← Book details Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 67

Sashe 19

Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Laylah nakomawa daki zaunawa tayi tunda basuda abin Yi ga Sa'adah ba damar samun Momy a waya bare takira suji duk da kila Basu isabama
Qarshe dai Kawu suka Kira suji koya Isa din shima tunda shima a ranar ya wuce da nasa tarin Sha Tara ta arzikin da Turaki yabasa Wanda sai lokacin daya tak ya sawa dangin Momy albarka dasuka kirasa yazo Dan son ransu gashi shi gaba takaisa Dan kuwa yasan Inshallah shi da rashi sunyi hannun Riga Dan babbar sanaar zaije yafara da abin daya samo din.

Kawun bai Isa nijar ba Amma suna Hanya Dan Haka sama sama yakuma musu Yar nasiha tareda gargadi Mai girma akan su maida hankali ga karatun da za'a sakasu Dan iyayensu suyi alfahari dasu idan suka dawo.

Sai bayan sallar magriba aka kawo musu kayan dogayen jallabiya marasa nauyin adon stones ko wani abun daban sukai wanka akai musu ison fitowa cin abinci suka sauko Sa'adah ce agaba Laylah na bayanta.

Dining room aka nufa dasu aka Basu gurin zama a kujerun dining din
LAYLAH ita aka bawa wadda ke facing ta Anne sbd sanin itace Matar gidan sai Sa'adah da aka bawa ta gefen Anne din alamar itakuma 'ya kaidar zaman dining kenan.

Laylah data dauka hakan amatsayin kusancin alaqar Mata da sirikane yasa Sa'adah ke zaune gefe ahankali ta furtawa halima data ja mata kujerar data zauna "Nagode"
Abinci kusan kala biyu ne sai drinks da fresh milk da kayan plates dasu Tumblrs ke jere a fadadden dining din da Air-cooler ke facing dinsa suka fara cin abinci Banda Laylah data kasa sakewa sbd rashin sabo
Dan a gida tasaba tsaitsaye takecin abinci sbd tarin ayyukan gabanta Bata iya cin abinci Haka.

Lura da yanayinta yasa Anne kallonta da kulawa tace"
Laylah?

Lafiya ko?abincin baiyi bane a kawo wani?

Ahankali ta girgiza Kai tareda Kai hannu anatse tadauki spoon cikin cutlerys Dake gefen plate dinta tasaka cikin lafiyayyar fried basmati rice dataji veggies da nikakken Naman rago da spices na qamshi tafara ci ahankali.

Anne wayayyar tsohuwar Yar boko ce data Gama jiquwa acikin daula da hutu tareda rayuwar yanci Dan Haka batada wahalar zama saidai tsayayyar mace ce da Bata daukan shirme ko shiririta tareda zancen banza Dan Haka duk Wanda yasanta yasan Yar kaifi daya ce Dan Haka Dole Sa'adah ta tilastawa kanta sakewa tareda tilasta Laylah wadda tasan bazata Saba da mutane lokaci dayaba sbd yanda ta taso duk da hakan tanata nanata Mata sakewarta cikin mutane nada amfani.

Kwana daya sukai da wuni daya a gidan aka kawo wasu irin tarin kayan suturar sawarsu da abubuwan buqatarsu Wanda yasa Sa'adah kasa daina mamakin rayuwar gidan Dan kuwa hatta skin products set na kayan gyaran fatar jikinsu kusan kowa da kalar nasa fatar Haka aka siyo musu set set tunda ba kalar fatarsu dayaba Laylah tafita haske sosai.

Kaya kuwa bazasu iya gane iya adadinsuba Amma Kam sunada yawa Saida suka Kuma kwana daya sashen Anne kafin aka Ware musu babban shashe a gidan maqale da sashen Anne Wanda yake hade Dana Anne din Dan akwai palonda zai kaika Kai tsaye palon Sashen Annen daga nasu palon,
Palone Wanda yaji gyaran English royal set na komai blue and milk,
Kayan Dake palon ko Haj Karima da ake gani wadda tafi kowa a dangin Momy kaf gidanta Babu kayan dasukai kyawu da tsaruwar wainnan kayan,
Qatuwar TVn Dake palon tana aiki Laylah ta kalla tana sauke numfashi Dan said yanzune zata Dan sake da aka barsu suka dawo Sashen anty Sa'adah,
3 bedrooms ne apalon sai dining area da kitchen,
Babu abin Jin Dadi da Babu a Sashen Dan Haka Kai tsaye aka kaiwa kowacce kayanta makeken dakinta.

Kallo Sa'adah ta wuni Yi ranar bayan sungama cin abincin rana tareda Anne wadda yau ta fita,
Ita Kam Laylah aikin zama kallon Sa'adah tayi wadda take harta fara sauyawa da sakewarta.

Sai dare Anne tadawo Dan Haka can suka tafi sukaci abinci
Suna gamawa suka dawo sbd Anne a gajiye take shigewa tayi kawai Dan hutawa.

Ahaka ba sakawa ba fitarwa sukai sati biyu a gidan
Bayan cin Mai kyau da Shan Mai kyau su kwanta suyi bacci cikin AC da gado Mai taushi Babu abinda sukeyi
Har gwara Laylah da Bata Saba da zaman hutun ba Dole tasaka kanta fara Shiga cikinsu halima tana tayasu aikin Abinci
Anne dataga Kamar hakan na Bata nutsuwa sai Bata hanata ba Amma Kam su su halimar ba ruwansu tsananin girmanta suke Bata duk da gargadi da umarnin da Anne ta bayar na Kar Wanda yasan LAYLAH ce Matar gidan.

Ko ba'a fadaba sauyi yazo musu
Fatarsu ta bayyanarda hakan Dan kuwa tuni fatar kowannensu tafara wankewa dayake dama can tunda ba yawo sukeba anyhow sunada kyan fatarsu musamman Laylah da zaman gida da rashin fita yasa fatarta koyaushe a lafiye take Dan Haka sai taqara washewa sosai.

Sa'adah kuwa ba damuwa sabuwar rayuwa ta bude a gidan musamman kullum tana Kiran Momy suji yanda jikin Abban yake
Momyn dai har lokacin taqi cemata komai akan Abin daya farun Dan kuwa yanzu ita tagama shiga shock na mutane dakeson kasheta da qarfi da yaji.

Psychologist ta musamman ce take zuwa gida suna hadawa da therapy gurin kokarin dawo da Laylah daidai dan kuwa yanayin depression data Shiga yasa Sam sam tanada matsalar sabo da mutane ko kadan Dan Haka kafin maganar karatunsu hakan Anne taga yafi.

Babban cigaban da aka fara samu shine Dr Meenah wayayyar macen datasan me takeyi da Laylahn tafara dan sakewa da ita
Aikuwa hakan ba qaramin farin ciki yasaka Sa'adah ba da Anne.

Ms Na'imah wadda tabi Turaki Lagos Dan zai koma tun washe garin ranarda su Annen suka dawo batareda tasan abinda akayo Mata ba sai data cika wata biyu da sati daya a Lagos cif kafin tadawo Abujar.
##MAMUH#
*_SAKINA VENDABLES_*
*_Ina ma'abota son qamshi da gyara?

Ina masoya qamshi dasuka San darajar qamshi da gyara irin na qamshi?_*
*_To kuzo ga SAKINA VENDABLES Tasake zuwar muku da ingantattu Kuma tsararrin kayan qamshi masu kyau da qarko,_*
*_Ga wainda suke buqatan turarukan gaske masu kyau na asalin qamshi da Kama jiki da Kaya suzo ga inda aka tabbatarda kyau da qarfinsu a gurin SAKINA VENDABLES_*
*Turaren wuta list*
Queens special
Kajiji mix and r
Kajiji whole
Gabgab
Brown Hawiii
Special Halut
Sandal balls
Sandal strips
Sandal flakes
Dubai oud
White Hawii
Classy Dufr
Black bange
Black bange
Musky Dorrot(Na tsuguno)
Cous cous
Khumra White & Black
*Kulaccam* Black(for hair) white (for body)
Handles *Instagram* @sakina_vendibles *Facebook* @Sakina vendible *Tiktok* @Sakina vendibkes
08106974073
Follow me @ArewaBooks
Mamuhgee For my latest updates
*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_
*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_
*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_
*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_
*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya
*_09032345899_*
*KATIN MTN*
09166221261
*_Mamuhgee 17_*
Duk yanda Ms Na'ima taso Kar tayi kishin Sa'adah kasawa takeyi saidai kamar yanda Haj Zinat ta fada Mata dannewa kawai takeyi Bata wani nunawa saidai ko inda Sa'adah take Bata kalla sbd duk iya qanqantawa tagama daukan Sa'adahn a qasqance ganin harda ilimin boko Mai qarfi sosai Bata dashi Dan Haka sai sukafi maida hankali akan Laylah wadda cikin kwanaki kadan Ms Na'ima din tagama fahimtar irin kaunar da Anne ke yiwa Laylah ga laylan nada wuyar sakin jiki da mutane Dan Haka tuni ba itaba ba Haj Zinat ba suka maida hankali sosai Kan nunawa Laylah kulawa Sosai,
Musamman Ms Na'ima ke janta ajikinta tana Mata siyayyar kayan Yan gayun 'yan Mata 'yayan manyan duk da Anne Babu abinda Bata siya musu na duk Wani abun buqata Amma dayake Ms Na'ima wayayyar Yar gayun gaske ce sai siyayyar datakewa laylan yana sake wanke Laylan
Anne said kawai takawo ido tasake sakawa Na'ima Dan tagama gane manufarta ta son abata Laylan Dan samun damar data fi wadda take da ita yanzu Alan dukiyar Turaki,
Murmushi kawai takeyi na ganin wautar Na'ima so da dama idan taga yanda suka taqarqare akan Dole qaunar Laylah sukeyi ba
Kuma ganin rashin sanin zaisa bazata taba cutatar da Laylahn ba ayanzu Dan Haka saita bar komai ahakan yanzu saima tabada fuskan da Ms Na'ima din ke daukan Laylah tana fita da ita.

Laylah Bata sakewa da Ms Na'ima Sam ko kadan sbd sanin matsayinta na kishiyar Sa'adah batason jawowa Sa'adah matsala sai Anty Sa'adah din ta nuna Mata bakomai ai hakan shizaisa azauna lfy kowa da kowa,
Da Haka Ms Na'ima taja Laylah sosai jikinta har Dan Dole Laylah tafara sakewa da ita Dan har cikin ranta so take ta cusa qaunarta Mai qarfi a zuciyar Layla ta yanda zata dauketa tamkar uwa tako Ina yanda Turaki zai sake musu komai yanda yakamata tunda ta rungumi 'yar Kamar ita ta Haifa.

Sa'adah tafara zuwa makaranta tuni a one hundred level takuma farawa tana karantar Biology
Kuma ba laifi tafara sabo da makarantar da 'yan friends din data fara tsirarru ga uwa uba surutu da manyan designers Kaya data duka
Ga hankalinta tuni yagama kwanciya Dan Laylah tasamu lafiyarta cikakkiya itama karatun zata fara Amma Ms Na'ima ta dage akan ita baza'a sakata anan Abuja ba da ita zata tafi USA acan zata sakata karatun kafin su tashi dawowa Laylan tagama Inshallah idanma harta tashi dawowan Laylah Bata kammala karatun ba zata jirata ta kammala kokuma tabarta acan tadawo tunda Turaki na can ga maids a gidan Kuma.

Da wanna ba musu Anne ta Amincewa tafiya da Laylan wadda da farko ta daga hankalinta Amma Sa'adah ta lallasheta tareda sanar da ita Anne tace acan kusa suke da gurinsa Abba zaa ringa kaita tana dubo Abba da Momy tarea Bata qwarin gwiwar karatun shine zai tallafi rayuwarsu data iyayensu Inshallah Dan Haka badan tasoba Haka ta amince musamman da Anne ta zaunar da ita ta rarrasheta Akan Turaki nacan Dan Haka kartaji tunda yasan matsayinta akansa na dolenta.

Hakama dai maganar ganin abbanta shine yafi komai Bata nutsuwa da tafiyar wadda takasa gane dalilin dayasa Ms Na'ima ke sonta Haka Bayan ita din qanwar kishiyarta ce Amma idan ta tuna wasu daga nasihun Anne sai tana yadda da akwai sauyin da Allah ke kawo maka na rayuwa da basai ka tsaya wani tunaninba Bayan gode Masa.
Chapter 19 · 0% Book details