← Book details Ni Ke Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 18

Sashe 18

Ni Ke Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Karka da mu insha ALLAH zata haihu lafiya ,ai bata gama rufe bakiba sai wata Nurse ta leko tace sister kawo kayan ta haihu ai tuni Arifullah ya karasa waje dauke da manyan a kwatuna ,bakinsa harkunne yana fad'in Alhamdulillah me akasamu ,tai Murmishi tace " Baby Girl akasamu yasoma kokarin sakai dakin haihuwa ,nan fa suka dakatar dashi dafadin yayi hakuri yanzu za,afito da ita dakin Hutu,yace OK nagode,waya yaciro yakira Mami yagayamata ansauka ,Mami cike da farin ciki tace "kai Alhamdulillah me a kasamu?". yace "takwarar ki ce Mami gamu a Asibiti".

Mami cike da wani Farin ciki tace wani Asibiti ne ?
Nan dai ya mata kwatance,bata sha wuyaba wajen gane Asibiti Dan ba boyayyebane acikin Kaduna millennium City.
Mami tasamu Arifullah yarike jaririyarsa kam sai faman fara'a yake ,yana ganin su Mami ya mike tare da fad'in Abba kayi sabuwar Amarya Dan Mami tazama tsohon yayi ko Dadyna?.

Alhaji Abdullahi yayi Dariya yace kwarai da gaske kuwa gasabuwa me zai da tsohuwa,Mami tayi Dariya tace " oho dai ai Dady da tsohuwar Zuma ake magani,akai Dariya Fatima wadda takosa abata yarinya tace amma Mami ai sabuwa fa akace itama ai danata maganin ,akasake yin Dariya, nan Daddy yayi ma jaririya addu'a ,kamin ya mikawa wa Mami ita ta amsa ,cike da Farin ciki yau Allah yanuna mata yar'Babanta Muhammad Arifullah,yarinyar babu inda tabar Fatiman ta kamar ita tahaifeta,nan danan jaririya tashiga ran Mami sosai,tadubi Arifullah tace "mutanan tudun wada sunji?"

" Eh" nafad'a masu ,surutun sune ya farkar da Rabee'a daga Baccin da take cike da kunya tasoma amsa sannun da kowa na dakin yake mata tagai dasu,suka amsa,bayan shigowar likita yakara dubata yatabbatar masu da babu matsala tare da rubuta masu sallama,suka rankaya akai gida.

Kullum gidan Arifullah cike yake da yan barka,Ana gobe suna Yaya Saif yazo daga kano,Wanda a yanzu yakara kyau da kiba ga Hutu Dan yanzu shine manager a kanfanin Alhaji Abdullahi Wanda ake futar da kowace roba,sakamakon sanin dasukai shine yayan Rabee'a awajan Bikinsa lokacin da yan kamfaninsu kwata suka zo taya Murnan Auren dan Megidansu.

A gidan yasamu Fatima wadda duk takasa zaune takasa tsaye Dan Farin ciki Allah yajarbceta da son Saifullahi tun haduwarsu ta farko,sai dai shima Yaya Saif din yanayin Fatima sosai ,aiko afalo tasamesa ta caba kwalliya kamar wata Amarya inda ta dauko masa yarinya aransa yace kamar tata,Allah muma kabamu yarinya nan badi warhaka Dan wallahi bazan bar garin nan ba insha Allah sai anbani ke Dan kema naga kinayina sosai,duk wannan tunanin yanayine a zuciyarsa,fuska dauke da Murmishi tamika masa Baby,ya amsa har da hadawa da hannayentawani shock suka ji a tare ,da sauri tajanye hannunta tana yarfe hanunta,Murmishi yayi kamin yace "yadai Maman Baby lfy?".

Tad'an hararesa ta gefen ido tace " um bakai baneba".

Yadda tai yabasa Dariya, "OK matso kigayamun abinda nayi ,tare da gayamun yarinya nan watabiyo mu ko Ku? ".

Ai da sauri tace "kai ai kasan Mune kaduba kagani mana?".

Um hakane kece ai wannan Babyn ,matso kiji wata magana tako matso yace haka kema nan da 9 months zaki haifomin mai kamadake nima nadunga dauka,ina goyawa,cike da jin kunya ta rufe fuskar ta tana Murmishi tare da fad'in Allah yanunamin wannan rana,batasan zancenta yafitoba ,sai ji tai yace Ameen Tawan."

Rabee'a wadda tundazu take ta sallama amma Sam basujitaba sunacen sunyi zurfi cikin kogin so,yanata nink'aya da su.

Karo da tai da mutum yasata dago kai taga Auntyn tace ai da sauri tafita afalon babu ko waiwaye.

Rabee'a ta karasa wajen yayanta suka gaisa ya mata barka tare da yimata addu'a Allah yasa sugama wanka lfy ,nabada sako abaki yana wajen Mama.

Rabee'a tayi Murmishi nagode Yaya Allah yakara budi yasa afi haka,Ameen inji Arifullah wanda yashigo gidan yanxu ake shaidamasa zuwan Saifullahi abakin kanwarsa.
Tare sukai murmishi, yakaraso sukai musabaha tare da fadin yau Ummina tasa kawu kawo mana ziyara " inji Arifullah .

Saif kuwa sai faman dariya yake to kagani,akasake yin Dariya.

Taron suna yakayatar anci ansha anraba abubuwa ,Mami akwati guda tayi nakayan Takwara haka ma Abba yayi nasa da na mejego tare da ba Amaryarsa mota yar karama wai adunga kai ta Makaranta da shan Ice cream.

Ummi nada 1year akai bikin Yaya Saif da Fatima wanda dubban jama'a suka shaida amarya ta tare asabon gidan mijinta da ke nan tudun wada wanda akaimata ginin zani,kamar ba acikin Tudun wada gidan yake komi yaji sai dai muce Amarya da Ango Allah yakawo ciki da goyo.

A watarana Alhamis Arifullah yad'auko Rabee'a daga Makaranta wadda tuni Arifullah yasaimata Admision na Kaduna state Unibasty inda take karantar Food tech.
Yau kawai taji batasan tuki tace yakaita dakuma suka tashi ya daukota itada sabon Babyn ta mai Suna Kabir wato mahaifin Rabee'a inda suke kiransa da Musannaf,kamar daga sama ta hangi Alhaji Dalladi yana tafiya akan kwalta yayi baki yakara tsufa babu Mota dagani kasan rayuwa ta canxa ,har sun gota shi Arifullah yadubi Rabee'a yace ya dai Madam lfy naga duk kinrikice?"

Cike da dimauta tace Hubby wallahi Alhaji Dalladi nagani rayuwa tajuya masa baya, Dan Allah in bazaka damuba muje katai makeshi, koda da nace fanene kaji.

Yace kar ki damu uwargida abinda kikeso shi za'ai, yad'an koma baya inda sukai masa hon ,Afirgice ya koma gefe yazuge glass din tare da fad'in Assalamu a laikum.

Alhaji Dalladi cike da jin tsoro yace wa'alaikumussalam yaro ya akai,ai kamin Alhaji Dalladi yarufe baki sai ganin Rabee'a yayi tafito yakoyi saurin fad'in Rab..Rabee'a kece !
Ya ko sa kuka ,ba Rabee'a ba har Arifullah sai da yabasu tausayi,Rabee'a tadubesa kai shiru kadai na kuka ga mijina nan kugaisa,tanuna Arifullah. Alhaji Dalladi cike da kunya yamikama Arifullah hannu tare da fad'in ykk ya yara,Yagoge hawayen da suka zubo masa yace kinga yadda Allah yayi dani lalle Usman yafini gaskiya akan hanani Aurenki da yayi domin a halin yanzu garin Aurena na Auroma kai na mai kashin tsiya ta sace komi nawa tasaida min da duk wata kadara tawa ,tagudu tabarni cikin masifa da bashin banki yanzuhaka gidana anyi gwanjonsa ,Usman ma yanzu baya gidana dan kuwa yanusan sheni kan yawan Aure Auren da nake alokacin gani nake NI KE DA GASKIYA dan ina da kudi zan iya Auro yarinyar da naga dama ,dan Allah kiyi hakuri kiyafemina ni da Yarona alhakinki ke tafiya damu domin anci maki zarafi ke da iyayenki.

Rabee' a ta tausaya ma Alhaji Dalladi tare da fad'in" yanxu kana inane da zama ?"

Ina nan Badarawa Balangu road nan nakama haya .

Arifullah ya dubesa cike da takaicin abinda sukai ma matarsa amma inyatuna wani abukuma sai yaji sanyi tunda gashi shike da Gaskiyar dan shine keda rabo ajikin Rabee'a ,ya nisa yace Alhaji bani Account dinka,nan da nan yabashi yamasa transfer na dubu dari 5 wai yaje yaja jari.
Nan fa Alhaji Dalladi yashiga godiya kamin sukai sallama cike da al'ajabin rayuwa.

Alhaji kabir yamurje yayi kiba kamar bashi dan bana Arifullah yabiya masu shida Mama suka je suka sauke faralli,kafin sudawo Arifullah yasa ancanza masu ginin gida yakoma na zamani,gaskiya sudai Auren Rabee'a bakaramin rufin asiri bane ga rayuwar su,sai yanxu yake godiya ga Allah da baisa ya Aurar da Rabee'a ga inda bata soba shiyasa inkabi komi ahankali sai kaci nasara arayuwa.

Arifullah kam yayi kyau dashi da Rabee'a ga yaransu guda 4 Ummi ,Musannaf,Hubby,wato takwaran ( Arifullah) sai Aisha ,cigaba kam Arifullah yasamu sosai arayuwar sa suna tai makon marasa karfi da gajiyayyu ,ba wai kara wa mai karfi karfi ba kamar yadda wasu masu kudi sukeyi,sun tare a sabon gidan su wanda Yagaji da tsaruwa cikin Unguwar dosa layin y'an majalisu,Hajiya Rabee'a tazama Babbar mace domin kasuwanci take baji bagani duk sati sai ankawo mata kaya Atamfofi,less,da shadda ya'yayi ,gamida kayan kicin tana dorasu a Whatsap Wanda yanxu tafara zuwa dubai da kanta don saro kayan.

Kwance take kan faffadan kirjin Arifullah inada take ta faman tumurmusan san sa yace kai Baby wai ke baki girmane?

Tako kara narkewa ajikinsa tare da yimasa wani fari wanda take matukar saurin burkitashi tace Abban Ummi Hubby na ai jina nake kamar yau aka kawoni gidan ka yarinya d'anya sharaf.

Yaja dogon hancinta yace Inagodiya da Allah yabani ke Amatsayin matata,nima a kullum nayi sallah ina kara godiya ga Allah da yaxabomin mijin nunawa sa'a.

Alhamdulillah!!!!!!

To Sai dai muce masha Allah ,Allah yataimaka yakawo kasuwa me Albarka,Yakaro maku dankon Kauna a tsakanin ku damu ma baki daya Alkhairin dake cikin wannan littafi Allah yabamu lada dani da ku masoya ,akasin haka Allah ya yafemana gabadayan mu muhadu Asabon littafina me taken Y'AN UBANE MU,Nagode taku har gobe da jibi wato:

MAMAN KHALEEL✍️
Chapter 18 · 0% Book details