Sashe 13
Ni Ke Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inji Arifulla ya fad'a cikin sauri.
Mama tace ka kwantar da hankalinka insha Allah zuwa anjima in tasha magani zata warware dan Malam Yaje wajen liti me chamis ya had'amata magungunan kaji?".
"To Mama Allah ya sawake yasa Kaffarane ya fad'a tare da kashe wayer sai Faman juya ta yake yanata faman safa da marwa hankalinsa da ruhinsa suna wajen Rabee'a da yakulle idonsa ita yake gani Sam yarasa sukuni ,koda yaje sashin Mami Dan gaidata take tanbayarsa me ke damunsa,cemata kawai yayi Bakomi jiya bai samu bacci bane saboda wani aiki da yayi jiya",bakinsa yaji kawai yana zuba ma Mami karya abinda baisaba ba,tadubesa tace "ok Allah ya taimaka adai dunga rage aiki anasamun isasshen bacci".
Yayi Murmishi to Mama, wai yaushe Dady zai dawone nakosa yadawo,
Tadubesa cike da kulawa tace " asatinnan zai dawo insha Allah, ya akayi akwai maganane?".
Yasoma Sosa kai yana Murmishi yace "Um Mami dama kan Maganar Yarinyar da nake sone" .
Mami tak'ara gyara zama cike da farin ciki abinda tadade tana Rokon Allah kenan yau gashi lokaci yayi Arifullah dakansa yau yake maganar Aure,tadubesa kamin tace "to masha Allah a ina sirikar tawa take?".
Yasoma shafa lallausan gashin kansa Wanda yake kwance luf akansa Wanda yake samun gyara akai akai yawani kwanta kamar na mace,yace " Mami yarinyarkice ai Allah yasa ma kubani."
Mami tayi Dariya tace Muhammad Arifullah fad'amin wata y'ar tawa kakeso inji in zan iya aurama".
Kansa na k'asa yace "Mami bawata bace Rabee'a".
Aran Mami tasbihi take da godiya ga Allah da ya amshi addu'ar ta ,cike da firin ciki tace Masha Allah, Allah yasa Alkhairi Allah yasa kuma a yi damu.
"Ameen Mami"
Bayan sun d'an ta6a hira wadda tashafi Rabee'a,an an ne yake shaidamata rashin lafiyar Rabee'a ,in da Mami, tasoma fadin to ka hanzarta kalekata kaduketa ka kaita Asibiti ya dubata kaji.
To Mami zan yadda kikace.
yamike yace "Mami bari natafi daga can nawuce Office kar namakara ".
Yafada yana kallon agogon da yake daure a tsintsiyar hannunsa.
To Allah yatsare a gaidata kamin muzo dubiya.
Mami ta fad'a tare da Murmishin Farin ciki.
*******
Rabee'a kam jin Muryar Arifullah yasata jin wani sanyi acikin zuciyarta akalla tasamu saukin rad'ad'in da zuciyarta take mata sai dai haryanzu kanta namata wani irin ciwo,fuskarsa kawai take son gani,kozata samun sanyi a cikin zuciyarta,tanaji Mama tana kwantar masa da hankali,Baba yashigo yana fadin kinga Maman su Liti bai budeba sai zuwa anjima yanzu ki tanbayeta da me take son karyawa?.
Mama tace to Malam tashafa mata kai kamar mai shirin rad'a tace" Rabibina sannu kinji mezakici kamin anjima Babanku ya amso maki Magani".
Ta danyi Murmishi badan tanason cin komiba Dan Sam batasan cin komi ko ganin komi in ba Arifullah ba,ganinsa shine samun kwanciyar hankalinta,amma dan ta kwantar da hankalin Mama tace "Mama a kawo min Masa ".
Mama tace to talek'a tagayama Baba ,baijima ba yadawo Mama ta amsa kadan naci nature kwanan nazame na kwanta.
Kamar daga sama naji wata Murya Mai dad'in saurara da sanyi a zuciya,ga kamshinsa Wanda yacika gidan gabadaya ,wani sanyi ne yaratsa zuciyar Rabee'a takara bude hancinta tana shakar Daddad'an turarensa,bayan sungama gaisawa da su Mama tare da tanbayar mejiki,suka amsa masa da sauki,Mama tai masa jagora hardakin .
Kara kulle idona nai kamar mai Bacci Mama tasoma dan jamin yatsa a hankali tare da Fad'in Rabee'a ga Yayanki nan yaxo dubaki.
Nasoma motsa jikina a hankali,Wanda yasoma birkita Malam Arifullah namike Sam na manta jikina babu wata rigar kirki,Mama tana tashina tai gaba abinta tana Fad'in zauna mana ga waje tanunamasa kan Dadduman dakin Rabee'a wadda dakyar tai Sallah a kai.
Kallonta kawai yake babu ko k'iftawa duk tayi wani fiyau da ita kamar ta dad'e tana jinya,to me yasameta haka?
Tanbayar da yake ta ma kansa kenan ,itakam ganin kallon nashirin yin yawa yasa tadubi kirjinta taga komi nawaje kamar babu komi ajikinta da sauri ta bud'e baki tare da kallansa da sauri taja mayafinta ta rufe jikinta.
Yayi Murmishi aransa yace kwana nawane zasuzama mallakina nayi yadda naso dasu,ganin kirjinta Wanda yacika da nashanu tam yakara tayar masa da sha,awa abinda bai taba jiba ,lalle yakamata nasamu me d'ebemin kewa ina bukatar mace kusa dani matuka yayi a jiyar zuciya,yalumshe idonsa ya bude a hankali,sukai ido hudu dashi inda yakamata tana Satan kallonsa,Murmishi yayi tare da Fad'in kalleni mana,ta kauda kai gefe tasoma wasa da zobenda yabata,"yayi Murmishi to ni Bari nagaidaki tunda ni baza a gaidaniba nazama sirikinki ko ,to ina kwana Y'anmata yajikin?".
Dariya taso kufce mata ta d'an turo baki cike da shagwaba tace" kai Yaya wai Y'anmata ni ka bari banaso".
"Dariya yayi tare da Fad'in nimakidaina Cemin Yaya" ya fad'a tare da kwaikwayon muryarta.
Tai Dariya tare da rufe fuskarta tace "To ina kwana Yaya ya su Mami?".
Yadubeta cike da sha'awar yadda take shagwaba komi nata burgesa yake ,ya amsa da lafiya lau suke, nikam balau dan jiya ke da saurayinki kunhaifarmin da wani sabon Ciwo anan d'ina".
Yanuna mata gefen kirjinsa ,tadubesa da sauri tana dan zare ido tare da Fad'in ciwo kuma yagyad'a mata kai,alamar " eh".
"Yanzu dai kishirya muje adubaki a Asibiti".
Kai Asibiti kuma Yaya ,aranta tace nikam nawarke dan ganinka shine magani kuma Alhamdulillah.
"Tunanin me kike daga an ambaci sunan AsibitiK'anwata?".
Ya fad'a tare da mikewa kiyi sauri ina jiranki a mota ,wannan Umarnin Mami ne ,tace maza nakai mata d'iyarta taga likita .
Yana kai wa nan yafita tare da Fad'in kiyi sauri kishirya zani office karkisa na makara.
D'akin Baba yakoma yamasa Sallama tare da Fad'in "Baba dan Allah zankaita Asibiti a dubata" .
To!to!! Madalla nagode Allah yasaka ma da Alkhairi.
Ameen Baba ba da muwa nan ya a je masa wasu kudi masu dan kauri sannan yamike yafito dai dai nan kuma Mama tafito daga D'akinta hark'asa Arifullah yadurkusa yace to Mama zan tafi amma dan Allah inason kai Rabee'a taga likita .
Mama tace "kai ai bakomi duk d'aya nadauke ka da kai da Yayan Rabee'a sai kun dawo Muna godiya a gaida Hajiya" .
A mota Rabee'a ta sa Mesa ya bud'e mata wajen mezaman banza takai hannunta tabud'e k'ofar takai kanta cikin Motar wani sanyayyen kamshine yadoki hancinta ta shak'a tare da zura sauran jikinta a cikin motar sanyin Ac da daddad'an k'amshin turaransa sungama cika mata ruhi ,ta jingina kanta a kujera ta lumshe idonta jikinta duk ya saki tarasa meyasa aduk sanda suka kasance tare takan rasa nutsuwarta,yadube a tsanake yace" yadai jikinne ?".
Ta bude idanunta a hankali tasauke su a kan kyakkyawar fuskarsa yasakar mata wani yalwataccen Murmishin inbakeba....!
Tako so tagane yaren itama,tamayar masa da martanin Murmishin tace" um amma da sauki".
OK Allah ya sawake ko My K'anwas.
Yafada tare da rufe motar yatada Suka soma tafiya a hankali babu Wanda yakuma magana sai dai bugun zuciyoyinsu Wanda suke sauka kusan atare,ko wannan su da tunanin da yake a zuciyarsa,Rabee'a tunanin da take inama karsu rabu inama ta xamo matarsa uwa awajen ya'y' ansa, wai da ta ca6a.
Shikam addau'a yake Allah yasa takarbi soyayyarsa kar ta watsa masa k'asa a ido,wai in Allah ya mallaka min Rabee'a ya juyo ya kalleta yayi wani Murmishi lalle zansha gara.
Giwa Hospital ya shiga ya gyara parking yadubeta yace to bismillah ko in taimaka makin ne ?
Da sauri tace a,a zan iya nagode tare suka fito amota Kai Masha Allah abinda najiyo wata mata wadda take zaune a gefen wajen fulawa suna magana da wata dagani d'iyartace ,yarinyar tajuya inda Maman take kallo GASKIYA wannan dagani ango da amaryane danko sundace da Junansu Mama.
Maman tace kwarai ma kuwa dagani yarinyar kamar tanada shigar ciki.
Karaf a kunnen Rabee'a taisaurin duban bayin Allah dasuke ta sharhi akansu tai Murmishi, yace yadai kema kinji addu'ar da suke mana ko ,Allah Ameen.
Tace ni dai banjiba Yaya nadai tuna wani abune.
Tafada dai dai sanda zasu shiga office din Dr.Khaleel da sallama Arifullah yamurda kofar ,Dr.Khaleel Wanda daman yasan da zuwansu ya amsa masu sallama tare da Fad'in bismillah Rankayadade ,yamika masa hannu sukai musabaha kamin suka zauna ,Dr. Khaleel ya dauko file din Rabee'a yasoma budewa tare da Fad'in Hajiya meke damunki.
Rabee'a ta dubi Arifullah kamin tasoma fad'ama Dr.Khaleel komi.
Shikam tana fad'a yana rubutu har ta ga ma,Yad'ago kansa yace" bayan nan babu wata matsala?"
"Eh babu komi Dr.".
Wani guri ya danna ko minti daya ,ba ai ba sai ga Nursing tashigo cikin girma mawa ta gaidasu kamin tadubi likita tace " Sir gani "
Yadubeta yace kuje tare da Hajiya kiyi mata Allura sannan ki je phamecy ahada mata wadannan magungunan.
"OK sir."
Inji sister Rukayya,takarb'i komi kamin tadubi Rabee'a tace ranki shidade taso muje ko.
Rabee'a fa tunda taji an ambaci Allura fa idanuwanta suka soma raina fata,tadubi Arifullah yadaga mata gira alamar karfafamata gwiwa aransa yace akwai aiki akanka fa Arifullah domin Allah ya baka mace mai raki ya lumshe ido lalle wannan akwai aiki ranan haihuwa ,shikawai take kallo yanata Murmishi tadubesa tare da katsemasa tunani Yaya nafaji sauki kace tabar allurar kaji .
Tafad'a tare da wasu hawayen shagwaba.
Cike da burgewa Dr.Khaleel yadubesu yace to inafa ganin kanwar nan taka zata bamu matsala kasan yanzu tasamu dama can Baba me lallabamana ita kamin ai mata Allura.
Arifullah yanisa tare da Fad'in ok, yadubi Rabee'a cike da so yace" bakison kisamu lafiya ne Rabee'a?"
Tadubesa cike da wata irin shagwaba tace " Yaya to ai naji sauki fa .
Karon farko a Rayuwarsa na ta6a yarikemata hannu yamikar da itaba va Arifullah ba had Rabee'a sai da tai kamar zata shide saboda wani maganadisu da yake fixgarsu ga ba d'ayan su ,takasa yi mass musu har suka isa dakin Allurar cike da dabara Arifullah yasa Rabee'a a faffadan kirjinsa yana shafa mata baya a hankali ahankali,tai wani lamo da ita Rana wani sauke numfashi a hankali ,da ido yama Nurse din magana tazo tamata ,ai wata damka Rabee'a ta kaima Arifullah tana Fad'in wash!!!!!!!!.
Maman khaleel
Dinkuce✍️
NI KE DA GASKIYA
💖💖💖💖💖💖💖
Na
Rabee'art Muhammad
(Maman Khaleel)
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]
Daga Marubuciyar :
HABIBA
KISHIYAR ZAMANI
AND NOW👇