← Book details Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 67

Sashe 54

Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Halima ce data fito kitchen tagansu
Aikuwa bakinta yakasa rufuwa da sauri ta ja kayan tana cewa Ruky ta biyota da sauran kayan
Suka nufi dakin Laylan tun na farko dake guri daya Dana Sa'adah
take halima tasa Ruky din ta Kama aiki suka hau gyaran dakin dukda yananan da komai na tsari da buqata acikinsa.

Sir Turakin kuwa qarasowa yayi zai gaida Annen ya wuce nasa bangaren,
Ita Kuma a silale ta nufa inda Annen take zaune tana kokarin Nemo muryarta data maqale a maqoshinta zata gaidata Ms Na'ima ta shigo palon Kai tsaye ta sallamar da kwata kwata batamasan Yaya ta fito abakintaba..

Yana ganin Na'ima ya dakata daga inda yake tsaye Bai qarasa gurin Annenba ya tsaya kallonta fuska a kame hankalinsa kwance.

Anne kuwa tashi daga zaunen datake tayi Tana qarasawa gaban Laylan Kai tsaye tace"
Wuce ciki kifara hutawa tukuna.

Duk yanda take tunanin tashin hankalin fuskantar mum dinta abin ya wuce hakan a zuciyarta sbd daukewa numfashinta yayi Jin muryar mum din daga bayanta,
Yanda zuciyarta ke harbawane yasa takasa juyowa ta tsaya cak a inda take tareda rufe idanuwanta hawayen dasuke ciki suka gangaro har sai dataji saukan muryan Anne datace ta wuce ciki.

Daga kafa tayi zata wuce batareda ta juyoba har lokacin,
Cikin tsananin bacin Rai Mai girma daya sake rufe Ran Ms Na'ima tace"
Laylah?

Tsaya agurin,
Yaushe Kika dawo?

Meyasa Baki fadamun ba?

Wacece kuka dawo da ita tareda Turaki??

Cak Laylan ta tsaya agurin cikeda mamaki da fargaban yanda mum din tagane itace zuciyarta na karyewa da abubuwa da dama,
Har cikin ranta tasan Bata kyautawa riqon da Mum tayi Mataba,
Ta wani bangaren ta yarda da tabbas taci Amanar mum sbd koma yayane tayi Mata riqon 'ya ba irin Wanda ta taso acikinsaba Amma ace itace take dauke da cikin mijin Mum.,
Da wane idon zata kallo mum data kamu da tsananin son Turakinta Mai tsananin datake Jin rabata dashi shine mafi Munin illar da zaaiwa rayuwarta....

Cikin fushi Ms Na'ima ta tinkari Laylan idonta rufe da bacin ran wadda suke boyewa da Turaki yazo da ita tana cewa"
Magana nake Miki amsa Zaki juyo kibani Raina abace yake
karki dora wani laifi akan wannan na zuwan da kikai batareda kin sanar dani b......

Hannunta Turaki ya riqo akaro na farko tun shigowarsu gidan daya bude Baki Yana kallon cikin idonta Kai tsaye murya a kame yace"
Ki nutsu banason hayaniya Anan,
Wuce,koma kije bangarenki....

Qwace hannunta tayi da qarfi tana kallon Anne idonta jajir tace"
Anne gwara ayi komai a gabanki tunda da alama kinsan komai,
Turaki Wlh nasan yanada wata macen daban bayan Ni da waccar dayar,
Najima da Dani Dan Haka gwara a fadamun meyasa za'a rufeni akan wani auren daya Kuma.....

Just shut up Na'ima,
Ki fita kibar Nan nace...

Gurin Laylah takuma nufa gadan gadan tana cewa"
Wallahi bazan fita ba sai nayi magana da Laylah kokuma tabiyoni muje ai dama nice mum dinta,
Nice nake riqonta,
Ta wuce muje da kaina zanyi magana da ita.

Kallonta Anne tayi cikin kulawa kafin tayi mgn
Baice komaiba ya Kama hannun Na'iman ya juya da ita
yana ganin Haj Zinat bayansu ya sakar Mata ita Kai tsaye yace"
Jata ku tafi.

Kama hannun Na'ima Zinat tayi dukkanin wutarta na daukewa da zallan mamaki da firgici harma da tashin hankali dan kuwa kallon tsaf dataiwa Laylah daga bayanta sbd a hangi ciki a jikinta wallahi.....

Kokarin Jan Na'ima takeyi Amma ta fizge da qarfi kafin kowa ya Ankara ta Isa gurin Laylah Dake tafiya zuwa daki Tasha gabanta....
##MAMUH#
Cak ta tsaya gaban Laylah tareda mutuwar tsaye tana fiddo dukkanin girman idanuwanta afili tana kallon ciki dayake gaban Laylan
Kallonta ta maida Kan Turaki da sauri Dan batada lokacin Anne ita ba yanzu ba
Ganin yanda fuskarsa take a hade tsaf yasata maida kallonta Kan Laylah cikin wata muryar tashin hankali tace
Laylah,ciki kikayi?

A Ina
Waye yayi Miki?

Shiyasa ake mun boyo?Kokuwa kinada wata uwar data fini da baza'a sakani cikin masana ba
Hawaye Laylah takeyi sosai takasa ko kwakwaran motsi sbd gabaki daya neman fita take hayyacinta sbd firgicen datake
Hannu Ms Na'ima takai ta damqo hannunta tana cewa
Muje can bangaren zamuyi magana a tsanake Dan kinada laifi Mai girma agurina,
Gabaki daya an sauyamin ke
Komaima Dake ake boyemin
Bangare hannunta daga na Layla yayi zuwa Lokacin fuskarsa na bayyanarda bacin ransa sosai ya jata tana kokarin qwacewa bataji Bata gani idan ba Laylah aka Bata ba ta zaunar da ita sukai budaddiyar wasika Dan koma menene Laylah tasan komai
Ita ba cikin jikin Laylah ya dameta ba Maganar wacece a rayuwar Turaki takeson ji
Dan akan hakan yau tafison ta cinnawa gidan wuta Har Turakin da ita su mutu hankalinta ya kwanta
Haj Zinat ta fita tana waiwayen Laylah hankalinta tashe saidai itama takasa yadda da tunanin abinda suke gani da Wanda suke Shirin ji ma
Bin bayansu Na'ima da Turakin tay
i Bata daina waiwayeba har tana kifewa da sauri ta tashi tabi bayansu qafafunta na rawa
Bakin Kofar bangaren Na'iman ya dakata tareda sake hannunta
fuska daure ya kalli gefenda Haj Zinat ta iso da sauri ta riqe Na'iman Kai Tsaye yace
Ta zauna aciki idan ta fito ta tafi gurinta Zan dauka matakin hakan,
Ta dawo hankalinta wannan zallan rashin Kama Kaine ga masu aiki suna kallonta,
Ki nutsar da ita zaifi Mata mutunci
Juyawa yayi yabar gurin sbd yasan duk hakurinsa da kamewarsa bazai iya tankwafar da Na'iman ba,
Sbd Bata ganin kowa idan tana rashin Jin ta
zubar Masa ma da mutunci zatai a gaban securities da masu aikin gidansa idan ya biyewa tankwafar da ita din
Yana barin gurin bangarensa ya nufa ya shige batareda ko waiwayensu yayi ba saidai yasan duk fashinsa da fadansa bazai Hana Na'ima tashin hankali ba idan tagama sanin ZAINAB da cikinta duka nasa ne Dan Haka Dole zai rabasu
Bazasu zaunu guri dayaba
Laylah tunda tazo bazata komaba saita haihu Dan Haka Na'iman zai tura Takoma Lagos kokuma US
Da karfi fa yaji a haukace Haj Zinat ke janta tana kokarin qwacewa
Tayi ciki da ita suna Shiga babban palonta ta qwalawa siddika Kira da qarfi tana cewa
Yi sauri saka key ki rufemin kofar ki zare keys din
A rude da mamaki siddika ta qaraso ta dannawa kofar key tareda zaresu tayi saurin miqawa Haj Zinat din kafin Ms Na'iman tayo kanta
Damqe keys din Haj Zinat tayi kafin ta saki Ms Na'iman cikin tashin hankali Mai girma da itama yau haukar takusa kamata ta nufi kujera ta zauna tana zare mayafinta tayi wurgi dashi
Danwkalinta takuma zarewa ta jefar Kan kujera tana kallon siddika cikin tsawa tace
Kawo Mana ruwa ko zuciyata zata dawo Kan aiki
Kallon Na'ima Dake safa da marwa cikin masifar Dake cin koina jikinta tace
Ki zauna wlh akawi babbar matsala Mai girma.

Ke bama matsala bace wannan akwai masifa da bala'i masu girma a cikin wannan zancen
Kasa zama Ms Na'ima tayi taci gaba da safa da marwa cikin masifa da takaicin Mai tsananin gaske tace
Sai naci uwar Laylah
Zan koya Mata darasi Mai girman gaske idan munkoma ta yanda bazata Kuma ya yarda a munafurceni da ita ba
Banyimata riqon dazaisa taji Ina cutartaba Dan me zatamun mufurci,
Yanzu gashi Nan duk yanda nake kaffa kaffa Kar tayi saurayi Ashe ciki tayo ta rufeni baibai
Har Anne da Turakin sun sani tunda sune jininta gashinan an daukota da saidai naga 'dan shege a gidana
Ni tsabar masifa da bala'i Banda Allah yayita asararrar duniya wlh data Bari nasan da cikin bazan Bari Turaki da Anne su saniba haifemun shi zatai taban nasamu magaji gurin Turakin tunda yanzu yasamu lafiya hakurinsa na haihuwa ya gaza Sai bin Mata yake.

Wallahi Laylah taci Amanata Kuma wlh zatasan bacin Raina baida kyau ko gaba ance tasake min irin Haka bazata kumaba
Ruwan da siddika takawo masu Dan sanyi Haj Zinat tagama shansu tayi wurgi da robar ruwan da sauran Dake ciki
Siddika tabi robar ta dauke tareda zuwa ta dauko abun gogewa
Na'ima ki dawo hankalinki ki fuskanci gaskiyar da idonmu ya ganar Mana,
Idan Baki dawo hayyacinki Kika kalli komai a bude ba za'a cigaba da rufemu ne Muna bulayi cikin hauka.

Cikin jikin Laylah na waye
Sbd kariyar danaga Turaki da Anne sun bayyanarda Shirin Bata ta gaske ce bana tunanin 'ya zatai cikin shege ayi Shirin Bata wannan kariyar.A
Zima Ms Na'ima tayi a kujera tana yiwa Haj Zinat din wani kallo tace
Bangane wannan bayanin ba
Na'ima wlh nafara tunanin Mai cikin da muke nema Laylah ce
Ranarda yace Miki karki kuskura ki Isa gidansa idan kin koma US
Maganarsa ta tabbatarda abinda yake son hanaki Isa garesa Yana cikin gidansa kenan sbd tun aurenki dashi Bai taba hanaki tafiyaba ko wace irice sai lokacin
Kuma muka kira Laylah Dan neman sanin abin dayake faruwa cikin gidan tabamu tabbacin Babu kowa a gidan bayan ita da Cindy
Yanzu Kuma ga ciki a gaban idonmu mungani
Gata Babu sanarwa yaje ya daukota mungani
Gashi suna kokarin Bata kariya daga gareki
Idan har tayi cikin shege da Bai shafeki ba meyesa za'a Bata kariya daga gareki bayan kece yakamata ki Bata kariya daga garesu sbd fusatar da zasuyi idan tayi cikin shege
Zuru Ms Na'ima tayiwa Zinat da Ido tana kallonta tamkar wuwuya
Kiran sunanta Zinat tayi tana girgizata tace Kinaji kuwa
Girgiza Kai Ms Na'ima tayi tana cire hannun Zinat din daga jikinta tana cewa
So kike kicemun cikin Turaki ne a jikinta
Da mamakin tambayar Zinat ke kallon Na'iman tace
Bazaki bud qwaqwalwanki ki fahimta ba kenan
Sake girgiza Kai tayi tana dauke kallonta daga Zinat din tace
Zancen ne bamai taba yiyuwaba,
TURAKI fa kikace da cikin jikinta?

Kinsan me kike fada kuwa
Abbantane fa
Aminin Mahaifinta daya hada auren uwarta da ubanta
Tayaya kike kawo wannan rikitaccen bayanin
'yar uwarta dasuke uba 'daya yake Aure shi Turakin idan kin manta,
Hakama tamkar yar cikinmu muke riqonta
Wannan tunanin babusa a cikin duniyar mutane..wallahi bazai yiyuba
A rikice Zinat ke kallonta tace
Abokin uba nawane yayi lalata da Yar abokinsa?
Chapter 54 · 0% Book details