← Book details Ni Ke Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 18

Sashe 10

Ni Ke Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya nisa to Maryama nagode. haka yafita jikinsa ba kwari tare da bakin cikin sanin Rabee'a wadda tazo ta war gaza masu zaman lafiyan gida, a hankali ya bud'e get din Y'an sanda yagani Mota guda tare da Yaya Saif da Malam Musa Wanda sai zare ido yake, 'Yan sanda 2 suka fito hannun su d'auke da ankwa suka sa masa suka tasa keyarsa ba ko musu sai station.

"Mai gadin gidan yanufi falo da gudu ya na fad'in Hajiya sun tafi da Alhaji".

Da sauri ta miƙe tare da dafe kirji cike da razana tace" su wanene suka tafi dashi Garba?.

nan dai Garba ya mata bayanin yadda komi ya faru .
Kwanansa daya kamin aka gano station d'in da yake. Tambayar duniya an masa, amma amsa daya ce bai san inda suke ba, Alhaji Dalladi ya rame sosai dan ma Baba yace kar a dake sa, binciken duniya anyi ma Umar ba a gansa ba, Hajiya Maryam ce kadai tasan in da ya ke i ta ma ta hanyar Y'an gidan su, amma tai shiru bata gaya ma kowa ba, har ranan da Alhaji ya fito. Shima bata gaya masa ba dan gudun ɓacin rai, tunda ita dai ya sanar da ita duk yadda Abun ya faru sai dai ya 'boye mata k'udirin sa na ya lalata Rayuwar Rabee'ah.

Wannan kenan

*************
Arifullah kwance ya ke yayi ruf da ciki a ma ke_ken gadon sa wanda yaji shin fida ta alfarma.

tuna ni ya ke shin ta ina zai soma ne¿ tabbas yana sonta, ya shafi kyakkyawar fuskarta wadda ta ke manne a jikin screen din wayarsa. sanda ya dauketa ran da xata koma gida tana Murmishi, sake shafa Hoton yayi , ina sonki Rabee'atu Ya Allah ka Mallaka min Rabee'ah tazamo Uwa ga yarana, Murmishi yayi mai tsada tare kai ma Hoton wani kiss 💋 mai kyau ya lumshe ido ina ma mafarkin sa ya zama gaskiya? Ina ma ya bud'e idonsa yagan ta kusa da shi?

Ka kira ta mana kaji Muryar ta ko kaji sanyin zuciyar ka ya duba a gogon wayar sa yayi 11.50 pm anya batai bacci ba¿ tanbayar daya yiwa kansa kenan ba mai bashi amsa, kamin daga bi sa ni naga ya Matsa kira, kamar a mafarki taji k'arar wayar ta cike da tsoro ta farka bakinta d'auke da addu'a, tasoma motsa Hannunta ta kai in da tasa caji a gefen katifar ta Yar'sale 😄 wani Murmishi naga tasaki mai sauti tare da sauke wata nan nau yan a jiyar zuciya ta soma hada kalamanta Masu taushi kamin naji tace.....!

*To masu karatu kuyi hakuri da wannan na barku lfy daga y'ar uwar ku.*

Maman Khaleel ✍️

NI KE DA GASKIYA

💖💖💖💖💖💖💖

Na
Rabee'art Muhammad
( Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 88 &89

Wani Murmishi naga tasaki mai sauti tare da sauke wata nan nau yan a jiyar zuciya ta soma hada kalamanta Masu taushi kamin naji tace "Assalamu a laikum Yayana"

Lumshe idonsa yayi saboda Muryar da tai amfani da ita tashige sa sosai bawani sanyi da ya ziyarci zuciyarsa.

"Hello Yaya kanajina? ".

Jinmuryar ta yasa shi da wowa daga shaukin da ya shiga, Yayi wani Murmishi mai sauti, kamin Yace "ina jinki K'anwata ya kike ya su Mama? "

"Lafiya lau Yaya,ina yini ya aikin da Mummy da Daddy? ".

"Yayi Murmishi Kinyi kewarsu kenan K'anwata? ".

"Eh mana Yaya da tunanin su Bacci ya daukeni Yaya nayi kewar Mumy sosai domin duk Wanda ya xauna da Mumy to tabbas ta shiga rai saboda kyawawan halayenta Yaya nayi kewarta sosaia".

Yace "Muma munyi kewarki sosai haka sukaita hira cike da farinciki da shaukin kauna, kamin sukai sallama, kowannan su xuciyarsa kal dan farin ciki, washe gari da safe ta tashi cike da wani kuxari aiki kawai take tana hasaso kyakkyawar fuskarsa wadda kullum take cikin annuri, tabbas dole Saudat ta rikice domin gaskiya shidin na da banne gashi da shiga rai ba kamar yadda ta xataba a baya, Murmishi kawai take wadda ita kanta batasan sanda take yinsa ba, Mama wadda tunda tafito take ta lurada yanayin Rabee'ah Ko mai yasata cikin farin ciki oho?.

Rabee'a takoma makarantar Islamiyyarsu inda tacigaba da karatunta Wanda ta mai da hankali sosai tunda acewarta ta a jiye Soyayya karatunta xataciga ba har Allah yakawo mata Wanda zai so ta tsakani ga Allah, a yaune kuma tasamu labarin dawowar Malam Hussain a bakin kawarta Aisha, wadda sai faman yaba kyau da kibarsa take tace"kai Rabee'a wallahi Malam yakoma kamar wani Balarabe, kece kawai a ransa har gida fa yazo yake tambaya ta wai kin yi Aure ko, sai nace masa aiko ba a yiba anfasa".

Kallon Aisha kawai take tana Murmishi tana ta kallon bakinta wadda take ta xuba kamar Y'ay'an kad'ayar da babu zaki har ta kai aya, kamin ta dubeta tace"Nagode sai dai ni yanxu Aisha Maza tsoro suke bani kuma bayan haka ma Malam Hussain ya manta dani ko kin manta da yanxu yana da Mat, wani xafi taji yataso mata a zuciyar ta sai take ganin ai duk laifinsane komi yafaru da ita shiya jawo dan da yafurta yanasonta da wuri da Alhaji Dalladi bai shigo Rayuwar su ba, wasu hawayene masu xafi suka gangaro mata a kyakkyawar fuskarta wadda ta kasa sanin ko nameye, "Aisha tai saurin fad'in meye kuma na kuka? "

Tasoma sa zaratan Hannunta tasoma share hawayen wadda itama batasan dalilinta na yin kukan ba, "Tace bakomi nima ban san kukan nameye ba kawai ni dai naga hawayen ne, "to ya isa haka inji Aisha".

Ko da tadawo gida sai tunanin hirar su ta karshe take inda yake cewa Rabee'a xanbarki badan raina yasoba, ina sonki amma yazama dole in barki gashi Iyayena sunmin mata Rabee'art zanbarki badan ina so ba sai dan babu yadda xamuyi ina maki fatan alkhairi a gidan mijinki..! ai baikarasa maganarsa ba nafada cikin gidan mu ina kuka mai cin zuciya, jin abin take kamar yanxu yake faruwa gawani kishinsa yanatasomata Sam baxan yadda da kai ba Malam Hussain karkaxo gareni kaje ka xauna da Matarka, nadaina soyayya, tana cikin wannan tunanin ne taji Muryar wani yaro yana kwala Sallama a cikin soron gidan tare da Fad'in wai Rabee'a tazo inji.........!

To Masu karatu ga Malam Hussain ya dawo ga kuma Gwarxo Arifullah shin wa zai dauka acikin gwarazan Rabee'a shin Waye kuma yazo neman Rabee'a?

Sai kubiyoni gobe in mai duka ya kai mu gobe.

Maman Khaleel

D'in kuce👌
Comment and shire

NI KE DA GASKIYA

💖💖💖💖💖💖💖

Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

Ina kuke masoyan gaskiya ina jinjina maku ina godiya da kulawarku gareni, Masoyan Arifullah sakon gaisuwa gareku ya d'aga maku Babban d'anyatsa👍 😄😄.

Wannan Page din nakine Fatima Abdurrahman ina godiya da kaunarkigareni na bibiyar wannan littafi tundaga Farko Allah ya bar kauna mai d'orewa Ameen.

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 90&91

Gabanta ya fara dukan Sakwarar Legas tare da tunanin waye kuma ita dai tasan tunda suka Rabu da Alhaji Dalladi bata karajin anyi sallama da ita ba da sunan anxo zance, Muryar Mama ta tsinkaya tana cewa" kai waye yake neman ta? "
"Um wani ne Mama nima bansan shiba yace dai inmasa iso wajenta".

Rabee'a dai tana jinsu taga in Yayantane zai kirata ne baitaba yo aikeba, "Rabee'a kixo kije kiga ko waye inji mama Tafada tare da fad'in je kace tana zuwa".

Yaron yace "to"

Tsaf take jikinta Sam babu k'azanta ta fito talek'a d'akin Mama ta shaida mata fitarta kamin ta nufi soron gidan su zuciyarta a cunkushe Malam Abubakar ne tagani tsaye abakin Baburd'nsa cike da mamaki kwance a fuskarta ta k'arasa, Shikam sai faman washe baki yake, Malam Abubakar Abokin Malam Hussain ne, to meyakawosa?

Muryar sace taziyarci kunnuwanta inda yake cewa "Barka da fitowa Tauraruwar taurari, mai rikid'a y'an maza".

Yafad'a yana Murmishi.
Itama Murmishin yak'e take Wanda iyakarsa la66anta, tace "kai Malam wannan kirari ai sai kasa mutane sukama bina da idanuuwa kamin sukawon hari".

Dariya yayi mai sauti yace" tab Rabee'atu dama haka kika iya zance?".

Tai Murmish "tace Malam munyini lafiya ya makaranta da iyalin? "

Tafada tare da kawar da nasa batun, domin takosa taji tatsuniyar da yazo mata da ita.

"Duk suna lafiya suna gaidaki".

"Ina godiya nima Malam".

Shurune ya ratsa wajen nawajen sakon goma kamin yakatse shirun da fad'in "yauwa Rabi nasan dai kinji labarin dawowar Abokina ko? ".

Tai kamar bataganeba tace "Malam wane kenan?".

Duk da yasan tagane nufinsa amma sai kuma tawaske da yimasa wannan tanbaya, Murmishi yayi yace "nasan Kinsan waye Amma Bari nakara tuna maki Malam Hussain nake nufi nine wakilinsa Inda nazo na ari bakinsa nacimasa albasa, wajen yada da, awar Soyayyarsa kamin yaxo gareki, Kinsan dai irin yadda yake sonki basai nakara fad'a ba mudai muna K'ara miko maki k'ok'on bararmu, ko da wani ma asashi a gefe Domin mune kan gaba, yafada yana Murmishi".

Wani irin hawaye ne suka xubomata tabbas da taso Malam Hussain amma yanxu batasan me yasa take jin haushinsa ba musan man ma matarsa wadda nasan yanxu suna sonjunan su sosai yana nufin zai raba masu sonne gida biyu sannan bakullum zata dunk'a ganinsa ba sai bayan Kwana 2 ta6 yanzu yadda gidan Malam Sallau haka zamuyi muyita fada kamar yadda Indo tafasama Habiba baki da muciyar tuwo, kema haka matarsa zata biyoki tadaki banxa, duk wadan nan tunanin tanayine a zuciyarta.

"Lafiya Rabee'atu Mekuma ya faru? "

kalmar dataratsa tsakiyar kwakwalwarta kenan, batasan sanda tace kuma Malam yana son Matar sa, nidai na hakura nabarmata shi, nima Allah ya bani mijina Wanda zamu zauna dagani sai shi, Tafada cikin wata irin Murya mai taushi gamida shagwaba.

" Yagane sarai kishine ke addabarta amma sai yadubeta yace to share hawayen kinji wallahi ni shaidane akan irin Sonda yake maki kuma zaki gani Idan yazo anjima kinji kidaina kuka dan Abokina bazaiji dad'iba idan yaga kina xubar masa da hawayensa masu tsada".

Tasoma share hawayen tare da fad'in "Malam ai acikin mu biyun dole yaji yafison wata ko? ".
Chapter 10 · 0% Book details