← Book details Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 67

Sashe 4

Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan tagama sallar dakin Anty Sa'adah taje ta dauka Qur'an ta nufi palon abbansu ta zauna gefensa tafara karatun al qur'an din cikin zuciyarta har akai sallar ishai anan palon tayi sallah bayan tagama taga alamar shima sallar yakeyi Dan Haka Kai tsaye ta nufa abincinsa ta zubo ta tareda zuba Masa ruwa a wani kofin ta daukosu tareda magani tadawo gabansa.

Tana Gama basa komai ta gyara Masa koina abdullahi yazo ya daukesa daga kan kujera ya maidasa Kan gadonsa Tai Masa addua ta fice shima abdullahin tare suka fito taja Masa kofa.
gurin Anty Sa'adah ta nufa Dan karatun dare datake koya Mata na littafan addini.

Acan takai kusan karfe goma na dare suna karatun kafin ta harhadawa anty Sa'adah dakin ta gyara Mata shimfidar gadonta dasuka zauna Baki taje ta dauko Mata ruwan dare datake yawan tashi Sha ta aje Mata kafin ta fito taje ta rufe gidan da koina ta nufi nata dakin tayi Shirin kwanciya tayi addua ta kwanta.

Kuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete
Mamuhgee @Arewab
ooks
*_Rabo sai Mai shi...Bata taba saka ran shigowarsa ko zama jigo a rayuwarta ba sbd kallon datake Masa amatsayin Uba,Abokin mahaifinta,Amininsa Kuma Mariqi.!_*
*_Soyayyace tashiga tsakaninsu Mai girma da qarfi batareda sun ankare da hakanba bayan dukkaninsu sun haramtawa kansu hakan,Shin ta yaya zata kalla mijin yayarta,Yar uwarta wadda ta riqeta tamkar yanda uwa me riqon 'da amatsayin nata mijin?_*
*_Qaddararsu wannan kokuwa itace rabonsa tun farko?_*
*_NOOR ALBI Hasken rayuwata_*
_Littafina dayazo muku da wani salon na dabam Wanda soyayyarsa ta kere sauran labaraina,salonsa ya bambanta da sauran,nishadinsa da shauqinsa na musamman ne_
_Fata dai ku kasance taredamu kuji zafi zafin damuka dawo muku dashi_
*_NoorAlbi#MAMUH_*
Follow me @ArewaBooks
Mamuhgee For my latest updates
*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_
*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_
*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_
*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_
*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya
*_09032345899_*https://arewabooks.com/book?id=628264fab77ff582983da456
*_NOOR ALBI_*
_*Mamuhgee*_
Washe gari tunda safe da hadari Mai qarfi aka tashi da iska
Da sauri ta fito palon ta nufa windunan dake palon guda biyu ta rufe ta nufi dakin momyn da sauri ta bude ahankali sbd karta dameta da motsinta
bakinta daukesa sallama ta shiga
Momyn na kwance kan gadon ta nufa windon dakin ta rufe ahankali ta fito ta nufa dakin anty Sa'adah itama ta rufe Mata nata windon kafin ta fito tsakar gidan lokacin iskan yaqara qarfi da gudu ta qarasa dakin abbanta ta rufe Masa koina duk da idonsa biyu bata tsayaba sbd aikin gabanta ta fito da hanzari tafara kwashe shanyar wankin momyn datai jiyan duk wasu har zun fado sunyi qura tahau kwashewa zuwa lokacin tuni ruwa masu qarfi suka sauko ta shiga ciki da sauri ta aje kayan palon Kan kujera duk da tasanma saita Kuma wanke wasu
Ta fito tsakar gidan ruwan na dukanta tahau tattara kayan dake tsakar gidan takai na kaiwa cikin takai na kaiwa Palo tasake fitowa ta taje ta bude gida sbd Kar suna ciki Abdullahi yazo basuji bugun gidansaba.

Kofar kicin ta tsaya ta kakkama gefen
kayan jikinta ta Dan matsesu tarage musu ruwan dake tsayaya ta zame Dan kwalin kanta shima ta matse daga waje ta shanyasa Kan kofar kicin din sbd Kan yasha iska Dan kuwa ta barsa da dankwalin sanyin Kan Dana dankwalin suka hadu sanyi zai shigeta ya kwantar da ita
Babu ciwon Dake tsananin azabtar da ita kamar sanyi idan yashigeta
Gashi kwantawarta ciwo ba kyau
Wuya takeci Mai tsanani Dan duk rintsi saitayi aikin dake kanta ga abbanta idan ta kwanta batada Mai kulawa dashi Dan hakan nema take dannewa duk girman ciwo sai idan yafi qarfinta Dan Haka takeda kiyayewa akan lafiyarta.

Risho ta kunna ta Dora ruwan zafi ta hada qullun kunun alkamar dazatawa Abban Takoma ta zauna Kan kujera tana jiran su tafada wani irin sanyin ruwan da ake Yana ratsata tanaji.

Ba jimawa ruwan suka tafasa ta hada kunun ta zuba Masa a flask dinsa ta rufe ta juyewa Anty Sa'adah sauran a flask itama sbd tanashan kunu sosai itama musamman nata dayake da Madara take shansa sbd lafiyar fata Inji momy.

Cikin ruwan takuma fitowa takaiwa bbanta ta basa Tasha tabasa magani ta goggoge Masa jiki ta fito Yana binta da kallo yanda take jiqe sharkaf sai Kama jiki take karta jiqa Masa daki Takoma kicin tahau aikin abincin karin kumallonsu momy.

Dakin Sa'adah taje cikin rashin son takurata daga baccin datake tace"
Anty Sa'adah me za'a dafa na Karin?

Cikin bacci Sa'adah ta juya tana sake shigewa Dan madaidaicin bargonta tace"
Laylah duk abinda kikai Amma dai karki manta da kunu na.

Anty Sa'adah jiya Momy bataci abincin dareba sosai Naga abincin yayi saura ko ulcer dinta ya tashine saina dafa Mata ruwan tea da faten dankali kawai.

Kimata duk yanda kikai kaina na ciwo bacci nakeji sosai.

Juyawa tayi Takoma kicin din tahau aiki.

Wani maganin ulcer din momyn tafara dafawa Mai wuyar dahuwa Haka taita jira har yayi kafin ta dafa taliya Mara yaji ko kadan sbd momyn ta juye a kula ta zuba Mata maganin a babban kofi ta saka Mata a fridge duk da Babu wuta zaiyi sanyi sbd ruwan sanyin Dake ciki.

Tana gamawa anan kicin din taci abincin sama sama tagama tai wanke wanke ta sharesa tsaf ta fito lokacin ruwan sun Dan rage sosai sai Dan yayyafi ta nufi dakinta tacire kayan jikinta ta watsa ruwa ta sauya zuwa wata atampar tafara gyara nata dakin fes ta fito tafara aikin gyaran palon tana gamawa tashiga na mum tayi Takoma na anty Sa'adah tayo tafito tsakar gidan shima Tai Masa tas kafin ta fita tasamo garwashi maqota tazo tayi turaren wutarda momyn qaidane sai anmata shi Dan tanason qamshi.

Gurin abbanta ta nufa ta gyare Masa koina taje ta dauko Dan sauran burbushin hayaqin turaren daga palon Momy takawo Nan dakinsa shima yasamu Dan qamshin ko yayane,
sai alokacin ta zauna gabansa bayan ta aje kaskon turaren cikin kulawa a natse Tai Masa Ina kwana tana kallon idanuwansa dasuka qanqance Suka sauya launi da alama Bai samu bacci ba ta dauko ruwa tasake bashi yasa cikin kulawa a natse tabude Baki tace"
Abba?

Akwai wani matsala da kakeji ne?

Saida ya Dan hadiye yawun dayake hadiyewa da dabara daqyar shiyasa shi nasa ciwon baya zubarda yawu ta gefen Baki Allah ya taimakesa saboda saukin dayake samun Yana iya hadiye yawu.

Dan rintse idanuwansa dasukai laushi yayi ahankali alamar yanada damuwa.

Faduwa gabanta yayi da qarfi saidai fuskar Bata nuna hakan
Ta zuba Masa fararen idanuwanta batareda ta iya cewa komaiba.

Hannunsa Dake rawa da gyangyadi yadan daga yayi Mana alamar karta damu bayajin ciwon komai.

Shiru kawai tayi Dan batasan Mai zataceba bayan jurewa ta boye damuwarta sbd ko nacewa tayi tasan abinda yake damun nasa Babu abinda zata iya Masa bayan tashiga qunci da damuwa sai addu'a da take Masa.

Shiru sukai daga ita harshi Dan ko Dan zancen datake Masa wasu lokutan takasa sbd mutuwa da jikinta yayi dakuma damuwar datashiga yanzu din akan yanayin nasa tasan Dole Kam akwai abinda yake damunsa tsakanin jiya zuwa yau din.

Ganin gwara ya kwanta kozai samu baccin yazo Masa yasa ta tashi ta tura kujerarsa har bakin gadonsa da kanta ta mirginasa zuwa Kan gadon ta gyara Masa kansa akan pillow ta rufe Masa Rabin jikinsa sbd akwai sauran sanyi sosai na ruwan saman da aka gama ta bude Masa windows Dan iska da Sanyi na shigo Masa ta fice Takoma dakinta itama ta zauna jigum sbd Haka tata rayuwar take.

Sai qarfe kusan goma Sha daya saura momy da anty Sa'adah suka fito dayake komai takawo musu palon na Kari suka zauna karyawa
Ita Momy tuni tayi wanka kafin ta fito.

Motsinsu yasata aje littafin datake karatu na koyan wasu abubuwan addini da anty Sa'adah tabata ta aje gefe tareda miqewa ta fito.

Bata tsaya ba kicin ta nufa ta dauko maganin data dafawa Momy Kai tsaye ta juyo tadawo palon cikin tsananin girmamawa ta qaraso gabansu ta aje kofin maganin gefen Momy anatse da biyayyarta tace"
Barka da fitowa Momy.

Ga magani andafa na ulcer dinki naga
Kamar zafin jiya ya tada Miki ita.

Batareda ta kalli gefenba ta dago ta kalli Sa'adah dake kallon Laylan cikin tsananin qaunarta kafin ta kalli Momy tasaki murmushi tana sake maida kallonta ga Laylah cikin sakewarta tace"
Laylah kinfi kowa sanin Momy da iya kulawa da ita.

Miqewa laylan tayi tabar gurin ta nufi kofa ta fice tsakar gida tana Kama hanyar kicin Dan Dora abincin Rana Dan kuwa tasani ko shekarun duniya zatai agurin ba tankawa Momy zataiba hakama ire iren wannan son cusata agurin momyn da anty Sa'adah keyi tana iya gani akan fuskar momyn tado Mata da tsananin dacin Dake zuciyarta na shekarune kawai takeyi shiyasa anty Sa'adah na farawa take ficewa Dan dama idan ba aikin doleba Bata tsayuwar data wuce minti biyu agurinda momyn take tunda momyn ta bayyanarda rashin son hakan qarara tuntuni.
Chapter 4 · 0% Book details