← Book details Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 67

Sashe 29

Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana kokarin baro dakin taje ta sanar da siddika tazo ta tayata kada 'yar Mutane ta mutu a hannunta ita kadai bayan ta fito dakinsu saitaji doorbell na tashi ahankali ta kalli hanyar zuwa kofar gabanta na faduwa da karfi
Ta juya ta kalli makeken agogon dake palon taga lokaci sai kawai ta juya zata nufi hanyar komawa daki wayarta Dake hannunta tayi haske tana vibrating da sauri ta daga ta duba ganin sunan A Abdoul yasata dauka da wuri har jikinta na rawa.

Kai tsaye yace ta bude Masa kofar shigowa ya kashe wayar.

Da sauri takuma juyawa ta dawo ta nufi kofar ta tana zuwa ta bude ganinsa tareda Dr Noah da wata nurse yasata matsawa tabasu hanya Suka shigo
Ya kalleta kafin ya kalli siddika data fito itama tana kallon kowa cikin tsoron menene yake faruwa yace"
Ki shiga dasu gurin Ms Laylah.

Juyawa tayi suka bita
Ya maida kallonsa kan Cindy Yana magana da ita Dan tunaninsa yagama basa abinda yafaru Dan Haka ya sanar da ita zata kulada Laylahn sosai batareda ya sanar da ita abinda yake damun Laylan ba.

Sosai Dr Noah ya duba manyan raunikan da Laylah tasamu yayi Mata treating dinsu tareda taimakon nurse dinsa kafin yayi Mata allura yabar nurse din zata kwana anan harsai da safen idan Laylah tasamu kanta.

Allurar da Dr Noah yayi Mata yasa ciwon datake ji suna Dan raguwa sai jikinta yaqarasa sakewa ta lumshe idanuwa bacci ahankali ya dauketa a wahale.

Guestroom aka Kai nurse din suka barta tunda tasamu bacci tareda kashe wuta da rage Mata AC.

Bata farkaba sai qarfe Takwas na safe ta bude jajayen idanuwanta tareda motsawa kadan tana kallon dakin dake qamshi alamar har Cindy tashigo tayi gyaransa.

Ahankali ta dafa ta tashi zaune tareda zuro qafafuwanta qasa ta miqe tsaye tafara takawa ahankali ta shige toilet tana shiga ta shige ruwan zafi sai alokacin ta Dan saki numfashi tana rintse ido tareda Hana kokarin Hana kanta tuna komai Dan kuwa tsautsayi ne kawai zata iyace ya gifta Wanda har abada bazasu tunawa,
Bazata Bari zuciyarta ko gangar jikinta ta tuna komaiba game da wannan Kota halin Yaya.....

Hawayen datake riqewane suka balle Mata takasa riqe kukanta tasake kukan tana qanqame jikinta Dake amsa radadin duk wani cakuda da kisses dinsa dake yawo jikinta.

Ta Jima a toilet saidatayi kukanda Babu Mai rarrashi ko Wanda zata iya fadawa wannan qaddararren tsautsayin kafin ta fito idanuwanta da fuskarta a matuqar kumbure ga wani ja datai na kukan.

Towel ne ajikinta ta fito kanta na tsayayyar ruwa
Lafiyayyar fararta sai sheqi takeyi kanta a qasa yake jikinta amace ta nufi bakin gadonta zata zauna ta huta sbd gajiya da rashin qarfin jiki.....

Qamshin daya doki hancintane lokacinda takai tsakiyar dakin yasata dagowa ahankali jikinta na sake mutuwa ta kalli inda take jiyo qamshin idanuwanta na sake fidda tsananin mutuwar jikin datake ciki....

Tsaye yake sanye cikin farar jallabiyar data bayyanarda wani Hasken daya qara Wanda ke bayyanarda bayajin dadin shima Amma ba'a wani ganewa, sauraron nurse da zata tafi yagama Yi kafin ya dago oily eyes dinsa da har lokacin Basu Gama dawowa daidaiba yayi Mata kallo daya ya dauke idanuwansa Yana juyawa ya fice Dan ganin yanayinta na rashin kaya sbd towel din jikinta qarantarsa Tayi yawa gashi rashin qarfin jikinta yasa takasa dauresa dakyar riqe kawai take dashi saman saman kirjinta Yana Dan bayyana.

Jiki mace ta iya saka Riga Mara tsayi Takoma tasanya jallabiya tayi sallah a zaune kafin ta lallaba ta koma gado tana kokarin kwantawa aka shigo Mata da breakfast batada apatite Amma Sbd magani da zatasha Dole Tasha tea da kidney sauce Mai kwai aciki Tasha maganin Takoma ta kwanta wani baccin yakuma daukanta.

Sai yamma ta farka lokacin zazzabinta ya Dan rage Amma dai tana Jin pains kadan kadan ajikinta Dan Haka takuma komawa tasakarwa kanta ruwan zafi.

Wayarta a kashe ta wuni Kuma Bata kunnaba Saida takwana biyu zuwa Lokacin taji sauki ba laifi tana iya fitowa daga bedroom dinta Amma iyakacinta kitchen kokuma qaramin palo wadda bazata hadu da Wanda batason haduwar dashiba.

Kwana biyu tasake samun sauki sosai suka koma school Dan Haka ta fara fita school ta rage zama gida Sosai sbd mum Na'ima Bata dawoba har lokacin,
Abin daya faru tsakaninta da Abban ta dannewa zuciyarta ta Hana kanta tunawa sbd ta dauka hakan babbar qaddara wadda tariga ta faru tunata kamar tunawa kanta kuskuren dayariga ya faru ne Dan Haka ta danne ta talastawa kanta Yi kamar Bata tana sanin wani abin makamancin hakan ya faruba ta saka kanta zama busy Sosai a karatu
Danma kada ta bar duk wani tunanin dazai tunatar da al'amarin saita sake sosai tana yin rayuwarta Kamar koyaushe acikinsu Cindy.

Sai Bayan sati biyu Mum Na'ima ta dawo gidan lokacin Bata Nan tana dawowa school taganta wani irin Abu taji Yana bugawa a zuciyarta na tsananin kunyar Mum Na'ima din Mai tsananin qarfi da baqin cikin kanta Dan kuwa sai tanajin kamar ta zama babbar butulu saidai tayi alqawarin qin saka zancen wannan al'amarin cikin kanta Dan Haka ta qaraso da murmushi a Kan fuskarta da murnar ganin mum din ta rungumeta kamar yanda ta ware Mata hannu tana cewa"
I'm back princess.

Murmushi tayi Mai sauti tana cewa"
We miss you mum.

Dariya Mai sauti Ms Na'ima tayi ta farin ciki Dan kuwa da farin ciki ta dawo sbd abinda sukaje Yi sunyi komai cikin Jin Dadi yanda sukeso na kasuwancinsu tace"
Nayi kewarki sosai My baby keda Abbanki gashi nadawo shima bayanan tun last week Yana Nigeria yatafi.

Dan murmushi tayi tana cewa"
Mum lemme go and freshen up, I'm morethan tired.

Bedroom dinta ta Isa ta tube tafada toilet tayo wanka ta fito ta shirya cikin qaramar Riga mara nauyi da skirt tayi sallah ta fito ta nufi kitchen ta hado Krispies tafito tanaci ta zauna tareda mum din daketa Mata labarin boutiques da sabbin shagunanta da za'ai launching.

Da daddare tare sukaci abinci a dining Kamar yanda aka Saba tunda mum din tadawo Kuma qarin samun nutsuwarta a dining din daga ita sai mum din Dan Haka har fira sukai sai 10 ta shige tayi wanka ta kwanta.

Da anty Sa'adah sukai waya wadda take fama da Dan rashin lafiya kwanakin Amma dai tasan bazai wuce stress na karantun datake Shirin kammalawaba,
Tunda wannan abun yafaru da ita Bata iya waya da Anne sbd wani irin nauyi Mai girman gaske takeji duk da tasan har abada Babu Wanda zaisan hakan ya faru Amma ta kasa Hana kanta Jin tsananin nauyin Annen,
Annen da kanta take kiranta Amma hakanan sai Bata wani Gane Kan Laylan sbd yanda take magana cikin rashin sakewa bayan suna murnar lafiyarta data Dade da samuwa saidai Bata damuba sbd tasan bazai wuce yanayin jiganiyar karatuba itama.
##MAMUH#*_Mamuhgee 26_*
Dawowar mum Na'ima yasa takoma dawowa gida yanda ta Saba gashi dama kwanakin wunin a waje na Dole ne sbd Bata wani sabawa kanta da yawo sosaiba gashi gabaki daya ta Rasa asalin kuzarinta na zamtowarta budurwa duk ba Wanda yasan hakan,
Mum Na'ima itama kwana biyu dayake tana cikin farin ciki sosai Haka suka ringa yawon shoppings Dan kudi tasake karba daga gurin A Abdoul sbd wannan karon ba dashiba Turaki yaje Nigeria wani aiki ya tsaya Yi,
Sosai Laylah itama ta qaro kayan sawarta dasu handbags da tarin takarma da kayan turare dukda tanadasu har wainda batai amfani dasu ba Amma Haka taqara lodo wasu gashi suna Shirin zuwa Florida wani program na wata daya.

Kwana biyun tasakewarta tareda manta komai tunda Abban ma bayanan,
Daga kitchen ta fito sanye da doguwar Riga har qasa ta sallarta data fito bayan Gama sallarta batareda ta tube rigarba sbd gajeran wandone a jikinta da farar armless top.,
Abincin dare suka Gama Wanda yau harda ita akai aikin Dan Dama idan tana gida Bata komai itace ma Mai abincin wasu lokutan,
Bedroom dinta ta nufa tafara zare doguwar rigarta kafin ta nufi toilet tayo wanka tana fitowa tafarayin sallar ishai tagama ta saka Riga da wandon Enamor na bacci masu Dan kauri red color sai hular rigar data janyo ta rufe gashinta dayake zuba sheqi a daure da black band.

Wayartace kawai a hannunta ta nufi dining room hankalinta nakan wayar tana duba saqon Sofia fuskarta daukeda murmushi harta qaraso tana kokarin zama ta aje wayar tareda dagowa ta sbd qamshin dataji yakamata dakin cin abincin idonta ya sauka Kan kyakkyawar fuskarsa datai wani irin fresh gashin kansa ya kwanta sai sheqi yakeyi yana sanye cikin fararen Kaya tas bayan slippers dinsa dake baqaqe hatta Dan qaramin Rolex watch din Dake hannunsa fari ne Bai dagoba abinci yakeci cikin nutsuwa da kamewa
Ahankali ta dauke idanuwansa daga kansa bugun zuciyarta na neman sauyawa ta waiwaya gefen Ms Na'ima dake zaune tana kokarin fara cin abincin cikin wata Kuwait gown Brown sai shining na stones ke tashi fuskar fes da kwalliya alamar tasan da dawowar Turakin yau ta sauke idanuwanta qasa ahankali batada damar juyawa Dan Haka taqarasa zaunawa a natse cikin girmamawa tace"
Ina barka da dawowa Abba.

Ruwa yadauka yafara Sha kafin ya aje ya dago cikin nutsuwa da kamewa yayi Mata kallo daya da idanuwansa dasuka kusa sanyata zuba macaroni din data debo a serving spoon cikin cup din juice,
Yauwa barka ya school?

Alhmdlh ta furta batareda ta dagoba.

Cin abincin sukeyi kowa cikin nutsuwa da Sanyi
Itace tafara gamawa tana kokarin tashi tsaye ta saci kallonsa taga gabaki daya hankalinsa Yana Kan abinci dayake ci a natse ba wani garaje.

Tana barin dakin cin abincin ya dago fararen idanuwansa ya kalli kofar data fice kafin yaci gaba da cin nasa abincin,
Bayan Gama cin abincinsu sama ya Haye Kai tsaye Ms Na'ima kuwa dakinta Takoma sbd bacci takeji yau bazata Kai Masa firaba gashi Daman idan yayi tafiya ba'a damunsa sbd Yana buqatan hutawanda gajiya.
Chapter 29 · 0% Book details