← Book details Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 67

Sashe 60

Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itadai gaskia bazata yarda tayi biyu babuba wlh ta koma rayuwar wahalar data fito,
Dan gwara Mata wulaqanci da masifa harma da bala'in Ms Na'ima akan barin gidan AB TURAKI Dan Haka Dole zatasan yanda zatai bada saninsuba ta bayyanarwa da Anne ko Turakin lalurar da Ms Na'ima take dauke da ita ko za'a rabata da Zinat a cetota tasamu taci gaba da cin arzikinta lfy kafin Zinat din ta wargaza musu Suma komai.

Ba yanda ta iya da daddare Haka ta cinnawa dakin wuta
Aikuwa wuta Mai qarfi ta tashi wadda batama tsammata ba
Tsoro ya kamata ta fito da gudu tunda wuri ta nema jama'a sbd wutar kamar jiratake a kunna koina yafara dauka.

Hankali tashe securities da kowa gidan ya fito,
Anne na dakin Laylah a Daren sbd wani zazzabin datake fama dashi na damuwar Dole data sakawa kanta,
Gashi taqi yadda ko ganin juna suyi da Abban nata sai zaman boyo take a daki duk ta Hana kanta sukunin zuciya shima ta hanasa sbd rashin ganinta yafi komai daga hankalinsa ita kanta rashin ganin nasa ne yaketa nukurkusanta.

Jin hayaniya na tashi a gidan yasa Anne miqewa daga zaunen datake tana bawa Laylah tea abaki tana Sha jiki amace.

Fitowa Palo Anne tayi tana cewa"
Halima lafiya gidan Nan kuwa nakejin hayaniya?

Wutace ta tashi Anne a bangaren Ms Na'ima sosai Kuma wlh..

Subhanallh innalillahi, yanzu?

Ina Na'iman?

Bata ciki dai ko???

Fita tayi da sauri tana faman nanata tambayar Allah yasa Na'iman Bata ciki.

Siddika ce kawai a waje takasa komawa jiki jikinta sai rawa yake hankalinta ya tashi Bata dauka wutar zata juye ta zama hakanba..

Koda Turaki ya fito gurin cikin sauri ya qaraso Yana tambayar Ina Na'ima?

Cikin tsananin kuka da firgici siddika tace tana ciki...

Aikuwa Bai tsaya Gama ji ba ya nufa kofar ya shige...

Anne da sauran maaikatan gidan da securities suka fara ihun Kiran sunansa....

Anne da sauri ta bisa zata kamo halima ta riqeta ta hanata shiga....

Ihun Kiran sunan Turakin da ake yasa Laylah fitowa Bata ko ganin gabanta sosai jikinta har rawa yake ta kallesu cikin yanayinda muryarta Bata ko fita sosai ta bude Baki zatai magana sai gashi yafito daukeda Na'iman data Gama shaqar hayaqin harta fita hayyacinta da sauri ya nufa mota da ita Yana cewa A Abdoul daya iso ya bude mota da Sauri.

Shigewa motar yayi Suka nufa asibiti
Suna fita motar kashe wuta na isowa aka fara kashe wutar.

Anne jininta ya Riga ya hau Dan Haka Dole Saida aka kamata aka maidata ciki
Laylah ma daqyar ta maida kanta ciki suka kwantar da Anne bayan anbata maganin Hawan jininta ta kwanta itama ta nufi daki ta zauna sbd bacci kam ya Riga ya qauracewa idanuwanta,
Zazzabin datake ji ma take taji yasake,
Gabaki daya hankalinta ya tashi Kuma sbd koma menene tasan wanna wutar tanada alaqa da abinda yake faruwa..

Gida takeson zuwa kowa yasamu damar samun nutsuwa.
##MAMUH#
*_Mamuhgee 53_*
Suna Isa asibiti aka karbi Ms Na'ima aka karbeta tareda shigewa emergency da ita sbd ta shaqa hayaqin sosai gashi har lokacin Allurar da akai Mata Bai saketaba jikinta a mace yake Sosai fuskarta da jikinta sunyi duhun hayaqi daya Bata jikinta.,
Zama Turakin yayi a office din Dr faruk daya bude Masa Dan ya zauna anan,
Sai alokacin ya sauke numfashi tareda kallon A Abdoul daya shigo office din da wayarsa a hannu sbd shi yabaro tasa wayar.

Kai tsaye A Abdoul wayar Anne yafara Kira dan sanar dasu Inshallah komai yafara daidaita tunda anshiga da Na'iman gashi dama ba konewa tayiba kawai dai hayaqin ne yashiga cikinta.

Wayar Annen Bata shiga Dan Haka saiya kalla Turakin a hankali ya sanar Masa.

Gyada Kai kawai yayi hankalinsa na rabuwa biyu kowanne da damuwa,
Laylah yakeji wadda ya tabbatarda hankalinta ya tashi Sosai ga yanayinta
Sam baya son abinda yake daga hankalinta gashi ba waya bare ya kirata,
Wayar A Abdoul bazataiji wani dadin wayar da itaba Dan Haka zai hakura harya koma gidan...

Bangare daya Kuma Na'iman ce da matsalolinta,
Tashin hankalin kishinta yayi yawa,
Sam takasa saduda akan lamarin gashi tana neman halaka kanta sbd tunanin banza,
Sam yakasa gane ace Mai cikakken hankali ne zai cinnawa kansa wuta sbd kishi,
To idan ta mutu ai tayi abanza kenan tunda Wanda take kishin tabarsa da wadda take kishin itama,Dan Haka gskia lamarin nata yayi Muni..

Tana warkewa zai maidata Lagos idan Kuma Nan takeso LAYLAH na haihuwa zata koma US ita tabar Mata Nan.

Sai Asuba Ms Na'iman ta dawo daidai bacci Mai nauyin gaske ya dauketa
Suna kokarin baro asibitin Haj Zinat ta iso cikin tsananin firgici da tashin hankali tana ganin Na'iman tafara kuka tana riqe hannunta.

Ganin zuwanta yasa Turakin samun saukin barin Na'iman tareda siddika Dan Haka ya wuce yabarsu agurinta.

Yana tafiya Haj Zinat kallo daya kawai tayiwa siddika datake firgice har lokacin ta Dan jinjina Mata Kai.

Siddika dai Bata samu damar cewa komaiba sbd hankalinta bai gama dawowa jikintaba,
Saura kadan yau tayi kisan Rai takeji,
Meya kaita wannan aikin rashin Imanin akan kwadayi?

Yanzu da Ms Na'ima ta mutu koda ba'a ganesu ba tasan wlh shikenan haukacewa zatai nauyin Rai data kashe bazai bar qwaqwalwartaba.

Hawaye ne Suka ciko idanuwanta jikinta na sake daukan rawa Amma Ta hadiyesu sbd Kar Haj Zinat tagani tasan zuciyarta ta raunana ta illatata gudun kawo Mata matsala,Dan hak ta hadiyesu tareda maidasu suka koma tana kokarin nutsar da kanta.
****Washe gari tunda safe Anne da kanta ta shirya gurin tafiyarwa dasu Na'iman breakfast Wanda su halima suka hada tunda safiyar Dan akai asibitin.,
Sai data duba Laylah Dake kwance tana bacci ta shafa kanta ahankali cikin kulawa da kauna sbd tasan Laylan Bata cikin kwanciyar hankali na wannan abun daya faru kafin ta juya ta fice Suka wuce asibitin itada halima aka bar Ruky sbd Laylah.

Cikin bacci taji qamshinsa na shigar Mata hanci
Ta dan motsa Ahankali tareda Jan numfashin kadan hancinta yasake shaqar numfashin ta bude idanuwanta ahankali tareda saukewa akan fuskarsa..

Zaunen yake bakin gadon Yana kallonta cikin nutsuwa da tsananin sonta dayake bayyane akan fuskarsa da yanayin kallon dayake Mata.

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tareda lumshe ido ta bude ta kallesa hawaye na ciko idanuwanta na kewansa dama kewan kwanciyan hankalinsu ta bude Baki muryarta na rawar son yin kuka tace"
Abbah.

Lumshe fararen nasa idon yayi shima sbd yayi kewan Jin sunan abakinta Dan Haka yakai hannu ahankali ya Kama hannunta ya tayar da ita zaune ajikinsa hannuwansu sarke da juna.

Kallonta yayi cikin kulawa da azabtar da zuciyarsa keyi akan rashin ganinta da jinta ya shafa fuskarta tareda taba cikinta dage gabansa cikin muryarsa data kashe jikinta da sonsa yace"
Lafiyanki kalau kuwa??

Gyada Kai tayi tana kwantar da kanta jikinta ta zura hannuwanta ta rumgumesa tana rufe Ido.

Babyn fa?

Ba damuwan komai right?

Sake gyada Kai tayi Ahankali kafin bude Baki cikin sautin kulawa tace"
We miss you Abbahh.

Hannunta yakai bakinsa yayi kissing ahankali kafin ya shafa fuskarta ahankali Yana cewa"
I love you.

Ajiyar zuciya ta sake ahankali tareda sake lafewa jikinsa,
Sun Jima a hakan Saida kowannensu yasamu nutsuwar zuciya data ruhi kafin ta dago da idonta ta kallesa A natse tace"
Yaya jikin Mum?

Hope bata samu rauni ko matsalaba a koina?

Jinjina Mata Kai kawai yayi Ahankali Yana cewa"
Ba matsalar komai bane hayaqin ne yaso yayi Mata illa Amma tana lafiya.

Ajiyar zuciya ta sauke tareda tasowa daga jikinsa ta zauna daidai ta sauke Kai ahankali tareda sake riqe hannunsa Dake cikin nata murya a Sanyaye tace"
Abbah please kabarni naje gida.

Mum na buqatan abata space tayi digesting wannan abun,
Ranta ya baci Sosai sbd yanda abun yazo Mata nakuma fahimci Jin zafinta sbd yanda nakejin zafin kishinka na tabbatarda idan nice mutuwa zanyi Abbah idan ka tafi gurin wata,
Dan Haka mum na buqatan abarta abata guri da lokaci ta Gama daukan dumin abin kafin ta sauko...

Dan Allah kabarni naje gida Nima zanfi samun nutsuwa kwana biyu..

Please Abbah.

Girgiza Mata Kai yayi Kai tsaye tareda cewa"
Bazaki ko'inaba kina hankalina zai rabu biyu.

Ki jira idan kin haihu zakije gidan kafin ki koma US.

Riqe hannunsa tayi hawaye na ballewa daga idanuwanta tana kokarin tausar zuciyarta Amma takasa sai kawai kuka Mai qaramin sauti ya balle Mata.

Abbah bazai gane halinda zuciyarta take cikiba,
Tana tsananin sonsa Amma take nesanta kanta dashi sbd tashin hankalin da ake ciki,
Idan tana gidan bazasu taba samun damar magance komaiba har a zauna lafiya,
Gashi saidai taji qamshinsa kawai idan yashigo gurin Anne
zuciyarta na galabaituwa da hakan Wanda shima tasan Yana damuwa da hakan shiyasa bama zai iya tsayawa ayi gyaran ba,
Ita kanta kullum da kwanan tunanin Yana tareda mum Na'ima take
Shedan ya Hana zuciyarta sakat Dan Haka takeson tafiya gidan.

Kukanta yasashi zuba Mata ido Yana kallonta cikin qunci da damuwar ganinta ahalin ya janyota jikinsa ahankali ya rungume sbd baisan Me zai fada mataba,
Hankalinsa bazai taba kwanciya ba idan Bata kusa dashi ko Dan sbd irin wannan fitintinun na Na'ima..

Ahankali ya dagota daga jikinsa tareda Kai bakinsa yayi kissing idonta Dake tsiyayar hawaye ya kalleta ya bude Baki cikin Taushin murya yace"
Ya isa hawayen,
Zakije gida Amma Na'ima na Jin sauki aka dawo da ita gida Zaki dawo kin yarda?

Gyada Kai tayi tana tsayar da hawayenta cikin sanyin jikin kewarsa da zatai.

Kallon kyakkyawar fuskarsa tayi tana Jin dumin hannunsa daya sauka cikin rigarta ya Dora Kan cikinta..

Lumshe ido tayi Ahankali tareda Kai hannuwanta biyu ta kamo fuskarsa takai bakinta Kan NASA ta Dora tareda Kama lips dinta ta tsotsa kafin ta zira harshenta cikin bakin ta kamo harshensa shima ta fara tsotsa.

Lumshe ido yayi tareda matso da ita jikinsa sosai ya karbe kissing din yanayi.

Sosai sukai kissing juna kafin ya saketa Suka ya miqe tsaye tareda daukanta yakaita toilet.

Da kansa ya tayata brush tayi tagama tayo wanka ya tayata shiryawa cikin doguwar riga purple Mai haske suka fito shirye tsaf suka nufa dining.
Chapter 60 · 0% Book details