← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 8 OF 51

Sashe 8

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Afalon momcy ya tarar dashi, ya rissina ya gaishesu, suka amsa, papa ya ce, "Modeebbo miye matsayina a wajenka?.
Cikin matuk'ar mamaki Nawaf yad'ago yana kallon mahaifan nasa, ya daure ya ce, "papa kai mahaifinane, wanda banida kamarsa aduk fad'in duniya.
Papa ya jin jina kai, tareda cewa masha ALLAH, to modeebbo amatsayina na mahaifinka na zartar da umarni akanka yanzunnan, nan papa ya labratawa Nawaf duk abinda ya faru.
Atsorace Nawaf yake kallon papa yayinda zufa keta ambaliya adukkan sassan jikinsa, ya daure cikin rawar murya ya ce, "papa aurefa kace??.
Papa ya ce, "kwarai aure nace modeebbo, kuma ina fata amatsayina na mahaifinka zaka yimini biyaya, zaka kuma karb'i k'yautar da ubangiji yay maka da hannu biyu, natsuwarka nake buk'ata da farin cikinka, bana son wannan lamarin yatab'a rayuwarka bare kasamu matsala akan abinda kazoyi Najeria.
Nandai sukaita lallashinsa, dayi masa wa'azi mai shiga jiki.
Jiki a sanyaye Nawaf ya tashi yanufi d'akinsa, koda yashiga d'aki saiya zube afalo yana zabga zufa yadafe kai yana jujjuyashi, gsky yabani tausayi matuk'a.
Ahaka mas'ud yazo yasameshi, arikice yake tambayarsa lafiaya, amma Nawaf yakasa magana, da hannu yaymasa nuni daya basa ruwa, ruwa mas'ud yabashi, tunda yakafa kai saida ya shanyeshi tas.
Mas'ud dai kallonsa yakeyi cikin matuk'ar mamaki, saida suka d'uki tsawon minti goma ahaka, sannan Nawaf ya daure yabama mas'ud labarin abinda yafaru, mas'ud yay murmushi cikin tsokana ya ce, "haba mutumina kace kai yau angone, shiyyasa naji kana k'amshin angwanci.
Harara Nawaff ya watsa masa tareda jan k'aramin tsaki.
Mas'ud yay dariya ya ce, "ALLAH yasanya alkairi bro's, amma ka kwantar da hankalinka iyayenmu bazasuyi abinda zai cutar damuba, nima bari nazo nafara neman aure kafin ayi sadaka dani!, tunda anfara ta kanka.
Duka Nawaf yakaima mas'ud, mas'ud ya kauce yana dariya.
Nan yayta tsokanarsa har Nawaf yad'an saki jikinsa.

AMARYA YASMEEN
zuwa yanzu labari yaje kunnan yasmeen, tayi farin ciki da faruwar hakan, saidai tana fargaba kuma da sabon mijin nata wanda batasan koshi waye ba, wannan dalilinne yasakata kuka, wai ba'a rabu da bukarba an haifi habu, karin maganar ta hausawa.
Umma da abba sunata lallashinta da mata nasiha.
Amma gaba d'aya jikinta ya d'ume da zazzab'i mai zafi, dan danan tafar rawar sanyi, har hak'oranta suna had'uwa waje d'aya.
Asibiti aka tafi da'ita cikin hanzari.

FAISAL.
A gidansu faisal kuwa tunda labari yaje kunnan hajiya jummai ta yanke jiki tafad'i, saida aka yayyafa mata ruwa ta kawo numfashi, da kuka ta farka, lallai d'anta yayi ganganci, ya kumayi asara wadda tanada tabbacin bazai samu madadintaba.
Sukansu danginta dana Alhaji buba sai masifa sukeyi, suna fad'in aii laifinsune dan sune suka sangarta faisal d'in, shiyyasa baya ganin kowa da daraja a cikin family d'in.
Faisal kam ko ajikinsa, dan aganinsa hakan shine dai2, amma daga lokacin daya ci karo da sak'on wata takarda sai komai ya canja, ya daddage ya tsala ihu yana kiran yashiga uku!!.
Dafarko babu wanda ya kulashi, amma da akaga ihun nasa bana k'arewa bane sai aka fara kawo masa agaji, wani k'anin Alhaji buba ne yad'auki takardar yana karantawa, shikansa arazane yake duba takardar.
Dangi suka shiga tambayar lafiya??.
Ya ce, "inafa lafiya, lallai faisal kayima kanka, maganin mutumin dabaya bincike bare ganin girman manya a harkokinsa, kuma ka d'auka abinda ka shuka shine kake girba.
Sakina k'anwar hajiya jummai ta kwace takardar tafara karan tawa kowa yanaji.

Assalamu alaika babban yaro!!
lallai kacika dak'ik'i mara tunani, kodayake ALLAH ne ya kwaci yarinyar kirki daga hannun fasik'i, wanda bai d'auki sab'on ALLAH komaiba.
Na taya yasmeen murnar barin hannunka.
Faisal ban rama kashi goma daga cikin abinda ka aikata minba, 😭kaine kayi sanadin lalacewar 'yar uwata, ka lalata mata rayuwa ka koya mata fasik'anci, ALLAH ya isa tsakanina dakai faisal.
Kuma yasmeen ba karuwa bace, ita tsarkakrkiyace, kamilar mace, dama kun tursasatane itada mahaifanta akan ta aureka.
To yanzu ALLAH ya bata miji nagari, mai k'yawawan halaye, d'an babban gida.
Amma naso ace nine na auri yasmeen, kodan zuciyarka tabuga, sakari shasha.
Sako daga abokinka mai sonka da k'aunarka
HISHAM AHMAD KT! !!!!!!!!!!!.
Talek'o ta koma😆😆😜😜.

Gaba d'aya dangi suka d'auki sallalami, tareda ALLAH wadai da halin faisal.
Wasuma ALLAH yakara suke cewa.
Faisal kam sulalewa yayi a k'asa saboda bak'in ciki, dahanzari suka yayeshi zuwa asibiti.................✍🏻

Lallaikam yau anayin rikita2 a Najeria😜

💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞LUV U OLL MY FAN's💞

©2016
[1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆

NA BILKISA IBRAHIM💞

Page👉🏻15

....A asibiti kam al'amura sun dai2ta a b'angaren yasmeen, ansaka mata k'arin ruwa tanata barcinta.
Sai yamma lik'is ta farka, dak'ar tasha tee aka bata magunguna, takai dubanta ga Abba dake tsaye jingine da bango, saitaga har yad'an rame, ya ce, "mamana sannu kinji!.
Kai ta d'aga tana hawaye, umma tashiga sharemata hawayen tana rarrashi, yaseer yazo yazauna kusada ita, shikanshi duk yayi wani iri, cikin sanyin murya ya ce, "kiyi hak'uri aunty kibar kuka, na tabbata hakan alkairine agaremu, tunda ALLAH ya ku'btar dake daga hannun wannan d'an iskan!.
Yasmeen ta share hawaye, ta ce, "yaseer gskyarka, na! kub'ta daga hannun faisal, saidai bansan hannun wa? kuma na fad'aba, ta'kare maganar cikin kuka mai tsuma zuciya.
Abba yakaraso ya zauna d'ayan gefenta, hannunta yakamo yarik'e, yay d'an murmushin dauriya, karki damu mamana insha ALLAHU mijinki na yanzu mutumin kirkine, kuma nasan zakiyi alfahari dashi watarana.
Duk da nima banganshiba, amma yanayin mahaifinsa da kamalarsa yanuna d'an nasama mutumin kirkine, kiyiwa mijinki 'kya'ky'kyawan zato kinji!!.
Yasmeen tad'aga kai tana share hawaye, ahaka likita yashigo ya samesu, ya k'ara duba jikinta, yaga komai normal, babu 'bata lokaci ya sallameta, suka tattara suka nufi guda.
Wannan kenan.

A'bangaren Nawaf kuwa yana cikin damuwa shima, shikam dayasan abinda zai tarar kenan a Najeria dabazaiyi fatan zuwaba, yafitar da huci mai zafin gaske daga bakinsa tareda cije le'bensa na kasa.
Talatu taiyi sallam a 'kofar d'aki, banza yay mata bai amsaba bare yabata ixinin shigowa, takai minti biyar atsaye, jin ba'a amsataba yasa tadannakai cikin d'akin atunaninta baya nan.
Saida gabanta yafad'i yayin datayi tozali dashi azaune, jikinta yana 'bari ta ajiye abinda takawo masa, ta rissina tana gaisheshi!.
Maimakon ya amsa mata saiyaja tsaki tareda watsa mata harara, dasauri tatashi tafito tana rawar jiki.
Kafa yasa ya ture kular, ALLAH yasama abincin bai zubeba, wayarsa tafara neman agaji, kallo d'aya yaymata ya d'auke kai, takatse aka sake kira, nanma yay burus, shikuwa maikiran sarkin naci saiya cigaba da kira.
A'kufule Nawaf yad'auki wayar , amma yayi shiru ya'kiyin magana.
Daga can akace modeebbo wai sai yaushe zaka shigo?, karka manta munyi dakai! zakataho yau da 'karfe 4, amma gashi har 5 tayi.
Nawaf yaja siririn tsaki, ya ce, "saika bari kaga gari ya waye banzoba sannan kayimin 'korafi.
Daga can akace to shikenan, amma yakamata kayi 'ko'kari kasandai kanada matu'kar muhimmanci a wasannan!!.
Banza Nawaf yay masa, saima ya kashe wayar gabad'aya, yana bala'i, kabi ka isheni da surutun tsiya, bakusan abinda yadamu mutumba zaka wani dameni da kira, ku damuwarku kawai kuka sani, yaja tsaki tareda kwanciya ya lumshe idanu.
Ahaka mas'ud yashigo ya sameshi, yad'an girgiza kai ta reda ta'ba Nawaf.
Ahankali ya bud'e idanu yana kallon mas'ud.
Mas'ud ya ce, "haba bro's yanaga baka shiryaba ne, kasanfa ka makara ma.
Nawaf ya yatsine fuska yana yima mas'ud kallon gefe, har ya bud'e baki zaiyi magana saikuma yayi shiru.
Azuciyar mas'ud ya ce, "yau kuma miskilancin ya motsa kenan?, ganin Nawaf ba amsa zai bashiba yasa yanufi bedroom d'insa, kaya ya had'àma Nawaf tsaf sannan ya fito.
Kan hannun kujerar da Nawaf yake kwance yazauna, cikin sigar lallashi ya ce, "kayi ha'kuri my bro's, ka d'auki hakan amtsayi 'kaddararka, kasan kanada matu'kar muhimmanci a wajen wasannan.
Inaso kacire duk wata damuwa ka ajiyeta gefe, ka kar'bi 'kautar da ALLAH yabaka, aure alkairine, kuma nasan wataran zakayi alfahari dashi, idan papa yaga kana cikin damuwa zai d'auka bakabi umarninsaba, ka daure ka kauda komai kaji!!.
Nawaf ya d'ago manyan idanunsa dasukayi jajir ya ce, "mas'ud ina cikin damuwa wlhy, karka manta aurefa papa ya d'auramini batareda nasan yarinyarba, bansan halintaba batasan nawaba, bata sanniba.
yo wai tayayama zamu kasance amatsayin ma aurata?, kokad'an banida niyyar yin aure yanzu kaima kasani, amma papa ya kama 'ka'kaba mini, wlhy idan zaka kasheni bansan yanda zan zauna da macebama ni!!.
Murmushi mas'ud yayi, kaga d'an uwa kwantar da hankalinka, indai yanda zaka zauna da itane damuwarka to zan koya maka, yafad'a cikin tsokana.
Harara Nawaf yasakar masa, aii kaga matsalarka kai bakomai kake d'uka serious ba.
Mas'ud yay dariya kaiwai batareda ya ce, "komaiba.
Nawaf ya mi'ke yanufi bedroom d'insa, bayi ya shiga yasakarma kansa tsawa🚿, (nakula indai yana cikin damuwa yanaso yasakarma kansa ruwa🚿, komiye sirrin hakan??. ) yakai tsawon minti goma ahaka, daga baya yay wankan sosai yafito.
Yaudai ba'ayi wani gayuba sosai, danko sumarsa mai gyaraba yafito, amma yayi 'kyau ba laifi.
Mas'ud dake zaune yana cin abinci ya ce, "yauwa kokaifa, yanzu sauranka abinci, kaci saimu wuce.
Yatsine fuska yayi tamkar wata mace, ya ce, "babu wani abinci dazanci malam, dan konaci bazaiyi amfani ajikina ba.
Mas'ud ya ce, dadai kadaure kaci.
Hanyar waje yanufa yana fad'in kasameni a wajensu momcy.
Mas'ud yay murmushi, wataran yakan rasa Nawaf wane irin mutumne?, yasan duk duniya babu wanda yakaisa sanin halin Nawaf bayan iya yensa, amma shi kansa wata sa'in lamarinsa yana d'aure masa kai, mutimne miskili, masifaffe, saidai bayason yawan hayaniya, ba kowa yake ganin dariyarsaba, bakuma harkar kowa yake shigaba, wannan yasa wasu suke masa kallon mutum mai wula'kanci kuma ba haka bane.
Saika zauna dashi zakaga yanada su'kin kai da son mutane.
Chapter 8 · 0% Book details