← Book details Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 67

Sashe 12

Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikinsa ta zubawa idanuwanta sbd daukan idanuwanta da farar lafiyayyar fatarsa keyi,
Kan qirjinsa Mai Fadi da gangaro da idanuwanta dake raunana zuwa Kan qaqqarfan qwandar hannuwansa dasuke bayyanarda lafiya da qarfinsu ga lafiyayyar fata,
Ji tayi idanuwanta sun ciko da hawaye kamar ta Dora hannu akai taita rusa ihu tana birgima aqasa akan ya taimaketa ko Wasa yabari ta ringa Yi da jikinsa Dan kuwa duk lokacinda tayi arba dashi Babu Kaya Jin take Kamar ta jawosa Tai Masa fyade Koda kuwa shi baida abinda zai Mata ita tanada abun yimasa Amma koyaushe sai Yana hanata kusantarsa sbd karta sabawa kanta da abunda zai ringa hanata sukuni takasa riqe buqatarta,
Gashi ita tayiwa kanta ta hanyar cewa zata zauna dashi ahakan har tsawon rayuwarsu bayan yayi yayi ta tafiyarta tayi aure inda za'a Bata haqqinta na aure Amma taqi,
Har sakinta yayi so biyu akan tatafi Amma ta boye sakin tace Masa bazata taba tafiyaba itama batada lafiyar zata zauna dashi ahaka bayan tasan kwadayinta akansa kullum qaruwa yakeyi duk tana ganinsa
Shiyasa yake nesanta kansa da ita kada yaringa shiga haqqinta da yawa tunda Yana iya ganin tsananin sha'awarsa a tareda ita,
Gashi shi tunda yasan baida abinda zai iyayiwa mace yasa Koda Wasa ko kiss baitaba kwatanta yiwa kowace mace ba bare harya wuce Nan duk da likitansa Yana basa tabbacin sauki zaizo Masa Amma saiyana kiyayewa Dan saukin zai iya zuwar Masa da zazzafar sha'awa Mai qarfi da hadarinda idan ya fara sex da mace zaiyi wuyar iya barinta Dan Haka yake Kan magani da tsari sbd gujewa hakan idanma lafiyar zatazo tazo Masa alokaci na iya controlling kansa.

Sakin kofar dakin tayi tareda juyawa ta koma Palo bayan taja Masa kofar tunda ba'a tsaya Masa idan Yana shiri.

Baro saman tayi ta nufi bedroom dinta Kai tsaye da sauri ta lalubo wayarta ta kunna videos din data Saba kalla Dan ragewa kanta shaawa.

Gidan tsit yake sbd sanin Maigida na gari Dan Haka kowa ya kammala aikinsa ba matsala ya Adana kansa,
Bayan sallar magrib ya sauko palon sanye cikin wata lallausan milk jallabiya daketa kyalli
Qafafunsa sanye da slippers na D&g hannunsa ko agogo Babu sai qamshinsa dake mamaye palon cikin sanyi.

Sanin lokacin saukowarsa yasa Mss Na'ima fitowa cikin wani irin ado na wata purple Embellished Emboidery super datai Mata kyau sosai sai wani qamshi Mai qarfin gaske na turarukan daban daban take bugawa ga fuskarta Tasha simple kwalliya ta nufi dining room datasan can ya nufa
Kusan atare Suka zauna Kan dining din M Sarat ta matso tafara serving nasu abincin cikin girmamawa sbd itace Mai aikinsa ta tsawon shekaru tun Bai manyantaba take Masa aiki to yanzu yazama Bata aikinma saidai bada umarni wa masu aikin saidai hidimarsa Kam har gobe itace Mai Masa.

Shiru ya ratsa gurin sunacin abinci cikin nutsuwa da kamewa yake komai nasa shiyasa komai yayi abun burgewa da koyi ne wainda suke taredashi.

Bayan Gama cin abincinsu palo yadawo ya zauna Dan bawa Mss Na'imah lokacinsa itama.

Kusa dashi sosai tazo ta zauna tareda Kai hannayenta ta Dora akan nasa Dake Kan jikinsa ta zuba Masa fararen idanuwanta tana sakin murmushin Jan ra'ayi a yangance da son Jan hankalinsa tace"
Amma dai zamu kwana biyu anan kafin ka wuce Abuja?

Dan waiwayowa yayi ya kalleta batareda ya motsaba yayi Mata kallon minti biyu kafin ya maida kallonsa kan tv cikin kamewarsa da Dan sakewar fuska tunda ita din iyalinsace a gajarce yace"
Gobe Zan wuce Abuja da yamma.

Marairaice fuska tayi tana sake shigewa jikinsa tace"
Please Turaki ka qara ko kwana biyu ne kafin zuwa abujan,
Idan muka koma gobe kana zuwa can bazakai lokacin hutawarmu ba.

Ki zauna anan idan nagamo daga Can kafin nakoma zanyi kwana biyu anan bayan tafiyata din saiki koma Abujan.

Ba Dan tasoba tace"
Ok Amma dai zanbika Abujan Kuma idan zaka dawo nasake biyoka.

Kallonta ya Dan Kuma waiwayowa yayi sbd yasan tsoronta akan zuwansa bada itaba baifi akan maganar qarin aure da Anne keson yayiba ko zai samu haihuwa.

Juyar da idanuwa tayi tana kokarin boye yanayin data shiga din Dan kuwa har cikin ranta Bata qaunar kebewar Anne da Turaki tunda tasan zancen dai daya ne na qarin auren.

Wani irin lafiyayyan murmushi ne dayafi komai kasheta yasaki Yana dauke kansa daga kallonta yabarta tana qarasa zubewa ajikinsa Dan kuwa murmushin abune dabai cikayiba Amma yanayi din sosai.

Har qarfe goman dare Yana tareda Ita yabata lokacinsa sosai kafin buqatunta suka biyo baya inda ta wawashi kudi masu matuqar yawa agurinsa Wanda dama ita sune suka riqeta a auren.

Sai daya rabu da Mss Na'ima kafin ya nufi office room dinsa na cikin gidan inda A Abdoul ke jiransa da tarin bayanansa
Yana shigowa kuwa A Abdoul din ya miqe Yana Masa barka da fitowa kafin ya zauna Kan kujerar 1 seater dake facing din A Abdoul ya miqa hannu ya karba iPad din Dake hannun Abdoul din Yana duba bayanan.

Sai dare sosai ya fito ya ta kofar Dake palon qasan ya nufi sama ya Haye
Kai tsaye ya nufi bedroom dinsa.

Washe gari qarfe Tara an kammala komai na breakfast din gidan an jere sai qarfe goma yasauko sanye cikin Ash Kaftan na babban yadin Ambassador sai hular qube
Hannunsa sanye da agogon _Chanel_
Take qamshinsa ya gauraya palon kallo daya A Abdoul da M Sarat sukai Masa Suka sauke Kai ganin Mrs dinsa a gefensa sai wani Jan girma takeyi cikin nata adon.

Breakfast yayi tareda Ms Na'imah da A Abdoul kafin ya fito zuwa Inda zai gana da baqinsa.

Qarfe biyu yagama da baqinsa yadawo gida yayi lunch tareda Ms Na'imah kafin ya haye Bai fitoba sai qarfe hudu da rabi Ya sauko Kai tsaye suka shige mota zuwa airport dukkaninsu.

A jirgi ma hankalin Na'imah gabaki daya yakasa kwanciya Dan ita harga Allah ma rashin zuwan Turakin yafi Mata kwanciyar hankali akan zuwansa
Dan zuwansa kullum cikin sakata fargaba yake,
Kishinsa take sosai sbd bazaso akaro wadda zata tayata cin wannan dukiyarba.
#MAMUH#
Kuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete
Mamuhgee @Arewabooks
*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_
*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_
*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_
*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_
*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya
*_09032345899_*
*KATIN MTN*
09166221261
*_Mamuhgee 11_*
Umma Jamila kasa nutsuwa tayi ta ringa addabar Haj Karima Saida suka sako Kawu saidu da Kira Kan Kira ya shiryo ya taho sbd matuqar ba yana garinba Turaki yazo yatafi to fa Babu wata maganar aure bayan sukam tuni suka hau Shirin aure gadan gadan batareda lissafin komaiba ko tunani irin na masu shekaru,
Koda Kawu saidun ya iso daga nijar ya sauka a dakin Abba sosai yashiga mamaki da takaicin ganin halinda Laylah ke ciki sbd shikam kallo daya yayi Mata bayan Sa'adah takawota sun gashesa ya fahimci batada isashiyar lafiya Dan kuwa ko dagowa ta kallesa bataiba kanta a qasa ta gaidasa.

Abinci kawai yaci yayi salloli ya wuce asibiti gurin Dan uwansa yabar gidan
Yana fita kuwa saiga Alhaji Atiku da Umma Jamila sunzo gurinsa Basu tarar dashiba Dole suka koma da niyar dawowa gobe Dan subarsa yau din ya huta.

A asibiti kuwa tunda yayi ido biyu da Dan uwansa take jikinsa yayi Sanyi Dan baiyi zaton Jikin yayi Munin hakanba take qwallar tausayi Dan uwa taciko idanuwansa ya hadiye Yana jinjina Kai Yana sauraron bayanin yanda Abban yaketa fama da jikin duk tsawon lokacin Nan daga Abdullahi...

Shiru Abdullahin yayi yanason sanarda kawun wasiyar Abban na bawa AB TURAKI auren Laylah ko bayan ransa Yana shakkar Shiga zancen sbd sanin maganace Mai girman gaske tunda aure ake magana
Auren Kuma da mutum kamar Turaki,
Shi daza'a basa auren Laylah dinma da wlh Yanaso ya karba.

A asibiti Kawu ya tarewarsa Bai sake komawa gidanba ya zauna jinyar Abban Abdullahi yasamu hutu duk da kullum da daddare saiya leqo asibitin kawowa Kawun abinci duk da Babu wata wata daga gidan umma Jamila ake kawo Masa abincin safe Rana dare Kuma abincin Alfarma lafiyayye Wanda tun Kawun Bai kawo tunanin komai aransaba yafara tunanin akwai dalilin hakan Dan Haka ya zuba musu ido yaringa cin abinda Dan yasan Umma Jamila batada Tausayin bawa Dan uwan Mahmoud ko abunda bataso matuqar ba babban daliline garesuba Mai matuqar mahimmanci.

Ganin dai Kawun baida niyar dawowa gida bare suzo ayi magana dashi yasa Suka yanke shawaran haduwa dashi a asibiti Dan Haka yau da daddare Yana zaune bayan yadawo daga masallacin asibitin sallar ishai yaci tuwon semo da miyar kubewa da gandar da aka kawo Masa tareda fruits
Gamawarsa kenan Yana kokarin amsa Kiran Mai dakinsa daya shigo wayarsa saiga Alhaji Qarami tareda Alhaji Atiku da umma Jamila sai Haj Karima data iso a jiya sunshigo sanye cikin shigar Alfarma,
Miqewa yayi cikin sakewar fuska Yana cewa"
Marabanku da zuwa,
Alhaji Qarami bismillah ku qaraso daga ciki,
Alhaji Atiku barka da zuwa
Sannunku sannunku
Yanzu da Daren Nan kuke shigowa.

Haj barkanku da zuwa Bismillah ku shigo,
Hannu ya miqa musu sukai msabaha Yana sake gaidasu cikin mutuntawa duk dai ya girmesu saidai kasancewarsu manyan mutane yasa shine yafara gaidasu din Suma cikin mutuntawa fuska asake suke gaidasa tareda maida kallonsu Kan Abba cikin alhini suke tambayar jikinsa,..

Allah yakawo sauki da afuwa yasa kaffarane.

Amin Amin ya Allah,
Alhaji Atiku Naga hidima anatayi damu
Allah ya Sanya alkhairi yabada Lada
Ana kokari sosai wlh
Ngd Sosai Haj Jamila.

Bakomai Kawu saidu ai duk yiwa Kaine musamman kaida kabaro iyali kazo nesa gashima bamu samu lokaci anyi maganar datai dalilin zuwan naka.

Gyara Basu gurin zama Kawun yayi Yana zama shima kafin ya nutsu Yana kallon Alhaji Atikun yace"
Eh wlh to nazo na tararda jikin na Mahmoud ba sauki ba sauyi shine hankalina duk ya koma kansa Amma ai tunda maganar aurece ba wata damuwa duk lokacinda magabatan yaron suka tsaida ranar zuwa sai a sanar Dani naje saimu taru a tattauna din....
Chapter 12 · 0% Book details