← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 28 OF 51

Sashe 28

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

......Tunda suka dawo basa shiga harkar juna, sun koma zaman doya da manja, gaisuwa ce kawai ke shiga tsakaninsu, saikuwa girki da yasmeen zatayi, yazo shikuma babu kunya yaci. Abin yana bama yasmeen mamaki, idan ta tuna abinda Nawaf yarin'ka yimata a safana, takai dubanta ga 'katon hoton Nawaf dake falon, yana sanye cikin jan jc yayi 'kyau sosai, afili ta ce, "mutun 'kya'ky'kyawa a waje, amma azuciyarsa yafi maciji mugunta, ta gallama hoton harara. Nikam danake gefe na tuntsure da dariya, dan tabani dariye, kome hoto yay mata??. ☆ ☆ ☆ ☆ Ayaune kuma hajja zata lula saudia, fuskar kowa ka kalla a gidan babu walwala, amma babu yanda zasuyi, haka sukai gayya suka rakata airport Anwar sai kuka yake wai saiya bita, papa ya ce, "yabari ayi hutu saiya tafi, hakadai suka dawo gida kowa yana zum6ura baki. Yasmeen ma dabata daďe da sanintaba saida taji babu daďi, dan hajja tsohuwace mai shiga rai, ga kirki da son mutane, lallai anan momcy ta kwaso 'kyawawan halaye, to saimuce hajja ALLAH ya kiyaye hanya. Tunda suka dawo daga 'kauye yasmeen batada cikakkiyar lafiya tana 6oyewane kawai, amma yau dole ta kwanta, shi oga Nawaf ma bai saniba, dan yanata hidimar komawarsa Spain. Saida momcy taga har la'asar yasmeen bata shigo wajensu ba sannan, tafara tunanin ko lafiya, ta mi'ke ta nufi 6angarensu, babu kowa a falon saidai an gyarashi tsaf yanata 'kamshi, kai tsaye bedroom tawuce, da sauri ta 'karasa bakin gadon domin ganin yasmeen a 'kudundune cikin bargo. Momcy ta zauna agefen gadon taďan ďaga bargon tana faďin ďiyata kina lafiya kuwa?....ta 'karashe maganar a ahankali, danjin zafin zazza6i a jikin yasmeen. Dan danan momcy ta ruďe tashiga tambayar yasmeen tun yaushene batada lafiya?, yasmeen ta buďe ido da 'kyar, ta ce, "momy tunda daddarene. Cikin damuwa momy ta ce, "amma shine baki faďaba?, ina modebbo??. Yasmeen ta ce, "yafita tunda safe. A'a, baisan bakida lafiyaba ne??, yasmeen ta daga kai alamar eh. Waya momcy ta ďauka takira Nawaf, modebbo kana inane??, Nawaf ya ce, "ganinan zuwa gida ma. To saika iso momcy tafaďa. Abinci mai sau'ki momcy tasaka su talatu su dafoma yasmeen, ta taimaka mata tayi brosh da wanka dantaji daďin jikinta, tana fitowa Nawaf yana shigowa, tayi tsaye kamar gunki shima tsayen yake yana 'kare mata kallo, dan sukaďaine a ďakin, momcy tana falo. Da sauri yasmeen taja hijjabin sallarta ta kudundune aciki, baki Nawaf ya ta6e yana wani yatsine fuska. Itakuma tawuce ta zauna bakin gado, momcy tashigo da sallam tareda talatu. Sai asannan Nawaf yazauna akan kujera, momcy ma ta zauna talatu kuma ta ajiye abinda takawo ta fice, momcy ta ce, "ďiyata saboda mi baki gayama mijinki bakida lafiyaba?, dan ya ce, "mini shima bai saniba. Saida yasmeen ta kalli Nawaf sannan ta ce, "banaso hankalinsa ya tashine. A'a wanan ba hujja bace, yaza ayi ki zauna da ciwo saboda kar hankalin mijinki yatashi, daga yau karki sake kinji ko?, yasmeen ta ce, "to momy insha ALLAHU baza'a sakeba. Nawaf ya ce, "momcy bari na kira mas'ud yadubata, dan naga bai fitaba. To, yakamata kuwa. Momcy dakanta ta bata abincin taci, sai yatsine fuska takeyi, ahaka su Nawaf suka shigo suka isketa, mas'ud yay mata sannu, tana gama cin abinci ta tashi da gudu ta nufi bayi, amai ta ringa zazzagawa kamar hanjin cikinta zasu fita, momcy tabiyo bayanta dasauri, ta taimaka mata hartagama tagyaramata jikinta, sanan suka dawo ďaki. Su Nawaf suka shiga yimata sannu, ahankali take amsawa, tahau gadon ta kwanta, momcy ta ce, "mas'ud ai inagama wanan ciwon na yasmeen baya bu'katar gwaji. Mas'ud ya ce, "momcy saboda mi??, momcy tayi murmushi tana shafa kan yasmeen ahankali, ta ce, "mas'ud inaga lokaci yayi dazamuga yara suna tsalle2 agidan nan. Nawaf da mas'ud suka kalli juna cikin zaro idanu. Mas'ud yadaure ya ce, "dukda haka dai momcy barina dubata, saimuga maganin daya dace abata. Momcy ta ce, "to zoka dubata, ta tashi takoma kusada Nawaf daya shiga cikin waswasi da faďuwar gaba, momcy tadafa shi ya ďago da sauri yana kallonta, saikuma yamaida da kai 'kasa da sauri, momcy tayi dariya tana faďin modebbo yaukuma kunyata akeji??, ai wanan abin farincikine. Nawaf ya daure ya ce, "momcy bafa ciki garetaba, ciwone kaiwai nake gani. Mas'ud ya katse musu hanzari da faďin bari naje nayi text daga nan asamo mata maganin daya dace. Nawaf ya mi'ke yana faďin muje tare, momcy tabisu da kallo tana murmushi. Suna fita mas'ud ya tuntsure da dariyar mugunta, Nawaf yabishi da kallon mamaki, kai wai lafiya?, ko ciwon haukane yasameka yanzunnan?. Cikin dariya mas'ud ya ce, "mutumina aikaine lamarin naka yay kama da abin dariya, wai yaushe akaje wajenne??, har saka mako yafito?. Nawaf ya yatsine fuska yana faďin ban ganeba?. Mas'ud ya haďiye dariyarsa, ya dafa kafaďar Nawaf yana faďin abinda nake nufi ai afili yake malam. Nawaf ya ta6e baki, kai nifa abinda kuke zargi daga kai har mom ba haka bane, babu wani ciki da yarinyarnan take dashi. Mas'ud ya ce, "ban ganeba kai kana nufin yasmeen batada ciki, harara Nawaf ya sakarma mas'ud, to ana shan cikin aruwane dazakace wani baka ganeba, kainifa wlhy babu abinda yashiga tsakanina da yarinyarnan. Taf ďijan inji mata, mas'ud yafaďa, to malam momcyfa jika suke so, dan nakula tana cikin farin ciki, amma gsky wannan ba dabara bace, idan kai zaka iya jurewa ai ita kana shiga ha'k'kinta ko??. Tsaki Nawaf yayi, yana faďin matsalarta ce, nibabu wani ha'k'kinta dake kaina malam kaji. Dariya mas'ud yayi, humm Nawaf kenan, akwai lokacin dazai zo, kazo neman shawarar hakan agurina, kuma wlhy tanada ha'k'ki a wajenka, kaima kasani sairai, saidai katake sanin,. Hhhhhh ashe shekarun dayawa kuwa, Nawaf yafaďa. Dahakadai suka 'karasa asibitin, bayan sunyi duk abinda yadace suka dawo gida da magunguna, amma dai text yanuna ba ciki bane. Koda suka gayama momcy saitace, babu komai shima cikin yana zuwa insha ALLAHU. tunda yasmeen tasha magani take barci, bata farkaba sai cikin dare, tajuya taga Nawaf agefenta kwance yana kwasar barci, ta lumshe ido ahankali ta sake buďewa, sakkowa tayi tashiga bayi tayi wanka dan jikinta duk ciwo yakeyi. Jin motsin ruwa yasa Nawaf farkawa shima, ya laluba gefensa saiyaji babu yasmeen yatashi yanufi bathroom ďin, ahankali ya tura 'kofar saiyaji ta a buďe, yako tura kai cikin bayin batareda neman iziniba. Dasauri yasmeen tajuyo danjin motsi, ta kwalla 'kara dan ganin Nawaf tsaye yana kallonta, ta rarumi tawul ta 'kudundune jikinta. Da sauri Nawaf ya'karaso gabanta yana faďin "k dallah karki taramin mutane. Da'karfi ta ce, "to kafita mana, miye haka zaka wani shigo mini ina wanka. Tsaki Nawaf yayi ya ce, "ubammi zan kalla ajikinki, aikin banza kawai, yafaďa yana ficewa. Yasmeen tazauna jagwaf tana maida numfashi da'kyar, ta runtse idanu gam tana hawaye. A6angaren Nawaf madai hakan take, jagwaf yafaďa saman gadon yana fitar da huci mai zafin gaske. Yasmeen tadaďe bata fitoba, saida ta daidaici Nawaf yayi barci sannan tafito, ta saka riga mai ďan kauri ta kwanta saman kujera. Nawaf yana kallonta, yaja Numfashi ahankali, gsky shikam yana bu'katar matarsa, amma yarasa hanyar dazaibi yacika burinsa, dawanan tunanin barci yakwasheshi ___________________________________ haka rayuwa taci gaba da gudu da sauri, Nawaf yanata shirin komawa Spain. Yauma yana wajen papa suna tattaunawa, papa ya ce, "yanzu idan katafi sai yaushe??. Nawaf yay 'kasa da kai yana faďin papa da'an gama kakar wasanni insha ALLAHU zamuzo hutu. To shikenan, ammafa idan kadawo da matarka zaka koma, dan bai daceba ace kana can matarka tana nanba, tunda kana daďewa baka 'kasar. Kan Nawaf a'kasa ya ce, "to shikenan papa, ALLAH yakaimu lokacin. Papa ya ce, "amin. Daganan Momcy tashigo itama suka cigaba da tattaunawa, sun daďe suna hira saida papa ya ce, "yatashi yaje wajen matarsa, Nawaf yami'ke badan yasoba yatafi. A falo ya isketa tana waya da umma tana hawaye, ya zauna kujerar dake kallonta jiki a sanyaye, itako bama tasan ya shigoba, tacigaba da wayarta, umma wlhy iya gsky ta nake gaya miki, nikam nagaji wlhy. Tai shiru zuwa wani lokaci, tasaka hannu tana share hawaye, ta ce, "to shikenan umma nagode sosai, to ALLAH yakaimu. Sai asanan takula da Nawaf, ta kauda kai daga kallonsa. Nawaf ya ce, "k dawa kikeyin waya?, kuma wayace ki ďaukarmin wayata kiyi kira?. Banza tayi masa kamar batajiba, tamaida kanta tsakanin cinyoyinta tana kuka, haushi ya tokare ma'koshin Nawaf, jiyake kamar ya doketa agurin, dan bayason kuka musamman kukan mace, yami'ke cikin haushin rashin amsa masa maganarsa datayi, kujerar datake zaune yadawo, yasa hannu yaďago fuskarta. "K!!! Wai wane irin iskancine zaki zauna kinama mutane kuka, kamar wadda akaima wani abu, kuma kinaji ina tambayarki amma kikayimini banza. Cikin rawar murya ta ce, "tomi kakeso nace maka?, aidai kasan babu wanda zankira a wayarka sai 'yan gidanmu ko, kuma aiga wayarnan kaďauka kakira number dana kira saikaji waye??. Kuma wayarka dake faďin wayace na ďauka, kai wayace ka fasa mini tawa wayar??. Nawaf ya zazzaro idanu yana faďin "k!! Wlhy ki kiyayeni, kar 'kuruciyar ki tajaki ki ďakko mini zancen wani 'kato anan, dan wlhy zan iya zaneki!!!. Yasmeen ta tsorata da Nawaf sosai, amma bataso ta nuna masa tana jin tsoronsa, dan zai samu lagontane. Itama ta zazzaro nata idanun, ta ce, "aikai kajika, sai ba'kin kishin tsiya, wlhy kayi wasa sai zuciyarka ta tarwatse abanza, nikam an cuceni wlhy da aka haďani aure da kai, shiyyasa bazan ta6a sonkaba kuwa har......... Kafin ta rufe baki ya matse bakinta da 'karfi, yasa ďayan hannunsa ya matse gashinta, ya ce, "k!! karki ďauka kishi nake akanki, karki ďauka nima zan soki, dana soki gara naso dijangala, domin koba komai 'yar uwatace, inada waďanda suka fiki komai dayawa yarinya, ki kalli ummu habiba, yarinya 'kya'ky'yawa jinin larabawa, mai ilimin addini dana boko, akwai irinsu dayawa dasukeson na kasance mijinsu, tundaga turawa har ba'ka'ken fata, dan haka ki daina ďaukar kanki "k wata tsiyace awajena. Ya fisga gashin sanan ya hankaďata ta bigi kujera, yabuga yatsun hannunsa biyu yana faďin "k ba komai bace, face 'yar aiki, mai jiran tsammani, ki ďauka darajar iyayenace tasa nake zaune dake, kuma ina ganin mutuncin iyayenki, domin muta nen kirkine, amma daba hakaba hummmmm ya 'karashe zancen acikinsa. Yasaki bakinta yashige bedroom, sai asannan tasamu damar yin kuka, takoyi kuka mai
Chapter 28 · 0% Book details