← Book details Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 67

Sashe 18

Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shigowa Kawun yayi Suka zauna Palo daga momyn sai shi sai Anne wadda kai tsaye tafara magana da cewa"
ZAINAB kamar dai yanda Kika sani Allah Yana jarabtan bawansa ne Dan gwada qarfin imaninsa Dan Haka ki dauka komai na rayuwa na samu da rashi dakuma wasu sauyin duk cikin jarabawa da qudirar ubangiji ne,
Kamar yanda kikafi kowa Sani da shaidawa idan rabo ya rantsa tunda ga Laylah Nan Kin gani ishara
Hakane yakuma faruwa auren da aka daura jiya da Laylah aka daurashi sbd itace da haqqin hakan kin sani
Dan Haka idan da ansaka son Rai an daura da Sa'adah to wlh matuqar akwai rabo tsakanin Turaki da Laylah wannan Rabon saiya kashe Sa'adah ta rasu Dan kawai ayi auren a haifosa yazo duniya Dan Haka mudai munyi adalci kamar yanda Sa'adah da kanta tazo tafada Kuma ta roqemu akan hakan sbd hakan dai shine daidai,
Zainab ki godewa Allah daya Baki 'ya kamar Sa'adah wadda wlh samun 'ya kamarta ayanzu Abu ne Mai wuya,
Tayi hankali sosai nakuma yaba Mata iya yabawa shiyasama Zan tafi da ita a hannuna na dauka riqonta da yardar Allah harsai Mahmoud yasamu lafiya Inshallah.

Wani irin kuka Mai sauti da shiga Rai Momy tasaki tana rufe fuskarta da tafukan hannayenta dake wata irin rawa.

Shiru sukai dukkaninsu sbd Bata damar kokawa Dan sunsan hakan akwai tsananin ciwo
Tana ganin ta aurar da 'ya yanzu Ana fada mata ba wani aure.

Kuka takeyi sosai wanda yasakawa Anne tausayinta tafara Mata nasiha da rarrashi har zuciyar momyn ta Dan Yi sanyi Amma Kam wani nauyi da 'daci sun Riga sun dasa Mata shi Dan Haka share hawayenta kawai tayi batareda ta dago ta kalli Annen ba murya a cikin yanayi na sanyi da 'dacin zuciya tace"
Nagode nakuma bar Sa'adah a hannunku.

Jinjina Kai Anne Tayi tana sake Jin tausayin momyn sbd bayan qunci da baqin ciki Babu abinda yake zagaye da rayuwar momyn tsayin shekaru
Dan Haka tana Mata fatar samun budaddiyar zuciya Nan gaba.

Kasa ganin Sa'adah Momy tayi Dan bazata iya hada idanuwa da Sa'adahn ba Dan Haka Kai tsaye fice ta shige mota suka wuce airport
Suna Isa jirginsu ya daga.

Bayan tafiyar Momy da awa biyu Suma masu jirgin ya daga Wanda yasaka daga Sa'adah har Laylah cikin wani mugun yanayi Dan kuwa Babu Wanda yataba ko barin gari acikinsu bare Hawa jirgi har gwara Sa'adah tana Dan yawan tafiya wasu lokutan tareda umma Jamila kokuma Haj Karima Amma ba Wai tafiyar nesaba.

Tafiyar awanni sukai sai gasu a garin Abuja inda manyan Mercedes beymach ke jiran saukarsu Aka daukesu zuwa *_AB TURAKI RES_*.
##MAMUH#
*_SAKINA VENDABLES_*
*_Ina ma'abota son qamshi da gyara?

Ina masoya qamshi dasuka San darajar qamshi da gyara irin na qamshi?_*
*_To kuzo ga SAKINA VENDABLES Tasake zuwar muku da ingantattu Kuma tsararrin kayan qamshi masu kyau da qarko,_*
*_Ga wainda suke buqatan turarukan gaske masu kyau na asalin qamshi da Kama jiki da Kaya suzo ga inda aka tabbatarda kyau da qarfinsu a gurin SAKINA VENDABLES_*
*Turaren wuta list*
Queens special
Kajiji mix and r
Kajiji whole
Gabgab
Brown Hawiii
Special Halut
Sandal balls
Sandal strips
Sandal flakes
Dubai oud
White Hawii
Classy Dufr
Black bange
Black bange
Musky Dorrot(Na tsuguno)
Cous cous
Khumra White & Black
*Kulaccam* Black(for hair) white (for body)
Handles *Instagram* @sakina_vendibles *Facebook* @Sakina vendible *Tiktok* @Sakina vendibkes
08106974073
Follow me @ArewaBooks
Mamuhgee For my latest updates
*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_
*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_
*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_
*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_
*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya
*_09032345899_*
*KATIN MTN*
09166221261
*_Mamugee 15_*
Koda suka iso Turaki na gida sbd Ganin Daya daga cikin motocinsa _Rolls Royce phantom_ baqa pake a hanyar daf da Shiga sashensa hakama ganin A Abdoul a harabar gidan yasake tabbatarda hakan sbd idan Yana gidane kawai kake ganin A Abdoul.

A Abdoul da sauran masu aikin sashen Anne ne suka fito tarbanta tareda daukan kayan da akazo dasu duk da bawasu Kaya bane daga qaramar luggage din Anne sai handbag dinta su Sa'adah da laylah akwati dayace sukazo da ita na iya sabbin kayan da aka dinkawa Sa'adah sai kayan Laylah guda biyu aciki itama sababbin da Anne ta Bata dinne Kai tsaye aka karba komai akai ciki dashi kafin suka nufi babbans sashen Annen Dake baya kadan daga can gefen sosai danasu Turakin.

Daga Sa'adah data Saba zuwa gidanjen masu 'yan kananun kudi dangin uwarta har Laylah da Bata zuwa koina daga gida sai gida sai kasuwa sai asibiti
Babu Wanda ya rudar da kansa da wani kalle kalle sbd daidai gwargwadon nutsuwarsu,
Dan sani Kam sunsan sunzo wata duniyarce ta daban Amma Kuma Basu rikita kansu da wani kalle kalle a saima kokarin sake nutsuwa dasukeyi Dan kuwa jikinsu duka sanyi yayi Dan Basu dauka Haka duniyar gidan Turakin take da banbanci fiyeda tunani da inda Suka fitoba.

Ita Laylah Bata tunanin komai bayan bin duk dinta Yar uwarta tayi sbd dama tasan dawainiyar Yar uwarta tazo yi duk da taga yanayin gurin Kam ba lallai ta iya wasu ayyukan batareda an koyar da ita saidai Kam har a zuci da sarari tayi anty Sa'adah fatar samun rayuwar farin ciki da kwanciyar hankali tareda mijinta Dan kuwa shima da Anne zasu Shiga adduarta tunda suka aminta da karban riqonta a gidan batareda sunqi amincewaba.

Palon Anne Kam zaunawa sukayi Sa'adah na kallon koina tana yaba tsarki na ubangiji Mai ni'imta bayin dayaso.

Sanin akwai gajiya da buqatar hutawa a tareda dasu tace akaisu dakinta daya dake sama Kai tsaye Dan qasan manyan palone guda biyu da kicin dasu dining room sai dakin baqi guda daya Dana masu aikinta su biyu dasukai shekaru masu tsayi tare.

Ana kaisu dakin da'akace na Sa'adah ne aka fito aka barsu Sa'adah na kallon koina cikin dakin dayaji English royal set na gado Ash Mai haske da curtains milk masu touch na Ash kadan kadan aciki,
Daga gefe ga wasu set na sofa gua uku golden da table a tsakiyarsu.

Ac da aka kunna ne yafara Kama dakin da Sanyi Mai Dadi ga qamshin turaren _Rose night_ dake fita kadan kadan daga Air defyair Yana sakar da wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali a dakin.

Kallon Laylah wadda ke kallonta cikin Dan yanayi na sake shaidar da farin cikin da Antynta take ciki Ahankali tace"
Laylah???

Ahankali ta amsa cikin Taushin lafazinta da cewa"
Na'am.

Jinjina Kai Sa'adah tayi tana sauke numfashi ajere tana cewa"
Zamu iya rayuwa Inshallah anan,
Zamuyi kokarin inganta rayuwarmu sbd tamkar marayu muke yanzu mu dukan,
Ta wani sashen Kuma tamkar nice marainiyar kinfini gata yanzu.

Dan sauke Kai Laylah tayi cikin qaramin sauti Mai sanyi tace"
Anty Sa'adah kece kadai gatana a yanzu da Allah ya bani,
Nagode sosai Allah yasaka Miki da alkhairi Kuma Zan Miki biyayya daganan har qarshen rayuwata Anty Sa'adah,
Anne ma da mutanen gidan Nan Zan musu biyayya kowa bazan Bari kiyi danasanin zuwa daniba har su Abba yadawo Inshallah.

Murmushi Mai sauti Sa'adah tayi tana cewa"
Naji wannan maza muje toilet Naga abinda Zan koya Miki kiyo alwala akwai salloli akanmu.

A toilet kam qarasa saddakar da komai sukayi na gidan da rayuwar gidan Dan kuwa yanzu sukam sai abinda kawai idanuwansu suka ganar musu Amma girman toilet din da tsaruwarsa har kayar da agaban Laylah yayi.

Alwala sukayo bayan sunfito Aka kawo musu kayan ciye ciye dansu suci su huta kafin su sauko cin abinci,
Mai aikin ce ta nuna masu inda zasu kalla suyi sallah kafin ta fice.

Suna idarwa anty Sa'adah ce tafara cin su snacks din da akayi su a tsare sunyi kyau da Dadi Sosai sai fresh milk masu sanyi.

Sai data cewa laylah taci tukuna tasaka hannu a natse tafara dauka tanaci tareda Shan fresh milk din datai sanyi sosai ga wani irin kauri da dadin zallar Madara da nono.

Sosai sukaci suka koshi kafin Sa'adah ta miqe ta Haye gado tareda miqewa sbd gajiyar datake ji.

Laylah kuwa tattare gurin tayi tareda daukan kayan ta fito dasu har qasa
Masu aikin sukai saurin tarbanta cikin tsananin girmamawa suka karba suna cewa ta ringa kiransu a kowane aiki.

Ba musu ta gyada Kai a girmame itama kafin ta juya tana Shirin komawa wani qamshi Mai qarfin sanyin qamshi ya fara gauraye palon batareda ta dakataba ta Dan waiwayo kadan daidai shigowarsa Sanye cikin wani tsaddaden farin yafin filtex daya fitarda haskensa da annurinsa sosai
Take tayi saurin sauke kanta tana sauke idanuwanta daya cika matasu har Saida gabanta ya fadi
Taqarawa kanta sauri zata qarasa wucewa Kamar daga sama muryar Anne ta sauka cikin Kulawa tace"
LAYLAH dawo ki gaidasa.

Cak ta tsaya tareda juyowa ahankali batareda takuma dagowaba muryarta a wani irin Sanyaye ta furta"
Ina wuni?

Gabaki daya Bai lurada kowaba agurin Saida Annen tayi magana Dan Haka Kai tsaye ya amsa gaisuwar da sautinsa Mai kamewa batareda ya kalli gurinba yaqarasa wucewa zuwa palon Anne Dake hade da bedroom dinta.

Kallon Laylah dake sanyeda kayan dasukazo dasu har lokacin ajikinta Riga da skirt na wani babban zallar farin lace Mai adon golden ajiki.

Fuskarta ta kalla tasaki Dan murmushi tana cewa"
Jeki kihuta za'a kawo kayan sawarki zuwa Anjima ko gobe da safe
Karkiyi aikin komai kinji.

Gyada Kai tayi Ahankali tareda furta" Nagode" cikin sauti qarami kafin ta wuce tabar Anne nabin Dan kwankwasonta da kallo duk da akwai mayafi Mai Dan girma ajikinta Amma Kam Laylahn batada kiba ko kadan saidai ahakanma duk da Bata ganta dakyauba ta lurada tanada cikar qirji da qasa saidai Suma Kam duk Basu wani fitoba sbd Ganin take harda yunwa ajikin Laylan.

Juyawa tayi itama tayi hanyar palonta da Turakin ya nufa.
Chapter 18 · 0% Book details