← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 23 OF 51

Sashe 23

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 3 min read

.....koda yasmeen tafita zamanta tayi a waje, tanajin motsin fitowar Nawaf ta samu wani lungu ta 6uya, 6angaren momcy yanufa tasan zaije gaishesune, ďaki takoma ta ďakko hijjab itama, tana shirin shiga yana fitowa, tamatsa masa ya wuce batareda kowa ya kalli ďan uwansaba, yasmeen ta ta6e baki tareda shigewa.
Shima mota yashiga ya bar gidan.
Yasmeen zamanta tayi a 6angaren momcy har azuhur, sanan tadawo nasu 6angaren, har sanan Nawaf bai dawoba, tayi sallah ta sake wanka, falo tadawo ta zauna zuciyarta cike da tunani, yau kwana uku ke nan kullum sai faisal ya kirata, amma bata ďagawa, gsky tana fargabar Nawaf yagani, da sauri ta ďago domin jin sallamar ameena..
Taje ta rungumeta cikin tsananin farin ciki, Ameena ta ce, "kai yasmeen irin wannan 'kyawu haka, miye sirrin??.
Yasmeen ta ajiye kayan hannunta tana hararar Ameena, 'yar duniya abinma harda zagi, aii kobaki faďaba kowa yaganki yasan kina jin daďi, kodai oga mas'ud yayi ajiyane??.
Dariya Ameena tayi tareda shan lemon da yasmeen ta kawo mata, ta ce, "kin rama kenan??.
Dariya sukayi suduka.
Yasmeen ta ce, " 'yar uwa inatason shigowa wajenki amma ina tsoron na tambaya a hanani, ya amarci??.
Ameena tayi far da idanu ta ce, "amarci muna ci kam, kamar yanda nasan kuma kuna shan naku.
Yasmeen tayi murmushin takaici, ta ce, "k ni babu wani amarcin dana keci saima shan wahala, amma ba wannan bane mafi girman damuwata amina!.
Ameena ta gyara zama, yasmeen miye damuwarki???, humm amina faisal ne damuwata.
Ameena ta 6ata fuska tana hararar yasmeen, "k yasmeen kiji tsoron ALLAH wai da baki so faisal ba sai yanzu dakike agidan mijinki, karfa ki manta mijinki yafi faisal komai wlhy 'kyau aji ilimi wayewa, dan iskanci da shaye2 bashi bane wayewa.
Yasmeen ta kamo hannun Ameena ta matse anata, Ameena ki saurareni nakai 'karahen zancena mana, kema kinsan bazan ta6a son faisal ba arayuwata, baki bari nafaďi abinda ke raina bane.
Abinda yasa kikaji na ce, "miki faisal ne damuwata shine, yau tsawon kwana uku kenan kulum sai faisal ya kirani, gashi yay ta turomin sakwanni, shiyyasa ma kwana biyu na daina chatting kwata2.
Ameena ina tsoron mugun nan ya gane, na tabbata bazai ta6a fahimtata ba.
Ameena ta ce, "tofa, ba ance tun randa faisal yazo gidanku da safennanba washe gari yabar 'kasar??, nimadai haka naji, amma fa number dayake kirana da ita ta 9ja ce.
Ameena taja numfashi, ta buďe baki da nufin yin magana.......sai Nawaf da mas'ud sukai sallama, dole suka katse hirar tasu.
Su Nawaf suka zauna, mas'ud ya ce, "tunda ku kun'ki zuwa mu gashi yau munzo mu kwashe ladan.
Yasmeen da Nawaf sukayi dariya, yasmeen ta ce, "ayi ha'kuri muma zamuzo, Nawaf ya ce, "kinga ishirunki, ranar aii saida naje gidan, shiko tunda aka gama biki bai zoba, saboda santin amarci, ranar har momcy daida ta tambayeshi.
Mas'ud ya zaro ido kai da gsk kakeyi.
Nawaf yay dariya yana faďin eh mana.
Nandai sukaita hirarsu, har la'asar, mas'ud ya ce, "Ameena ta tashi su tafi, dole tabi umarnin mijinta, amma badan tasoba, dan tanaso su 'kare maganar da suka fara da yasmeen.
To itama yasmeen ďin taso hakan amma bayanda zatayi.
Har get ta rakasu sanan ta dawo dan harda Nawaf suka fita, tunda lokacin sallah yayi.
Chapter 23 · 0% Book details