← Book details Ni Ke Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 18

Sashe 11

Ni Ke Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya gyad'a kai "Eh hakane amma ke yake so ba itaba kinjiko".

Tai wani Murmishi to Malam naji nagode da haka sukai sallama yamika mata wata Leda, amma fafur tak'i amsa, "tace Malam nagode "

Tajuya ta nufi cikin gida cike da farinciki jincewa Malam Hussain dinta yana son ta, dantuni tasama kanta aya da tunanin cewa Arifullah yana son ta duk da cewa Arifullah yana cikin wani sashi na musan man acikin xuciyarta, sai dan kawai baxata samesaba sai dai tayi hakuri domin shidin mai tsadane sai su Saudat Y'ay'an manya, ba itaba y'ar talakawaba.

"Ka tai makeni karkabari ya yatafidani Yaya! Yaya!!..........!!!!!!.

kuyi hakuri da wannan ina godiya.

Maman Khaleel
nake maku fatan alkhairi muhadu gobe in meduka ya kai mu gobe ✍️.

Comments
and
Shire

*NI KE DA GASKIYA*
💖💖💖💖💖💖

NA
Rabee'art Muhammad

(Maman Khalil) ________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

Page 92&93

"Ka tai makeni karkabari yatafi dani Yaya! Yaya!! Yayaaaaa!!!! ".

"Binsu yake amma ya gaza cinmasu cike da wani kuxari ya ke gudu yana fad'in kai wayeeee?
Ka kyaleta Matana ne, shikam sai faman janta yake iya karfinsa bako wai waye bare kuma magana duk yadda ya so yacece ta amma a bu ya faskara, yanaji yana gani wannan mutumin yaja masa Baby, cike da firgici ya farka bakinsa d'auke da addu'ar mummunan mafarki yatofe ko ina na dakin kamin yakara maida kansa gefen damansa ya kwanta amma abin mamaki bacci ya gaza daukarsa daya kulle idonsa ita yake gani cikin hawaye tana miko masa zaratan Hannunta, ya mike ya zauna tare da fad'in ya Allah ka kare mu daga dukkan abinda zai damemu ya Allah katsaremun Rabee'atu na ya sa tazama mallakina ta zamo Uwa ga yarana yafada bayan ya ida Sallah nafila ya shafa kamin yakoma ya kwanta cike da tunaninta".

Dawuri yau ya shirya zuciyar sa yau a cunkushe take Sam bata masa dadi yayi kyau ainun cikin shaddarsa galila main ruwan Bula ya dauki hularsa Minister yadora akan sumarsa wadda take samun gyara akai akai ga sajansa Wanda ya kwanta yayi luf- luf a kyakkyawar fuskarsa ya daura wani tsadaddan a gogon sa ya daura asaman tsin-tsiyar hannunsa, Wanda sai faman daukan ido yake yakoma wajen takalmansa ya dauki takalminsa k'irar Italy kalan shaddar yafito sai faman kamshi yake yana taku d'ai d'ai, Arifullah kenan yaro dan kwalisa yaro mai tashe ga kuruciya ga Nera, cewar Mumy wadda take zaune a falo tafada acikin xuciyarta, sai faman Murmish take tare

NI KE DA GASKIYA

💖💖💖💖💖💖💖

Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel )

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

Daga marubuciyar :

HABIBA
KISHIYAR ZAMANI
AND NOW 👇
NI KE DA GASKIYA

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

page 94&95

Sai faman Murmishi take tare da fad'in"
Lale marhabin da D'angidan Daddy,wannan gayunfa kamar zakaje wajan surukar Daddy? "

Yasoma shafa k'eyarsa yana d'an Murmishi yakaraso Falon ya xauna kusa da Mahaifiyarsa ya soma gaidata, ta amsa tace "wai Arifullah yaushene zaka kaini gdn su Yarinyata ne wallahi nayi kewarta sosai".

tasosa masa inda yake masa k'ai k'ayi ya Murmusa yace to ko muje na ajeki agidan su, Fatima tafito daga d'akinta taji ana fad'in za, a ajeta takaraso cike da d'oki tace "Mami ina zaki? ".

Tai Murmishi tace" gidan 'Yata Yaya zai kaini".

Cike da farinciki tace" Yaya nima zani dan Allah kaji?".

Yayi Murmishi Yace "kai Auta Kinsan ina zata ne?"

"Eh" mana nasani wajen Sister Rabee'a mana Mami zataje ko Mamina?.

Mami tai Dariya tace "can zamu je kishirya ".

"Dama nasanarwa Daddy Kila muje gidan su Rabi asatin nan indai bakada aiki a wannan weekend din".

Fatima tai d'aki da gudu tana murnan yau zata ga Rabee'a da kyakkyawan Yayanta shiri take na kece raini tafito cikin wata doguwar Riga Marun wadda taji stone, sai d'aukan ido take, ta yane kanta da gyalenta tafeshe jikinta da turarukanta masu sanyi kamshi, ta d'auki takalminta mai tsini ta fito fes da ita, Mami tadubi yaranta aranta tace Masha Allah lalle Auta ma fa takawo itama.

"Mami nayi kyau?
Inji Fatima tafada tana juyawa a falon.

"Masha Allah kinyi kyau Auta, "yauwa Mamina nagode"

Ita kanta Mami tayi kyau cikin atamfarta k'irar Holland mai ruwan dorawa , Wadda akai Mata zanen Kore a jikinta, ta dauki gyale Shima Kore, tasa flat shoe kirar Italy kalan zanan atamfar, gawani kamshi tana fitarwa na Musan man, a mota suka sami Arifullah.

A mota hira kawai suke yanajinsu zuciyarsa fes farinciki yabiya wani Babban super makert yayi mata siyayya gamida kayan kwalam kamin yadauki hanyar Tudun Wada, suna shiga cikin layinsu Rabee'a, yayi parking a gefen gidan su , Mami da Fatima suka fito suka nufi cikin gidan Fatima nagaba duk takosa taga Rabee'a.

"Assalamu a laikum "
Fatima tafad'a acikin soron gidan su Rabee'a, gidan shiru dan Mama Bata nan ta shiga Barka mak'ota, kamar a mafarki tajiyo Muryar Fatima takara kasa kunnenta shin bagizo Muryar Fatima take mataba?

Sai da takuma jin Muryarta akoro na biyu, kamin tamike daga dogon tunin da tasava na Arifullah Wanda ko yaushe shine aranta sai dai kuma yamata nisa shi ba tsaran Aurenta bane, Malam Hussain shine dai dai ita, sai kuma ga muryar Fatima wadda ko a ina taji ta zata ganeta, tafito aikuwa da gudu Fatima tanufo Rabee'a tana murnan ganin ta, tarungumeta suna Murnan ganin juna,

Mami kam sai faman Murmishi take sun matukar burgeta, Rabee'a ta shiga jinin jikinta tana ma d'anta sha, awar Aurenta domin gaskiya sundace da juna, zataso taga yaran wadan nan taurari guda biyu kowa yana kayan kyau, Rabee'a ga tarviyya ga hakuri da girmama nagaba da ita gaskiya Rabee'a ta cancanci a sota,sai da suka dawo hayyacinsu daga Murnan ganin juna, cike da kunya ta nufi Mami tace sannu da zuwa Mami kushigo, takaisu d'akin Mama ta shinfid'a masu Darduma

Suka zauna takawo masu ruwa mai sanyi, Mami takarba ta sha kamin ta gaida Mami, Mami ta amsa tace ina Mamanku?

Tayi Murmishi tace" taje bayan mu barka tana hanya yanxu, zata dawo bari nadauko wayana nakirata".

Tana cikin neman layin Mama sai gata tana fad'in Aslm.

Bak'in takalma tagani nan dai takarasa ta shiga dagani babu tanbaya wannan itace Mahaifiyar Arifullah, nan suka yini suna ta hira Mami da Mama kamar daman sun san juna, misalin karfe biyar dai dai Yaya ya dawo, yakira ni cike da wani farin ciki nad'aga waya tare da fad'in" Assalamu a laikum Yayana .....!

Nabarku lafiya.

Maman Khaleel

Comments

and
share

*NI KE DA GASKIYA.*

💖💖💖💖💖💖💖💖

*Na*
*Rabee'art* *Muhammad*
*(Maman Khaleel ).*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.*

*Page 96*

___Ya lumshe idanuwansaa ya buɗe su a hankali kullum muryarta kamar sarewa dan dadi shikansa baisan yana da muryar da yayi amfani da itaba wajen faɗan " Amin wa'a laikis sallam ya ma'abociya kyau da Murmushi ya Tauraruwar Zarah mai haskake taurari Rabee'a da fatan kina cikin koshin lfy? ".

Wani Murmushi naga Rabee'a tana mai kwantawa a zuciyar masoyi Wanda yake da matuƙar wuyar futa a cikin zuciyar masoyi, tunda take akwai wanda ya iya kiran sunanta cikin Murya mai taushi irin Arifullah, bata gajiya da jin muryar sa, tasauke sanyayyar ajiyar zuciya wadda sai da Arifullah yadauke wayan a kunnensa ya lumshe ido, tace "lafiya Alhamdulillah Yaya Arifullah".

"Yau sai ga su Mami ko sunmaku zuwan bazata, Arifullah ya faɗa".
Ai kam nagode ma Yaya naji daɗin ganinsu,"Yaya ya Aunty Saudat?".

Duk da yagane sarai amma yace" wacece haka?"

"Haba Yaya Aunty Saudat fa Budurwarka fa nake nufi, tafaɗa cikin shagwaɓ".

"Sam ni banida Budurwa me suna haka ni Budurwata sunan ta metsadane amma ita Sam batasan ina yiba nikaɗe nake kiɗana nake kuma rausayawa tare da rangaji".

Tayi Dariya tace "to dama Yaya ka iya rawa¿ tabbbb.

Shima Dariyar Yayi yace "um mana banyi rawaba ma sai ranar da Babyna taxo ta amshi Soyayyata tazo gidana wai a ranan hmmmm, kedai bari yanzu kina ina ne? ".

tace "ina ɗakina"

"Ok " naga yamma nayi kice ma Su Mami sufito mutafi karna rasa jam'in Magariba".

"Kai daman kana ƙofar gida?".

Yayi Murmishi "yace tuntuni, nasan ko nace kizo ɓatamin rai zakiyi da wannan kunyar taki, shiyasa ma bansanar da ke ba".

A ranta tace Yanzunma bazan iyaba, amma tace "haba dai Yaya dane amma yanxu nadaina sai dai ina jin kunyar Mami sosai ta ganmu tare".

A binda Rabee'a batasaniba shine Mami tundazu taji komi dan yakirata ya shaida mata yakaraso,yace "ok nagode da har ina shirin cewa gobe zan kawo tawa ziyarar ta musan man a she bazansamu gatan kulani ba, kai Yaya ba fa haka nake nufi ba kazo mana wallahi Yaya nayi kewarka sosai, yaji daɗin kalaminta yace ok nagode.

Rabee'a!
Mama takira sunan ta, tacigaba da faɗin kifito kuyi Sallama kinshige ɗaki kina ta shewa keka dai a waya.

Ta datse wayan tace "to Mama ganinan ta fito cikin jin kunyar Mami wadda tace a,a Mama kibita ahankali, kika sani ko da sirikina take waya?.

Ta sunkuyar da kanta ƙasa tana Murmushi, Fatima a zaure take cewa "Rabee'a wai ina Yaya Saif ne naga tunda mukazo bangan saba, Rabee'a tai Murmishi ta dube ta kamar yadda tai mata tambayar cikin raɗa haka itama ta bata amsa da cewa"Yana Kano tunbayan dawowata gida yakoma".

Fatima ta rausayar da kai tace" Allah ya temaka".

"Ameen".

Kai Masha Allah kalmar da tafito daga bakinsa kenan sadda suka jero ita da Fatima sai yake ganin Fatima Mummunace a kan Rabee'ar sa.

Har suka Kara so bakin Motar cike da ladabi ya fito ya gaida Mama, Mama ta amsa tare da faɗin "karka ƙara zuwa gidan nan katsaya a waje ai nan gidan kune dan anzama ɗaya".

yace" to Mama nagode"
Ya faɗa yana Satan kallonta Sam hankalinta bai kansa suna cen suna magana ƙasa ƙasa sai faman Murmishi suke, yamike yace" ya isa haka Fatima suruntun na gida bai isaba?"
Chapter 11 · 0% Book details