← Book details Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 67

Sashe 11

Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Momy dake zaune palon tana amsa wayar Kawu saidu Dan uwan Abban daya daya rage Masa Yana can nijar daga nema yayi zamansa can ya Gina nasa iyalin Yama zama Dan can din
Yakirata ne akan Kiran da akai Masa na maganar neman auren Sa'adah wadda yake Bata hakuri akan bazai samu damar zuwaba saidai lokacin auren zaiyi kokari yazo ta amsa Masa da to kawai sbd zumuncin dama yanzu sai ahankali kowa nasa yasani shiyasa jikinta yaqara sanyi sbd ganin dai su Sa'adah din gwarama ace basuda dangin uba tunda shikansa uban gashinan Babu Wanda yanuna damuwa akansa bare Azo garesa baresu yayansa,
Itama nata 'yan uwan matuqar Sa'adah ba auren Mai arziki tayiba duk kaunar dasuke Mata zasu iya juya Mata baya itama.

Numfashi ta sauke tana kallon yanda Sa'adah din ke yiwa Laylah Dake kwance lamo a gefenta firfita tana duba saqon daya shigo wayarta.

Dauke kanta tayi daga kansu tana tasowa ta dawo gefen Sa'adah din wadda itama tayi zufan tadauka wani maficin tafara yimata firfitan ahankali itama.

Juyowa Sa'adah tayi ta kalla momyn da fuskar sanyin jiki ta bude Baki ahankali tace"
Momy meyasa bazaki sawwaqawa kankiba kibari natafi da Laylah sbd kema barinta gurinki damuwace agareki,
Umma Jamila nason daukan Laylah ne taje da ita gidanta
Tayaya Laylah zata iya wani aikin bauta a wannan yanayin matuqar baso ake ta qarasa juyeba,
Shin duk ranarda Abba ya farfafo yaganta ahakan kina tunanin sai qara Jin nadama ko tausayin halinda Kika shiga?wallahi Momy tsanarmu zaiyi duk mu duka duk ranarda ya farka ya ganta depression ya kusan haukatata gabaki daya.

Momyn batace kalaba saidai sauraron Sa'adah din datake kawai tana shiga nata tunanin Dan tunda Abba yabar gidan yake asibiti Takoma koyaushe cikin tunani take
Tarasa Ina zata Kama a rayuwar,
Ta rasa Yaya zatabi tacinye wainnan jarabawan da ake jarabtarta dasu.

Washe umma Jamila tana zaune babban palon gidanta tana zubawa Mai gidanta Honourable Atiku tsohon member house of Rep coffee aka kiransa Ana sanar dashi labarin zuwan AB TURAKI Nigeria Inshallah washe gari....

Tashi yayi daga jinginen dayake a kujerar 2seater cikin sauti Mai tsagwaron neman tabbaci da mahimmancin labarin garesa yace"
Ayi Mana booking tickets tun a Lagos zamu tarbesa Inshallah zamu samu ganinsa saimu shigar da proposal dinmu Dan idan ya iso Abuja zaiyi Mana wuyar gani Amma dai na tabbatarda zai iso anan garin sbd Amininsa Dake asibiti
Amma dai ayi Mana arranging tafiyar Dole zamu tarbesa a Lagos din musamu ganinsa acan.

Yana kashe wayarsa numbern uban gidansa ya nema ya Danna Masa Kira cikin qanqanin lokaci ya isar Masa da zancen shima take yace ayi Masa Shirin zuwa Abuja shikuma acan zai tafi samun appointment na ganinsa.

Wani yawu umma Jamila ta hadiye Jin tabbacin zaizo ganin Mahmoud,
To idan dagaske fa Zainab take maganar Mahmoud ya bawa AB TURAKIn auren Laylah,
Innalillahi wainna ilaihirrajiun
Da kuwa sun shiga uku sun lalace,
Yanzu ga Sa'adah Amma zai bada Laylah?wane so yakewa uwar wannan Laylah ne da ko aciwo ya zabesu akan zainab da 'yarta
Aikuwa zata dakatarda neman Sa'adah tagani idan da gasken AB TURAKin Zai karba tayin auren Aminin nasa,
Idan kuwa ya amsa wallahi Sa'adah zasu basa a Laylah bazasu yarda wannan Aljannar duniyar ta kubuce musuba ta sauka gurin wadda batadama dangin rabawa arzikin idan taje,
Gwara Sa'adah taje Koda wulaqanci tasamu cikinsa ta Haifa musu abinda zai gaje duka dukiyar da TURAKin ya Tara da mahaifiyarsu Anne Amma basuda magajinta,
Dukiyar da su kansu basusan iya abinda suka mallakaba Amma Babu magada
Ga duniya tasaka idon ganin ko Anne din ko Turakin waye zai gaji dukiyar wani tunda ita shikadaine 'danta sai 'dan yayarta datake riqo Wanda shima yazama babban mutum
Shima Turakin ita kadai garesa magajiya sai Matarsa da itama kanta batasan iya adadin dukiyar data taraba ta qarqashin mijin nata shiyasa ma Bata damu da rashin haihuwaba Dan kuwa a duniya ita kadaice tasan ba haihuwace bayayiba lafiyar saduwa da macece baida ita Dan kuwa tsawon shekarunsa da aure Bai taba muamalar aureba da mace ko matarsa koma ba matarsaba.

Kasa hakuri tayi cikin zurfafa tunani tafara korowa Hon Atiku bayanin komai na Bawa Turaki aure da Mahmud yayi kafin kwanciyaresa saidai take ta nuna Masa Sa'adah yabada ba Laylah ba
Ya saki fuska Yana sauraron zancenta cikeda shiga tunani shima kafin yace"
Tabbas ayanda akasan kusanci da Amintarsu tun suna yara zaiyi wuya Turaki Bai karba aurenba duk da Tai Masa qanqanta Amma kasancewar yanayin ciwo na Mahmoud din zai iya amsar auren saidai mun dage da addua ya amsa Dan hakan Kamar wani saukar rahamane garemu gabaki daya.

Miqewa yayi Yana cewa"
Bari kiga nafita zansa Aminu yaje yau akai sadaka duk Ina mabuqata suke Allah ya yardar Mana wannan al'amarin.

Ficewa yayi Yana fitarda wayarsa yasaka Kiran Aminu PA dinsa
ya fice yabar umma Jamila cikin tsananin zurfin tunani kafin daga baya ta miqe tayi daki ta dauka wayarta takira babbar yayarsu daya hajiya Karima Dake Abuja tafara koro Mata bayanin abunda kenan
Take Haj Karima tace a tabbatarda anyi delay din neman auren Sa'adah din har aji daga bakin Turakin maganar auren idan zai karba kokuwa aa kafin tace aturo Mata Numbern Kawu saidu yayan Mahmud din dasuke uwa daya uba daya subi ta hanyarsa Dan kuwa shi zasu turawa Turaki akan mganar tunda Yana ganin girmansa.

Da yamma kiransu commissioner yashigo wayar Hon Atiku
Yafara musu Yan kame kamen baya Nan tafiyar gaggawa ta kamasa
Sai suka nema Alhaji Qarami Wanda shima tuni Haj Karima takirasa shikam Kai tsaye yace musu Subari sai Hon Atikun yadawo daga tafiya
Da Haka suka fara Wala Wala da zancen neman auren
Hakama umma Jamila ta ringa yiwa hajiyar commissioner din labarai dabam dabam sunata Jan al'amarin.
#MAMUH#
Kuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete
Mamuhgee @Arewabooks
*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_
*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_
*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_
*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_
*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya
*_09032345899_*
*KATIN MTN*
09166221261
*_Mamuhgee 10_*
_ArewaBooks@Mamuhgee_
_Murtala Muhammed International Airport_
'Yan media ne wainda suka samu damar zuwa suke cakude cikin mutane suna Dan baza idanuwa akan gurin fitowar baqin dasuka sauka
Wasunsu nata gyara riqon wayoyinsu,
Saninsa amatsayin AMB ALT PERM Wanda yake daukan lokaci Mai tsayi Bai zoba ga labaransa da ake bugawa lokaci lokaci akan wasu ayyukan da wasu taron da yake halarta a sauran qasashe dakuma yawanci wasu daga manyan Nan Dake yawan ziyartar qasar America matuqar suna buqatan ganinsa yasa Yan media zuwa airport din samun labarin saukarsa ayau duk da Babu tabbaci Amma dai tunda sunsamu labarin sunzo Dan tabbatarwa,.

Sanin Kota yayane yan media bazasu rasa samun labarin zuwansaba yasa Tun kafin saukarsa A Abdoul daya rigasa isowa tun satin daya gabata ya iso airport din da wuri tareda motar securities daya daga cikin securities Dake gidan gidansa na Lagos.

Sanye yake cikin navy blue _Bottega veneta_ foreign kaftan dasuka tsananin bayyanarda kyawu da haiban da Allah yayi Masa da kwarjini
Hakama manyancinsa gabaki daya a sakaye yake sbd har wannan lokacin hutu da lafiya tareda irin Rayuwar tsari da nutsuwa dayake tareda tsananin hutu da arziki da Allah yabasa suna taimakawa gurin rage manyancinsa sosai,
Wayoyinsa ne kawai a hannunsa sai wata takarda wadda Yana fitowa gabaki daya kallo yadawo kansa sbd masu daukan hotunansa dasukayo kansa securities na taresu shikuwa ko dagowa baiyiba ya kallesu direct mota suka nufa A Abdoul na gefensa bayan ya karba wayoyinsa da takardar hannunsa Yana Masa barka da sauka
Har lokacin Yan media binsa sukeyi suna daukan hotunansa tareda jeho Masa tambayoyi akan dalilin zuwansa daketa yawo na sauya wasu daga cikin manyan Ambassadors da ake zargin za'ai Wanda shine Head Amb din.

Securities ko kadan Basu Bari Yan media din sun samu isowa ko kusansa ba har yashige mota batareda yako dago kyakkyawar fuskarsa ba.

Cikin wata black BMW 7 series A Abdoul ya jasa suka bar airport din bayan A Abdoul ya kunna Masa wayoyinsa guda biyu na Nigeria
Sai alokacin ya dago ya kalli A Abdoul din tareda karban wayoyinsa Yana Nemo Numbern mahaifiyarsu Anne yasaka kiranta tareda Dora wayar Kan kunnensa.

Babban gidansa deke Victoria island suka nufa Ana parking yafito Kai tsaye ya nufi ciki Yana waya har lokacin da Anne.

Masu aikin gidan ne Mata guda biyu sai namiji daya suka ringa Dan russunawa cikin grimamawa suna cewa"
Welcome sir.

Kai tsaye yake amsa musu da hannunsa Yana Dan jinjina musu Kai duk da bai waiwayo ya kalla inda suke a tsayen ba Amma dai qaidarsa ne duk Wanda ya gaidasa Yana amsawa Koda Bai kalleka ba sbd rashin kallon mutane kamar dabiarsa ce baya iya zubawa mutum ido kamar yasan cewa idanuwan nasa na rikita mutane da kwarjininsu.

Qamshin daya fara cin Karo dashi daga babban palon na qasa yasashi Dan dago manyan fararen idanuwansa ya kalli palon take ya fahimci Mss Na'ima na garin kenan.

Kai tsaye hanyar hayewa sama ya nufa Yana sallama da Anne ya kashe wayar Yana qarasa hayewa stairs din.

Bai tsaya palonsa na musamman ba Kai tsaye Master bedroom dinsa ya nufa Wanda Yana tura kofar ya shige qamshin turarensa na _Bois Elite_ daya Gama Kama komai na dakin ya tarbesa tareda qamshin Royal Night oud Roomfresh dayake tashi shima ahankali da gyaran dakin da akai masa,
Ya nufi gaban babban mirror Dake dakin ya tsaya Yana cire maballan gaban rigarsa bayan ya aje wayoyinsa Kan wani golden table set din Dake dakin gefen babban king-size bed dinsa.

Toilet ya nufa yajima aciki kafin yafito daure da brown towel yana tsane jikinsa da wani qaramin towel din ya nufi gaban mirror ya tsaya Yana cigaba da goge jikinsa.......

Murda kofar bedroom din akai aka turo tareda shigowa gabaki dayanta cikin takun nutsuwa sai Kuma ta tsaya cak daga bakin kofar tana kallon fuskarsa ta cikin madubi shima kallo daya yayi Mata yaci gaba da abinda yake...
Chapter 11 · 0% Book details