← Book details Ni Ke Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 18

Sashe 7

Ni Ke Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nakara gyara xama nai Murmishi nace "sannu da xuwa Uncle Mami yanxu ta hau sama Fati kuma yanxu xata dawo tashiga dakine ,ya karaso ya xauna a kujerar da ke fuskantar ta yana dubanta ya amsa ta sannun da tamasa ,yace yajikin naki,kai alhamdulillah naji sauki sosai Uncle, to Masha Allah Allah ya sa kaffarane, Ameen Uncle nagode Allah yasa ka da Alkhairi, dai daibabinda Arifullah yaji kenan to me yabata take ta faman godiya?

Ransa yabaci da ya hango Uncle Yusuf yana mata wani kallo xuciyar sa na harbawa ,yaxama dole yayi gaggawar mayar da ita gidansu sannan ya bayyana mata muradinsa gareta,juyawa yayi dan baxai iya jure ganinsu tare ba,koda Yakima da ki yanakwance ne amma ruhinsa na gurinta karfa yafada mata yana sonta ,inko ya fada ta amince to ya xayyi da soyayyarta da yadade da ita cikin xuciyarta tun bai Santa har Allah ya hadasu ta wannan sandain,aranan dai dakyar ya runtsa ,washegari ,da misalin Karfe tara nasafe Arifullah xaune yake yanata xanen wani aiki da akabashi ,yakasa fitowa ko karyawa baiba Mami ta aiko Fatima kan taduba masa Moran Yayan ta inyana nan ,tako koma tace duk motocinsa suna nan bai fitaba ,waya tadaga takirasa Ya dubi wayan yayi Murmishi Mami kenan,yadagavwayan da slm.

Mami tai ajiyar xuciya Son lfy bakaxo anyi break da kai ba ?

Tan bayan taxo masa a baxata ,yayi shiru shikuma a gaskiya ba wani Abu yahanasa xuwa ba illa ganin Rabee'a kansa shi yarasa nutsuwarsa gashi ita na tashi take ba ta Uncle Yusuf take dan da alama tana sonshi tunda har gashi babu ko kunya ta tanbayesa shi ,jiya ,Son kanajina in ji Mami.

Mami na lafiya lau ina kan wani aikine wallahi amma nakusan karasawa gani nan xuwa ince dai kun karya Ku?

Um min karya amma fa Kanwarka taki sakin jiki da mu kadan taci kila idan taganka kasa ta agaba taci, OK Mami kisa Fatima ta rakota Part dina sannan ahadomin kayan karyawana akawo kinji .

Mami tai Dariya to Son gasunan xuwa tace na Baba Halima ta hadama maigidanta ture akaimasa,tai Dariya tare da fadin yanxuwa kuwa ,kamin Mami tadubi Fatima tace kira min Auntyn ki in tashirya,to Mami dakin su ta nifa inda ta samu Rabee'a ta hade cikin wani danyan leshi pink wanda akai masa dinkin sket da Riga.......!

To nagode da Addu'arku masoya Khaleel yasamu lfy sosai kuyi hakuri da wannan bayawa.

Maman Khaleel

Dinkuce✍

NIKE DA GASKIYA

💖💖💖💖💖💖💖

NA
Rabee'at Muhammad
(Maman Khaleel)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

DAGA MARUBUCIYAR :

HABIBA
KISHIYAR ZAMANI
AND NOW👇
NIKE DA GASKIYA

Dasunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 78 & 79

Dinkin ya amsheta sosai duk Arifullah ne ya dinko mata su tun kwanciyarta a Asibiti bata taba sa kayanba sai yau ,Fatima ta dubeta kai sis kayan sun amsheki kamar Yaya ya gwadaki.

Rabee'a tacika da mamakin furucin Fati ,Tace kina nufin ba Mami bace ta kai din kunan, a,a Yaya Arif ya kai da kansa akwati daya ya kawo a dinke gaba daya yaba Mami yace akai maki Asibibiti,cab lalle wannan bawan Allah mai xan cemasa ,tayi wani Murmishi ,Arifullah dai yakara samun maxauni a xuciyar Rabee'a tare suka nufo falo jikinta ruf da hijab din sallah ,Mami aranta tace lalle Rabee'a tacika ya' diyar kuma da kowani mahaluki xai so hada iri da ita, tai Murmishi tace ina kuma xaki da hijab ?

Rabee'a ta sunkuyar da kai tace Sister Fatima ce tace wai kince Yaya na nemana amma bayan nan ba inda xani.

Mami dama ta tanbayane kawai taji tabakinta,tace to shikenan,Fatima tadubeta tace Mami nace kar tasa amma tace wai bai kamata Wanda ba muharraminka ba yadunga ganin jikinka .

Mami taji wani dadi har cikin ranta ta dubeta tace hakane Fatima rakata sashinsa kafin yasoma damun mutane da waya.

. Murmishi kai nai Muka nufi sa shinsa araina nace ko meye dalilinsa nakirana dakin sa oho.tafiya mukadanyi mai dan nisa kamin muka nufi wani hadadden waje gefe guda kuma anxagaye sa da kujerun roba masu kyau Pink &light popul kalan pent din wajen komi nasa daban ne nidai kai binta nake kamar Rakumi da a kala,lalle Ya Arifullah na daban ne acikin gdn su tadaga waya takirasa cike da girmamawa tace salm Yaya gamu abakin falon ka.

Banji me yace ba nadai ga tana ta gyada kai tana Murmish ta aje wayan ta dubeni tace Aunty Rabee'a gashinan xuwa kin san tsarinsa shi ba a masa knock sai dai kikirashi a waya ko flash.

Rabee'a tai Murmishi Ya Arifullah dan ka ida tafada axuciyarta amma afili tace shikuma nasa salon kenan tajuya tana dariya nidai baruwa natafi kar yajini dan shirin da muke ya wargaje gashi inason canjin waya ,nai Dariya nace ko to shikenan, ina nan tsaye ina ta karema part dinsa kallo cike da bansha,awa sai kace mace gurin tsaf dashi babu alamun datti ko kadan,Kamshinsa shine ya alamtamin yafito naki ko wai ge sai da naji yace Hello My Baby.

Naji wani dummmm akai na My Baby nikuma ni a suwa ,cab ai kafi karfina lalle wannan bai san daga gidan da nafitoba,bacinma ni ai baxan taba auren Mai kudiba gara na auri talaka dan uwana ,In muna da rabon arxiki mayi tare...!

Kanwata Rabee'atu !

Ya katse mata tunani ta juyo da sauri suka hada ido yasakar mata wani lallausan Murmishi,
ta sauke kanta kasa yace shigomana,ta dago kai a hankali,suka sakarma juna Murmishi ya ware hannayensa tanufesa Sam takasa yimasa Musu takan rasa gane kanta indai yana kusa da ita,ya bude mata ya bata waje tashiga yaturo kofa,tajuyo da sauri yadaga mata gira alamar ya akai da ido ta basa amsar bakomi tsarki ya tabbata ga Allah lalle inda abin yake yana nan,komin na falon pink&popul ne falon ya hadu matuka yana gaba ina binsa abaya har muka isa kan Dining, yaja min kujera yace oya bismillah xauna ,nai Murmishi xaniyi magana yadoran hannunsa kan labbaina yakara nunan kujerar ,na xauna shima ya xauna kusa dani ya dubeni yaxuba tagumi kamar wani maraya,abin yaso yabata Dariya tadubesa cike da kulawa tace Yaya antashi lfy ,ya karya wuya lfy ba lau ba.

Ta xaro ido kai Yaya me ke damunka ?

Kamar yace mata kece ,sai kuma ya waske yace aiki mana da kuma kasala ga yunwa,ta xaro harshe tana kadawa kai to ba ga abincin nan ba, kaci mana, yakara karya wuya yace um gashi nan narasa mai xubamin Mami ke samin abinci amma yau nakasa xuwa part dinsu dan nai Break, saboda nan dina ,yanuna mata xuciyar sa ,tadafe kirji xuciya kuma Yaya ,yagyada kai to mai Yayi xafibhaka,kadunga cire da muwa ko kuma kadunga ragema kanka aiki kaji Yaya .

To Rabee'a tayaya xan dai na tunani alhalin tunanin yaxama dole,kedai kawai ai sha,ani ya lumshe ido yashafi cikin sa Allah sariki Mami na dayanxu kinban abinci ko abakine ,tai Dariya kamar wani yaro,yadaga gira eh mana yarone ni a wajenta,mana,gaskiya yakamata nasamo Abokiyar rayuwa wadda xata rage ma Mami dawainiyata,tai Murmishi da nafi kowa Murna Yaya dan ko xanxo bikin ka nasan lokacin nakoma gd.

Gabansa yafadi kardai ace yarinyar nan ba tasona,cikinsa yaba da kuuuuuu!

Nadubesa to Yaya kaci mana naji cikinka na kara karfa wani ciwon ya sameka ,ya dubeta aransa yace kamar da gaske ,sai kuma yasoma kokawa da kula,tai Dariya gaskiya Yaya Mami tashagwavaka yanxu kularma bakasan yadda ake budewaba,yatsaya kamar wani sakarai yana kallon ta cike da wani mahaukacin sonta,tace to bari na samaka cire hannun ,dama abinda yake son ji kenan,yakoma ya harde hannaye ,cike da kwarewa tasoma goge flet din da dan karamin towel tabude kulan tasoma samasa sinasir kamin ta bude miyar wadda akayita da ganyyen Ogun taji agushi da kaji miyar tai kyau sosai gawani kamshi na tashi na musan man,abin yaba Rabee'a mamaki da yaushe aka masa sinasir,dan su bada ita sukai Break ba,gashi abincin da take so,bayan ta xuba tadubesa tace Yaya naga flas din biyu ne, yace um duba,taduba taga kunun danyan shinkafa ne sai kuma na lifton yace samin Mutumina ,tadubesa wanne kenan ,yayi Murmishi Kunun shin kafa ,aranta tace kai duk abinda nake so shima yanaso ,tai Murmishi, taxuba masa ta mika mai yace sannu da kokari nagode da kulawa,itama Murmishi tai tace kai Yaya me nama ,har ya daga cup din xai kai baki suka kalli juna cike da burgewa tace komi nasa mekyaune ,tare suka sakarma juna Murmishi yace kefa dan Mami tace baki son cin komi ,dan haka xuba abinda kikeso ki karya xamuyi waya magana me muhimmanci,kai Yaya nafaci ,yabata rai inbaki ci to tattara nima nakoshi xanyini banci komiba kuma duk abinda yasameni to kece sila,nikuma?

Um ke !
Gaskiya yacika rigima kamar wani yaro,ita batasan xancen yafitiba sai ji tai yace dama aini Yaron Mamine dan haka indai kina son Mami kartai fushi dake to bismillah.

Badan ranta yasoba ta tsiyayi kunu kadan taxuba madara tasa cokalitana juyawa takasa sha nauyinsa take sosai, OK bari na mike naje na kwanta,tai saurin rike masa riga yi hakuri zauna zansha.yadawo ya xauna tasoma sha agankali shima yasoma ci cike da wani nishadi yake karyawa yana ta Satan kallonsa yaga ko xataci sunasir din amma yaga ko alama batadaniyya yaturo mata turen gaba oya maxa kici inba haka ba nakai ki kara gurin Dady.......!

Maman Khaleel

Dinkuce✍

NIKE DA GASKIYA

💖💖💖💖💖💖💖

NA
Rabee'at Muhammad
(Maman Khaleel)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 80&81

Oyo xokici ko in hadaki da Dady ..

Tai saurin xaro tare da fadin Dady kuma Yaya ?
Chapter 7 · 0% Book details