← Book details Ni Ke Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 18

Sashe 12

Ni Ke Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sukai ido huɗu da shi yayi mata wani irin kallo maicike da wasu sakwanni masu wuyar faɗa, ta ɗauke idonta daga nasa ta sauke wata ajiyar zuciya wadda sai da su Mami suka dubeta, wata kunyace takara rufe ta da kyar ta soma motsa ɗan ƙaramin bakinta tace "Munyini lafiya ya aiki?.

Lafiya kawai yace yana Murmishi yafaɗa Mota yatayar suka shiga sukai Sallama kamin suka dauki hanya sai gida kowannensu xuciyarsa fes, Musan man ma Mami wadda tuni tagano Soyayya tsantsa da kauna a idon Rabee'a da d'an nata.
*********
Malam Hussain kam yaji sakon Rabee'a a gun Abokinsa inda yau yacaralle yadauki na gwagwa ansha kyau Sosai Matarsa tadubesa tace "Baban Haneef yau kuma ina zuwa ko dai yau Kanwata tayi kirane?".

Malam Hussain a kai wani Murmishi yace "kai Lauratu kina burgeni wallahi shiyasa nake alfahari da ke nasan bazaki juyamin baya ba wajen neman Aurena da Rabee'a ba shiyasa nake Kara baki waje na musan man a zuciyata, a yau zani zance wajen Rabee'a karo na Farko, yafaɗa yaname lumshe idonsa, wani tuk'uk'in kishine yataso mata ak'ahon zuciyarta, a gabanta yake kiran sunan wata duk da dama indai tana son hira da shi tai tsaho to ta ambaci Rabee'a, wannan wata Kalan Rabee'a ce wadda ta sace min zuciyar mini?".

Lauratu meye kuma?

Muryasa kenan wadda tadawo da ita daga dankaramin tunanin da ya afkata, ta k'ak'aro Murmishi Wanda iyakarsa labbanta tace " To Malamina a dawo Lafiya ka gai damin K'anwata da kyau".

Zataji Insha Allah yafad'a tare da Sakai waje yanufi hanyar anguwarsu Rabee'a cike da farinciki ya shirya kalamai na banhakuri da nasiha da kalaman Soyayya irin na Ustazai.

Sai dai kash wata katuwar Mota yagani anyi Parking a kofar gidan ya hango Fararan Hak'oranta inda wani me mashin ya haska masa ita tana Dariya ta jingina da Murfin Motar, wani jiri ne yataso masa lokaci guda bai shiryaba shin waye wannan ita da tace ta daina Soyayya shin me ta mayar da shi soko ko me?
Ya kasa Matsawa ko ina itakam bata masan yanayiba yajuyane ko yakarasa yaji kuma wannan waye ko ko ya juya?...........!

To mai karatu nima bari na barku da Hussaini kutayashi alhini sanna kutayashi bashi shawara nidai nayi nan🤣🤣🤣.

*Maman Khaleel*

*Ɗin kuce✍️.*

NI KE DA GASKIYA

💖💖💖💖💖💖💖

Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 97

___K'afafuwansa sunsoma yimasa nauyi, a ransa yace yazama dole Rabee'a ta za6a ko ni ko me wannan Mota, yak'arasa cike da kwarin gwiwa wajen, Yayi masu Sallama, Arifullah ya amsa fuskarsa bayabo ba fallasa, yadubi Rabee'a wadda yaga ta sunkuyar da kanta kasa, kirjinta naduka tara-tara dan fargaba, Ya Malam Hussain zai mata haka ai tabashi no dinta, bayannan yanxu ita yazaitai da Arifullah dikda shid'in ba Sonta yake ba yana mata son kanwa da Yayan ta ne,har sukai musabaha Rabee'a batasaniba dan tayi nisa wajen tunani, Muryar Malam Hussain ce tadawo da ita dagon tunanin da ta afka, inda yake cewa "Rabee'a inba damuwa inason kiban aron minti biyu".

Da sauri ta d'ago kai tabisa da ido kawai, shikuma ya Matsa inda ya a je Frajen dinsa ya hau yahada kansa da gwiwa.

Rabee'a kam takasa ko Motsi, dik da son da take ma Malam Hussain amma kuma ta kasa koda Motsi ne kar Arifullah yayi fushi da ita.

Bakiji abinda saurayinki yafad'a ba, ai yakamata kiji da shi dan innine bazan lamunci hakaba, Malama kije kinmin tsaye a ka, Arifullah ya fad'a yana kauda kansa gefe.

tarasa bakin magana to meyake nufi da hakan? mekalaman sa suke nufine, in shine bazai lamuntaba, kuma gabadaya yacanza yawani sukurkuce kamar ba shine yanzu suketa nishad'i ba?

Ta soma tafiya ahankali har ta isa wajen da Malam, cikin siririyar Muryarta kamar mai shirin yimasa rad'a tace "Assalamu a laikum".

Yad'ago rinan nun idanunsa Wanda tuni suka canza launi daga fari zuwa jajaja, jin muryarta yasa zuciyar soma jin wani sanyi yaratsasa, duk da yana cikin wani yanayi natsananin kishi, amma bai hanasa yin Murmishi ba, ya amsa, tare da fad'in "Rabee'a Amaryar Mai rabo, shikuma wannan waye?".

Tace Malam munyini lafiya ya iyalin?

Tafad'a tare da kawar da tanbayarsa.

Yace "sudai lafiya nikam Sam babu", yafad'a tare da d'aga kafada.

Yaso bata Dariya amma ta dake tace" to Masha Allah".

Yace "ok bada muwa ni nasan yadda kika ajeni Rabee'a, nasan yanzu kindai na Sona, shiyasa kiketa min hanya hanya inba haka ba, meyasa kike kula wancan mutumin?".

Wai ke haryanxu bazaki daina san abin duniya ba haryazu iyayenki basu daddaraba a she Rabee'a?

Wani takaicine ya lullubeta tare da takaicin furucinsa, karar Motar Arifullah yasata saurin waigawa yafigeta da karfi yabad'a masu k'ura.

Wani takaicin ya kamata duk duniya bata da sama da Arifullah shine mutum na Farko Wanda yasamarmata farinciki yatemaketa lokacin da take neman temako, shine sanadiyyar samun lafiyar mahaifina, Motar kawai take kallo harya bar layin, tabbas ko ba'afadamata tasan tana son Arifullah so mai tsanani irin son da shikansa Malam Hussain baisamu kwatankwacinsa ba.

"Rabee'a inason sanin wannan waye kigayamin nasan matsayina awajanki".

Ta soma share hawayen da suka soma mata zarya a kumatunta, kamin tace " Shine Wanda nake So shine Wanda nake da burin Aura Wanda zai zauna dani batare da korafiba ko wata Mummunan fahimta ko yazargi Iyayena akan wani abu na da ban Wanda su Sam basuda masaniya kansa. "

Tanagama Fad'a tajuya tabarsa nan tsaye yana ta faman juya kalaminta, sai alokacin Yagane lalle baikamata yasaka iyayenta acikin kishinsa nababu gaira babu dalili, yadafa kansa shidakansa yasan yarasa Rabee'a bazata sauraresa ba domin yacima iyayenta zarafi akan kishinsa na banxa.

Da kyar yatada mashin d'insa ya bar layin xuciyarsa a cunkushe.

"Rabee'a kam tayi kuka sosai meyasa ita batada sa'a ne arayuwarta, to waima meyasa tafad'a ma Malam Hussain tana son Arifullah , shin shiyagayamata yanasonta, karfa tai saki nadafe tayi ba wan ba k'ani (wai karatun d'ankama) shin yanxu yazatayi ina zata sakanta taji dadi? ".

Haka tai ta kuka babu mai lallashi bacci kam yau sai dai b'arawo sudukkansu.

Dankuwa Arifullah a nasa ganin da gan-gan Rabee'a ta ce masa yazo gidan su dan tanunamasa iyakarsa to tabbas yau yagani, dama haka so yake dama haka mutum yakeji idan yaga Masoyiyarsa abin kaunarsa da wani kato can bashiba yakeji a zuciyarsa, meyasa bakafada minba kina son wani ba Rabee'a meyasa! Meyasa!!!.

Wata zuciyarsace tai saurin dawo dashi hayyacinsa na fad'in karka zargeta batada lefi kokad'an dan ita ba kafad'a mata kanasonta ba dan haka kome tama lefinkane, da ka fad'a mata da haka bata faruba, kanada daman yanxu da ka hanzarta kafad'a mata kana Sonta, inba haka ba kanaji kana gani wani can zai kwace ma ita, ko Uncle d'inka dan bashinan ne dayanzu anyi angama dan yana matukar Son ta shima, kawai malam indai kana Son ta to kacire komi kafito mata da zallar Son ta inko kaki, to sai dai ka dauki na annabawa wato hakuri.

Ya nisa tare da daukan shawarar zuciyarsa takarshe da tabashi yazama Dole ya da safe in Allah ya kai mu ya sanar da su Mami komi.

Tashi yayi yafad'a band'aki ya dauro alwala yasoma nafilfilu bayan ya idar yasoma koro addu'a samun nasara akan Allah yasa Rabee'a ta zab'eshi a matsayin Abokin Rayuwa kamin ya shafa, yabi faffad'an gadonsa ya kwanta yaja lallausan bargonsa.

(To sai muce Arifullah Allah yabamu Alkhairi Ameen.)

***********

Washe gari da safe Rabee'a ta tashi da wani matsanan cin Zazzab'i gawani ciwon kai Mai zafi da kyar ta iya yin sallah Asuba, tajawo wayan ta talatsa Number Yayana amma har tagama ringing 🔔 ba'a d'aga ba, abinda Rabee'a batasaniba shine Arifullah a Mota ya bar wayansa shiyasa bai daga wayanba tun daren jiya take kiransa dan ta bashi hakuri amma yaki dagawa.

Mama ce taleko d'akin yau gidan su baiga sharaba sannan ko kicin bata shigaba, tana fitowa taga ne yau Rabee'a ba lauba, k'udindine ta ganta da mayafi ta k'arasa d'akin da sauri tana fad'in "subhanallah meyake da munki Rabee'a?".

Ta d'ago ta a hankali ta 6a goshinta tai tajishi zafi rau, meyake maki ciwone Rabee'a? Mama tasake furtawa cikin kid'imewa.

A hankali tasoma motsa dan k'ara min bakin ta tace " kai ne Mama "

Sallamar Babanta sukajiyo atsakar gida tadawo daga masallaci, da sauri Mama tace" Malam gani adakin Rabee'a bata jin dad'i".

"Assha! assha!! Subhanallah to sannu Rabee'a ya fad'a dai dai lokacin da yashigo cikin d'akin sannu Y'ar Baba bari nafita nasamo mata magani".
*******

Bayan yatashi ya fad'a band'aki ya salla wanka tare da d'auro alwala yafito yazura jallabiyyarsa mai ruwan madara ya fito yanufi massalacin unguwarsu a get suka hadu da Daddy, bayan sundawo ya koma d'akinsa yana shiga nefa na d'auke kayansu, d'akin yaza dind'in ya shafa aljihunsa yaji wayam, sai alokacinne ya tuna da wayarsa ashe tana Mota juyawa yayi yaje ya d'aukota Miss call 📲 yagani wajen 79 kuma duk na tane......!

Maman Khaleel

Din kuce✍️

NI KE DA GASKIYA

💖💖💖💖💖💖💖

Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel)
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

Saga Marubuciyar:

HABIBA
KISHIYAR ZAMANI

AND NOW 👇
NI KE DA GASKIYA

Da sunan Allah mai rahma mai jin k'ai.

Page 98

__Ya dunga juya wayarsa yana kallan no d'inta yakasa dauke idonsa akanta,ba shida wani abinda yahuce illa yakirata.

Yasoma Neman layin amma said dai Sam wayar hartagama ring ba'a d'agaba ,yasake kira a karo na Uku Mama ta hango hasken wayan Dan tana silent ne, tace ke a nata ma kiranki Rabee'a ko waye oho?.

Yayana tagani a allon wayar a tunaninta Saifullahi ne tad'agatace " Assalamu a laikum"

Jin Muryar yayi kamar ta Rabee'a sai dai wannan tafi ta ta girma kadan,yalumshe idonsa tare da wata irin faduwar gaba a hankali yafurta "Was alaikumussalam Mama an tashi lafiya?".

Murmishi tayi jin Muryar Arifullah ta amsa da " lafiya lau yasu Hajiyar taka?".

Cikin kosawa dayaji abinda yasamu Babyn sa yace "duk lafiya suke Mama,Um ......am....Mama....Rabee'a tana kusa kuwa?".

Yafad'a yana Sosa kai kamar tana kallonsa .

Murmishi Mama tayi kamin tace" gatanan amma bata jin d'ad'ine zazzabi ne ya lullubeta gatanan kwance ".

"Subhanallah Mama yaushe ne ciwon yakamata?.
Chapter 12 · 0% Book details