana fizgota tace"
Dama bakida sani akai Kika kawo Mana wannan zancen kokuwa da gayya kikace Mana Sa'adahn ce?

Cikin azabar Marin datasha tafara rarraba Ido tana hawayen tsoro sbd komai zasu iya Mata tunda tafi kowa saninsu ba Imani ne dasuba musamman Haj Zinat din tunda har Ms Na'iman itake fada Mata yanda za'ayi komai.

Dukan fita hayyaci Zinat ta ringa yiwa siddikan tana cewa"
Kece Kika lalatamun komai da shirina na shekaru Dana Jima Ina fafutaka akansa,
Matsiyaci wlh zanyi lokacinki idan nagama da Laylan da Na'iman tukuna..

Tattarawa tayi tabar gidan sbd zata iya kashe siddikan idan Bata bar inda take ganintaba,
Sabon tashin hankali tashiga na musamman sbd na farkon duk Mai saukine a daukansu cikin shege ne jikin Laylan ba Turaki Dan Haka komai zaizo da sauki,
Amma Jin Laylah Matar Turaki ce yasata Shiga matsananciyar tashin hankali sbd Dan halak ne wato zata Haifa masa,
Magajinsa fa kenan??

Magajin dukiyar dasuka Dade suna shirka akanta Dan su mallaketa koba dukaba su mallaka Rabin,
Magajin dukiyar da akanta taketa durawa qawarta dasuka taso tare tun yarinta maganin data juyar Mata da qwaqwalwa ita ke controlling dinta....

Amma ace Rana tsaka wata qanqanuwar yarinya ta samesu daga sama Bayan tagama lalata mata komai na wargaza gashi sanadin hakan Turaki zai iya gano halinda Na'iman take ciki Wanda Yana ganowa tasan labarinta yaqare daga Nan Kuma...

Wlh bazata yardaba,
Komai zata iyayi dan ta tsira,
Yanzu babban burinta ta fito da Na'ima daga gidan,
Sbd sai Na'iman Bata gidan zata samu damar kawar da Laylah da cikinta daga duniya Kai tsaye sai laifin ya rataya Kan Na'iman wadda ita Kuma takardun shedar haukanta zaisa hukunci bazai hau kantaba
Dan Haka duk tsanani saita fidda Na'ima daga gidan
Kuma zata fiddatane daga gidan ta hanyar da Laylah zata daga hankalinta itama ta fito daga gidan.

Washe gari da gangan tana sane taqi zuwa gidan sai dare tazo
Lokacin Na'ima ta farka Amma Bata iya komai sai Ido datake Binsu dashi Haka ta sake sakarwa Na'iman wata allurar data sake maidata halinda ta fito idanuwanta suka rufe Takoma baccin wahala.

Fitowa dakin tayi siddika na biye da ita Saida suka zo palon ta kalli siddikan cikin bayyanarda Mahimmancin aikin da zata sakata ta kalleta tace"
Aiki Mai mahimmanci Zan sakaki
Idan Kika Bata mun aiki wannan karon Wlh yanda na maida Na'ima fin hakan Zan maida rayuwarki,kina Jina????

Gyada Kai tayi tana cewa"
Zan kiyaye Wannan karon.

Ciro qaramar kwalba daga jakar hannunta tayi tareda qaramar lighter ta miqa mata..

Karba siddikan tayi tana bude idonta akan kwalban da warin fetir ke tashi acikinta
Ta hadiye wani mugun yawu tana kallon kwalban da lighter din cikin rawar murya tace"
Wannan fetur.....

Katseta tayi da cewa"
Nafiki sani tunda nice nabaki,
Anjima da daddare ki zuba a akan gadon Na'ima Kuma ki zuba Mata kadan a jiki saiki janyota ki fito da ita daga bakin kofar dakin ki kunnawa dakin wuta,
Karki Kira jama'a sai wutar taci sosai Kuma ki tabbatarda ta shaqa hayaqin wutar saiki fita ki Nemo jama'a,
Kafin akirani idan antambayeki garin Yaya kice itace ta kunnawa dakin wuta da kanta tana cewa kunnawa gidan wuta zatai kowa ya mutu har Laylah.

Tsananin tsoro da mamakin girman rashin Imanin Zinat din da zata cutatarda Ms Na'ima sbd son abun duniya..

Cikin sake bayyanarda zata iya Mata abinda tace zatai Mata idan ta Bata Mata aiki tace"
Idan Kika aikata kuskure daya komai ya lalace wlh ke Zan cinnawa wuta kifara Isa lahiran kafin muzo.

Wucewa tayi tabar siddikan tsaye tana binta da kallon mummunan tsoro da tashin hankali...

Kasa zuwa kitchen tayi da fetir din ta nufi dakin Ms Na'iman dashi ta boye bayan Kan gadonta tana kallon fuskarta...

Akaro na farko da Tausayin Ms Na'iman ya ratsata sbd batada Mai qaunarta bare yabata shawara,
Tayi watsi da qanwar mahaifiyarta data riqeta sbd samun duniya a hannu gashi yanzu tazo tana neman Rasa komai...

Duk da Ms Na'ima Bata kyautata Mata saima izza da bossing dinta datake koyaushe Amma Bai kamata a cutatar da ita hakaba abun yayi yawa bayan arzikin dasuke ci suna Tarawa daga Haj Zinat din har ita duk qarsqashin Ms Na'iman suke samunsa...
Chapter 59 · 0% Book details