← Book details Ni Ke Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 18

Sashe 14

Ni Ke Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sunan Allah mai rahma mai jin k'ai.

Page 99

____ Wash! Yaya da zafifa,tafad'a tare da wasu hawayen shagwab'a,suka sauka akan Faffad'an kirjinsa,mulmula mata wajen yake a hankali tare da fad'in am sorry My Baby kiyi shiru anga kinji bazata sakeba kuma sai na mata hukunci indai tasake ,ya isa haka kinjiko,ya fad'a acikin kunnuwanta,har cikin ranta take jin wani sanyi yana ratsata tuno fa su ba maharraman juna ba ne yasata tasoma k'ok'arin zare jikinta daga nasa,sai taga d'akin ba kowa sai su kad'ai,tadubesa ta turo Baki tace kagani ko Yaya kasa Sister Rukayya taji kunya tabar mana words d'inko.

Yamike yaxo dab da ita yace" bake ba ce ba kinfiye rud'a mutum da wasu salonki mai sa mutum ya mance indayakeba,ya fad'ashima cikin wani salo Wanda shikad'ai ya iyasa.

Murmishi tayi kamin tace "nidai ka mayar da ni gida ,tafad'a tana tafiya tana d'an d'ingishi ".

"Wallahi ko kimike ko nad'auke ki cak nakaiki mota".

Ai tuni ta mik'e tasoma sauri ta nufi hanyar fita, Murmishi yayi kamin yace OK bajira ko nagode ,sai da yakoma Office d'in likita ya amso mata magani,kamin sukai sallama yanufo Mota,samunta yayi ta jingina kanta ajikin Motar,yace "Hello My Baby".

Muje ko ya fad'a tare da bude mata k'ofa tashiga ,shima yashiga bakinsa d'auke da Addu'a yatayar da Motar yasoma tafiya yadubeni yace" yadai haryanzu allurar batasakekibane ?"

Na bud'e manyan idanuna nasauke su a kyakkyawar fuskarsa, nad'an hararesa nace" to ya akayi kuma yanxu?".

Yace "kai !kai!!kai !!!!!
Ni kika harara dan baki sona ko nagode,ai da me mashinne da yanzu kinmasa fari ,bakomi nima Arifullah Allah kabani Me...!".

"Kai Yaya nace bana sonka ni karufamin Asiri dan Allah banaso, ai kai ma bakasona da kanasona ai da jiya bakai fushiba, katafi kabarni cikin wani haliba".

Ya k'ara gyara zama aransa yace anzo wajen ,kamin yace naga tsayawata batada amfani kinmayar da shashash,sai soyewarku kuke dan ni ba a sona.

Tawani turo baki cike da shagwab'a tace" wai Yaya banasonka ni kadaina fad'in haka ,kuma fa shid'in Malaminane fa kuma....!"

"Kuma saurayin kiko ".

Ta rufe fuskarta tana m
Murmishi tace "a dane fa, Yanzu Sam bana sansa,dan ni yanzu Maza tsoro suke bani Yaya".

Yayi saurin gangarawa gefen hanya tare da d'an zare Ido kamin yace" hadda ni ma ina baki tsoro,ya fad'a tare da dafa k'irjinsa.

Yaso bata Dariya saboda yadda yayi yasa ta k'ara narkewa a sonsa.

Ta juya masa baya kamin tace "banda kai ai kai Yayanane".

Yace OK to dubeninan Rabee'a tunda ni nasamu yabo ance bandani.

Takasa waigowa ,yasake cewa" Rabee'a kalli Idanuna dan Allah kinji".

Ta juyo a hankali sukai 4 eye's da shi wani yar take ji kamar tajawosa gareta ta rungume dan so,dan kallonsa yana tayar mata da wata tsigar jiki mai futa haicin nan ta Ma'abota So.

Yace" Rabee'a Me kikagani a cikin Idona ?".

Ta d'auke kanta daga Mayattatan kallon da yake mata dan bazata jure ba.

Yakai lallausan hannunsa kan kyakkyawar fuskarta ya juyo ta a hankali,yasakar mata wani Yalwataccen Murmish.

Ta kulle Idanta yace" kalle ni Rabee'a Kina So na!".

Ji tai kamar ta rungumesa dan farin ciki ,ai tuni tabude Idanunta tazuba cikin nasa yana Murmishi yace " ina fata kema zaki soni kamar yadda nake Son ki .

Wai yau Ita Rabee'a wannan had'add'an gay sadauki ingarma ga kudi ga ilmi da Nasaba yace yau ita yazaba amatsayin abokiyar rayuwa Allah kai ne abin godiya .

Ya soma murza mata hannu ahankali yana fad'in me kika ce Rabee'a karki ce baki So na kinji".

Tayi Dariya kamin tace na Amince amma kaje kanemi Izini wajen Baba na .

Ai bai San sanda yaja ta Jikinsa ba ya kai mata wasu mahaukatan Kiss 💋 masu zafi ,tare da fad'in nagode kwarai Rabee'a nikuma namaki Alkawarin yau ba gobeba zannemi Aurenki a wajen Baba.

Maman Khaleel

D'inkuce✍️

NI KE DA GASKIYA

💖💖💖💖💖💖💖

Na
Rabee'art Muhammad

(Maman Khaleel)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

Daga Marubuciyar:

Habiba
Kishiyar zamani
And now👇
Ni ke da gaskiya

Dasunan Allah mai rahma mai jinkai.

Page 100

Yau kam Arifullah cike yake da farin ciki yau a office aiki yake cike da walwala ,koda yakoma gida yasanar ma Mami yadda sukai da Rabee'a,Mami tayi Murna sosai da samun sirika tagari,aranta tace cab aikwai cakwakiya in Yusuf yadawo yaji zancen Auren Rabee'a da Arifullah,tayi Murmishi aranta tace Dan'uwa sai kayahakuri kabar ma danka wannan gonar domin wannan gonar tafidacewa ne da wannan da zai zuba shuka sannan musamu yabanya mai kyau.

Acikin satin nan kuwa wata Soyayya Mara misaltuwa tare da shakuwa ta banmamaki ta shiga tsakanin Rabee'a da Arifullah ,koda yaushe suna manne da waya a kunne tare da gayama juna yadda suke tsananin son junan,yanzu ma waya suke inka kalli zuciyarsu fes take babu wata matsala, sai tsananin son junan su,Arifullah yagyara zama yace" My Baby yau Daddy zasu zo nemamin Aure fa yau wajen Baba,Dan wallahi yadda nadade babu matan nan nakosa naganki a gefen damana ko ya kikace?"

Murmishi Rabee'a tayi mai sauti cike da jin nauyi tace" to Yayana Allah ya kawo su lafiya".

"Yauwa My Baby Amin yan zu me kikeyi ?".

Takara gyara kwanciyarta tare da rungume fillo a kirjinta tace " Bakomi Yaya ina kwance ne ina hutawa".

"Iye lalle ke y'ar gatace cab nikam ganinan ina neman na Abinci,aiki ya tasani agaba" .

To masha Allah ,Allah ya tai maka yasa asamu abinda akafita nema Yayana.

Harcikin ransa yaji dadin addu'ar fad'i yake" Ameen Ameen Amaryar Muhammad Arifullah".

********

Da dare kam kamar yadda Arifullah ya fad'a su Alhaji Abdullahi da kaninsa Alhaji Murtala suka zo nemawa d'ansu Auren Rabee'a,inda Baba yayi farin cikin tare da sa albarka acikin lamarin ,kamin yace wani hanzari ba guduba Alhaji inason Kuban kwana 2 muzauna naji tabakin yarinyar kasan yaran yanzu kai kakeson abinda zaifimasu alkhairi sai kaga su suna hangen wani shirmen banza,duk da nasan Rabee'a duk abinda mukaza6a mata bazata mana jayayyaba.

( hhhhhh anya kuwa Malam Kabiru ba ayoyi kaganiba kuwa kake so kabata y'ancinta nabaya ba)muje zuwa .

Alhaji Murtala yagyara zama yace haba karkadamu Malam munbaka satima mun amince Allah dai yasa rabon muce.

Baba ya amsa cikin sauri Ameen ya Allah.

Har Mota Baba yarakasu kamin yadawo gida cike da farin ciki,yasamu Mama yashaidamata yadda sukai da Iyayen Arifullah, kamin yace kiramin y'arbaban in tan bayeta,duk da nasan itama tana sonsa.

Mama kam murna take tare da godiya ga Allah mai yadda yaso a kowani lokaci ,Allah yarubuta dama can Alhaji Dalladi ba min Aurenta bane shiyasa Allah yakawo dansa cikin lamarin,sannan yakawo masu sauyi da Arifullah.

Da wannan tunanin tashiga dakin Rabee'a inda take ta hira da Masoyinta cikin nishadi Mara misaltuwa,Mama tai sallama ,Rabee'a tai saurin fadin ina zuwa ga Mama nan.

Batajira amsawarsa ba takatse kira tare da amsa sallama ,Mama tadubeta cike da so aranta tace Rabee'a Madubi sankowa,diya daya tamkar dubu.

Ta Murmusa dawa kike waya?

Rabee'a cike da jin kunya tace Mama Yaya Arifullah ne.

"To kizo inji Babanku Mama tafada tana Murmishi ,Kai yaron nan yaron kirkine Rabee'a Allah dai yasa ka masa da Alkhairi ".

Rabee'a taji dadin addu'ar Mama tace" Ameen Mama"

Baba yadubi Rabee'a cike da nutsuwa yace "Rabee'a inason in tanbayaki,shin kina son Arifullahi?".

Cike da jin kunyar maganar mahaifinta ta sunkuyar da kai kasa tana Murmishi, Baba yasake tanbayarta akaro nabiyu kamin ,tad'ago kai tadubesa tace "eh" Baba inasonsa."

Alhamdulillah ita naji Baba yana ta mai mai tawa tare da fad'in jeki a binki Allah yamaku Albarka.

Rabee'a ta mike cike da jin kunya tabar dakin .

Bayan kwana 2 kamar yadda Baba yayi Alk'awari yakira iyayen Arifullah yace yace sukawo komi na Neman Aure Yabama Muhammad Arifullah Auren Rabee'a,haka kuwa a kai ankawo komi na al'ada Wanda kowa sai zuwa yake ana kallon kaya kamar wani Dan karamin shago domin komi caton ne goro kam huhu 5 ne kai komi fa masha Allah, antsaida rana nan da wata 2masu zuwa.

Sai dai muyi fatan Allah ya nuna mana Ameen.

******

A bangaren Malam Hussain kam tunda yakoma gida yara sa sukuni yasan dole yakara rasa Rabee'a a karo na 2 yazama dole yakoyi hakurin rashin ta ,dan zayyi wuya takuma sauraransa ,wannan yasa yacireta arai yakuma yimata fatan Alkhairi,ko Amakaranta da suka hadu bai nunamata komiba,itama ba ta nuna masa komiba sundai gaisa daga nan kowa ya kama gabansa dayake suna shirin yin sauka ,Rabee'a ta dage sosai sai faman hadda take inda akabata tsakiyar suratul ma'ida shafin kusa da na karshe,yau sun taru a filin makaranta ana gwaji ,haka kowa yafito yana ta karatu har a kaxo kan Rabee'a Kabir,inda tafito tasoma rerawa cikin muryar ta me taushi da dadin sauraro ,Malam Hussain sai wani lumshe ido yake yana jin duk Wanda ya samu Rabee'a yamorewa Rayuwarsa domin ta hada komi.

Gashi anbata abubuwa da yawa Wanda zatai ranan sauka ,dan duk wani abu da yajibanci abunwasu karatu to Rabee'a fa tana ciki.

Ranan sauka karfe bakwai sunhallara a filin sauka, Malam Mustapha da sauran malamai suna ta shirya guri kowa ya zauna Rabee'a tasoma bude wajen da Addu'a cikin muryarta mai dadi kowa ya natsu yana saurare har ta kammala kowa ya shafa kamin takoma gurin zamanta ta zauna nan fa waje yadau kabbarar Allahu akbar.

Mami kam duk nakega a gun kamar tafi kowa farinciki domin duk kiran da za ai ma Rabee'a zai taje tasa mata kudi haka ma Oga uban gayya wato Arifullah jinsa yake kaf duniya babu wanda yafishi dacen Macen kwarai kuma Hafiza sun yi b'arin kud'i sosai ,inda abin yazama gwanin sha'awa Malam Hussain kam ko ba a fad'a masa ba wannan shine me motan da suka had'u agidansu Rabee'a wanda take ikrarin shine za6inta,ya nisa aransa yace gaskiya kuma sundace ,yafada tare da kawar da kansa gefe dan yasan Rabee'a tayi masa nisa sai dai fatan Alkhairi.

Misalin karfe 2:00pm dai dai akatashi daga wajen sauka akanufi gida ,inda na hango Rabee'a ta hade cikin wata shadda mai ruwan pouder wadda akai mata aiki da milk din zare doguwace harkasa tai daurin dankwalinta nazamani duk da bataima fuskarta wata kwalliya ba amma tayi kyau ainun,kowa yana yaba kyawu irin na Rabee'a.
Chapter 14 · 0% Book details