Sashe 3
Ni Ke Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
To tafada tareda sauke labulan dakin.
Tundaga nesa yahangota tsarki ya tabbata ga Ubangijin wannan halitta,lalle dole Baba yadage yaga kala wannan shila haka,yayi Murmishi yaga sai faman waige waige take gakuma waya a hannunta,ai insha Allah nine xankwashi romon ba kaiba ya lashi labbansa yasoma kiranta tadaga naji yace hello Baby na ganinan cikin bakar motar ,ta juya taga yabude glass din sa ya leko yana mata murmishi n yaudara.
Ta nufesa cike da kwarin gwiwa,bayan sungaisa yadubetayace wai dan Allah in tanbayeki mana Baby?
To inajinka tafada tana murmishi.
Dan Allah wa Baba xai auramaki ?
Nan da nan annurin fuskarta ya canxa,tayi kwal kwal Idonta yaciko da kwalla,kai !
Am sorry my sweet heart danasani banyi miki wannan tanbayan ba,yafada tareda dafa goshinsa,tayi murmishin yake kai haba bahaka bane kawai in natuno mutumin ne sai raina yabaci ta dalilinsa malamina mai sona yadaina kulani wanda komi nawa yasani shine mai sani farin ciki,amma caxuwan wannan dattijon yawargaxa man shirina Wanda duk Wanda yaganmu sai yace mu masoyane duk da bai furtaminba amma alamu sun nuna haka ,amma dagajin labarin wannan tsohon yace nabi umarnin iyayena indai inaso yayi alfahari da ni.
Takarasa fadin haka tareda wasu hawaye masu xafi gwanin bantausayi dole nahakura,shima kuma dama iyayensa sunbashi mata ashe yace a,a ni yake so amma daga baya ya amsa sukai aure yatafi da ita karo karatu.
Kai amma lalle wannan malamin naku yacika masoyi tunda har ya iya sadaukar da soyayyarsa ga wani.
Ya sunan Wanda akabakin ?
Alhaji Dalladi mai nera,tafada kai tsaye .
Yaxaro ido kai ! kai!! kai kikoka lalle dole ki koka,yafada yana girgixa kai da sauri tadubeshi tare da xare ido lahhh kasan sane?
Yadaga kai alamar "eh" nasan sa bayan mu yake lalle xai mai daki karamar baxawara wannan auri sakin,cab kinga yaran gidansa ne kamar Almajirai to abincima bai ishesuba bare kuma sittira,lalle Baby dole kikoka.
Jikinta yayi sanyi dagske Usman haka yake ?
Haba xanmaki karyane ai tsakanin mu ba wannan,um ba dan kar ace na hana raya sunnaba to da sai ince tunwuri kar Baba tasake yabashi aurenki,dan wallahi kema da kinshiga kina samun ciki xai koroki gd dan bai son haihuwa,nakega fa kamar ance fa yaransa 25 kuma kinga inhar kikaje gdn to dole kimasu wanki girki,gakuma uwa uba uwargidansa batada hakuri.
Rabee,a dai duk ta tsorata sosai dama menema sai kuma gashi ansa mu a ar ha,cikin kaduwa da labarin tadubesa kai wa yake baka wannan labarin ,wata mata ce tasoma aiki agidan dataji wiya tabari shine take ba danta labari shine yaxo majalisa muna hira dayaga yaron gidan xai wuce yasoma bamu lavari,ni dai amma!
Sai kuma yy shiru .
Takara gyara tsaiwa cikin na,am da labarin da yabata tace karka damu ni wallahi naji dadin haduwarmu kaga in naje gd xansanar da Mama inma kiranka xa,ai sai kaxo kafadi GASKIYA.
Yayi Murmishin samun nasara,dan yasan flan din sa yasoma karbuwaya karyar da wuya yace to shikenan ,nidai Allah yagani bawai dan inasan ki bane nafada maki GASKIYA nadawone dan karki fada halaka.
Tai Dariya kai ai nagode ai a wannan xamanin Wanda xai fadamaka GASKIYA sunyi karanci.
Ahaka suka rabu akan sai sunyi waya,takoma gd cike da tunani kala kala ga tsanar Alhaji Dalladi.....
To kundaiji Usman yaxo yashirya xance shin dagaskene ko akasin hakan shinbabanta xai yadda in akabashi labarin?
Sai kubiyoni insha Allah gobe nagode
Nagode
Maman Khaleel
Dinkuce✍
please🙏
Comments & share
WhatsApp no
07064341892
*NIKE DA GASKIYA*
💖💖💖💖💖💖💖
*Na*
*Rabee'art Muhammad*
*(Maman Khaleel)*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]
*Page 16&20*
Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.
Kwance yake yy ruf da ciki a luntsuma luntsiman kujeru na alfarma masu ruwan cofee and bround wanda dagani ba sai na bata lokacin fadin tsadar suba wanda suka xagaye falon wanda yake dan dai dai sun cika falon fentin falon ma kalan kujerunne,daga gefen hagu kuma kwai dakuna guda biyu ajere ,na kara wara idona nahango wata kofa wadda ke rufe da alama kicin ne,
Gawani katon flasma manne da jikin bangon dakin yana kallon labaran CNN tunda aka nuno wasu bayin Allah Wanda aka kama su saboda babu kudin fansan su aka hallakasu, ga sanyin ac na ratsasa tunani yake wai yaushe kasar mu xata dai daita ne kamar kowace kasa shidai wallahi da yasani yashiga aikin soja Dan tamakon kasar sa duk da sojojin na kokari wajen bayar da tsaron sai dai kash!
Bindigogin da suke aiki basuda inganci da mugayen tafi tasu karfi da lafiya shin haka kasata xataciga ba da lalacewa yan'ta adda na tsula tsiya kamar baxa ,a mutu ba kai kasa ta daga boko haram yanxu kuma ansamu wai kidnappers lalle yaxama dole mutashi da addu,a Allah ya kawo makasata dauki,saboda yasan komujima ko mudade dole da yakammala karatunsa ya dawo kasarsa ta gado watao(Nigeria).
Yagyara kwanciyar sa aransa yace gaskiya da ni wani mai fada akasane aji danace duk Wanda aka kama akashe shi kamar yadda suke farautan rayukan all,umma.Allah kasa muga karshen wannan masifa datasawo mana kai Ameen.
Yamike yy mika Wanda hakan yabani damar kare ma kyakkyawar surarsa kallo dogo ne kakkaura me faffadan kirji,baki ne amma ba sosai ba xamu iya kiransa da dai wankan tarwada ko ince coculate colour. Yana da dogon hanci Wanda yamasa cif tare da Dan karamin bakinsa Wanda yake da wani shef mai bansha,awa gashida manyan ido da gashin gira gashin sakam baki ne sidik yawani nan nade yabada wani style mai bansha,awa kai sai dai muce barakallah masha Allah Arifullah yaro mai tashe mai cike da kuruciya ga ilmin sa Wanda yahada duka kowanne ba a barsa abaya ba,Wanda dalilin sa kenan na xuwan sa kasar Japan Dan yin kos din sa akan karatunsa na Computer injiniaring Wanda yakware sosai indai akan Computer ne dole asara masa,gashi ya kware akan fannin xane xane.
Alhmdllh yasamu abinda yaxo nema Dan kasar Japan ma tana son aiki dashi awani kanfani inda makarantar su ta turashi IT.
Yau saura wata daya dai dai yadawo gida,Dan ya kammala abinda yaje yi,daret cikin daya daga cikin dakunan falon yanufa yafa da ban daki bayan ya fito yashirya tsaf cikin kananun kaya wandonsa baki mai wadatattun aljihu,Wanda gayun wannan xamani suke yy yasaka jar t-shirts mai gajeran hannu yadauki wata kangul baka da rubutun ja ajikinsa ya dauko kanbas din sa Wanda shima bakine mai sirkin ja,ya feshe jikin sa da tsaddadan turaren ya fito cikakken Namiji Ingarma
( nikai na sai da nace wai xanso ace ya auri yata inda inada ita🤣🤣🤣 amma sai dai kash na merabone)
Gaskiya yahadu wayar sace tasoma Neman agaji ya duba naga yy Murmishi Wanda yakara fito da ai nahin kyan sa.ya daga Aslm .
Naga yaxari key din motarsa ya fito ya kulle gidan ya fada Mota wadda tadace da shi Dan tayi masa kyau sosai.
Har yanxu waya yake jin ya ambaci mami yasa nagane da mahaifiyarsa yake wayan bayan yagama ya maida hankalin sa kan tukinsa har ya shiga cikin makarantar su inda nahangi wasu samari guda biyu xaune suke gefen su kuma wasu tsula tsulan yan,matane suna ta hira ga lemunan gaban kowannan su,Hannah itace tasoma ganin ster dinta Wanda ganinsa tunda ga nesa tasoma murmishi,Haneefa tadubeta kekuma ke..!
Ai bata karasaba taji shewan su Al,Amin suna fadin sai Babban Yaro.
Tafiya yake cike da Kasai ta har yakaraso wajen suka mika masa kujera ya xauna tare da mika masu hannu yana murmishi, nan fa yan matan nan suka soma shiga tai tayin su Dan Arifullah namiji ne akwai tsare gida, banda amsa gaisuwar su da yy babu abinda yakuma hadasu yaciro wayansa yasoma latsawa,Al,amiyan'maxautumina amma yakamata kamin katafi Ku dai dai ta kanku da Hannah Dan Allah katausaya ma yarinya taxurma da yawa,Hashim yy Dariya yace sosai kam ni wallahi tausayi ma take ban,yi yai kamar baisan sunayi ba Dan shi Sam tsarin sa bb yaudara aduk lokacin da yace ma yarinya inasonki to tabbas aurenta xaiyi,Dan bashida ra,ayin soyayyar minti,kuma shi Sam baida ra,ayin auren macen da tawaye Sosai kamar Hannah, sanda yadago kai sukai ido hudu yakara tamke fuska tamike da sauri fuskarta cike da kwalla,ta nufi hostels dinsu ,shikansa sai yaji bai ji dadin abinda yamataba amma yaxama dole na sauke wannan kayan a kai na .
Suma sauran kawayanta sukai ma nasu gwaraxan sai sunhadu anjima suka ce to My Babys,sukai dariya cikin yauki suka bar wajen inda shikuma yaji dadin tafiyarsu,ya dubesu yace Al'amin kai kafi kowa sanin wayeni tun muna gd Dan haka kai mai ba wani labari ne kan ni banda lokacin wasu yan,mata kuma yaudara bahalina bane kuma ba wannan ba ma ni banda ra,ayin auren mace Ya'jami,a dan gara gara ma in tana dakina in inada ra,ayi nasata da hannuna shima nakafa mata sharudda.
Hashim yanisa kuma haka ne kafimu gaskiya amma yaxama dole to kasaurareta ko so daya ne kabata hakuri,muma xamu bata,sai tanemi wani.
Da dai yafi mata,saura sati daya yataho gd yasamu Hannah xaune tayi tagumi abayan wasu bishiyoyi iska na kadawa ahankali ta tsunduma can cikin tunanin ta sababbe,na masoyinta Wanda shi Sam bata axuciyarsa,taji muryar sa wadda ko cikin mutane dubu taji xata ban banceta,kir takafe shi da mayatattun kallonta Wanda take wasa da hankalin yan'maxa,amma shi Sam ko birgesa baiyi,ya dauke kansa gefe, yasoma magana kamar haka"Hannah naxo gareki ne Dan namiki godiya visa kaunar da kike min ,sai dai ina mai matukar baki hakuri visa kalamin da xakiji daga gareni,na kiyi hakuri nama iyayena alkawari kan auren wata yarinya in nakoma gida,Dan Allah ina mai baki hakuri tare da yimiki addu,ar Allah yabaki miji Wanda yafini komi arayuwakinji kanwata.
Tunda yasoma magana hawaye suke ta xuba akyakkyawar fuskarta kamar fanfo sai da taji furicinsa na karshe mai hade da rarrashi,ta mike kamar xatai magana sai kuma ta fasa ta ruga aguje ,tsayawa yy kamar mitam mutumi har tabace masa dagani kafin yada ga kafada aransa yace gaskiya nafada maki .