← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 25 OF 51

Sashe 25

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 6 min read

Kuyi ha'kuri yau babu yawa, ina busy ne.

©2016

💞bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞luv u oll my fan's😘 💞
[1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆

NA BILKISA IBRAHIM💞

Page👉🏻33 & 34

.....Gidan babbaban gidane, wanda za'a iya kira family house, saidai 6angare2 ne, wannan yasa yasmeen tagaza tattance adadin yawan muta nan gidan, dan danan aka cika musu gaba da nau'in kwanikan fura kala2.
Gaishe2 aka fara da tambayar juna bayan rabuwa, amma sukan haďa da fulatanci, wanda Nawaf shima yana yarawa, lamarin yabama yasmeen mamaki, bata ta6a tunanin yanajin fulatanciba.
Nawaf ya ce, "wai inasu baffa??, 'yar tsohuwa mai ran 'karfe ta ce, "suna gona, wasu kuma suna kasuwa.
Ayya ALLAH yadawo mana dasu lafiya, amin saura suka faďa, bayan wani ďan lokaci kowa yafita yabarsu dansu ďan sha furar kafin a kammala abinci.
Ita dai yasmeen bin kowa take da kallo, dan bata sansuba, tagadai wasu awajen bikinta, wasu kuma bata gane suba.
Nawaf ya juyo yana kallonta, ya ce, "wannan ita ce, hajiya iya kakarmu kenan, kowa ya mutu yabarta, ya'karashe maganar da tsokana.
Hajiya iya tayi masa da'kuwa, Nawafa kaci gidanku, kenan sokake na mutu.
Nawaf da yasmeen suka tuntsure da dariya, cikin dariya ya ce, "nikam ba sunan Nawafa ba, shiyyasa saboda ke bana son zuwa garin nan.
Aii dama ba zuwa kakeyiba, sa'idune kawai da umma (momcy)suke zuwa, saisu Abdu, amma kai basai ka haďa shekara biyu bamu gankaba.
Nawaf ya tsaya da dariya ya ce, "bahaka bane hajiya iya, niďin nan dakike gani nafi kowa son garinnan, kawaidai yanayin sana'a tace haka, amma kiyi ha 'kuri tunda yanzu nayi amarya zan runga zuwa ganin uwargida sosai.
Yakamata kam, dan babu abinda yafi zumunci daďi, shiyyasa nakeson sa'idu fiye da kowa acikin 'ya'yan gidanan, tafaďa tana bubbuďe kwanukan da matan gidan suka tara, ko ina furace da tasha damu da nono mai 'kyau, hajiya iya ta ri'ke baki, to su waďanan ina suke nufin zakukai wanan uwar hura haka sakace masu cikin zani.
Nawaf ya ce, "karki damu duk zamu iya shanyewa kinsanni da son fura.
Tami'ke da 'yar sandarta tana faďin to saiku bada himma, kishiya kisha dayawa ďanyar fata bata fashewa.
A'a hajiya iya, sokike cikin matata ya fashe, nazama naki ke kaďai.
Hajiya iya tafita tana faďin ďan nema mizanyi da ďan ta maula.
Bayan fitarta yasmeen ta ce, wai kana nufin wannan itace ta haifi papa?.
Nawaf ya girgiza kai, wanan kishiyar kakarmu ce, duk yawan matan nan dakike gani daga matan 'ya'yanta sai na jikokinta, kakarmu papa kawai ta haifa, ALLAH yay mata rasuwa tuni itada kakanmu.
ALLAH sarki yasmeen tafaďa, ALLAH yagafarta musu sukuma.
A la66ansa ya amsa da ameen.
Yami'ke yana faďin bari naje nayi sallah lokaci yayi.
Yafice yasmeen tana binsa da kallo.
Bayan dawowarsa sukaci abinci, zuwa sanan mazan gidan sun fara dawowa, kowa yagansu saiyayi farin ciki da zuwansu, dan sunsan yau sun warke.
Zuwa dare Nawaf ya dam'kawa kowa tsarabarsa, sai murna da godiya sukeyi, har makwafta suma an kakkai musu.
Nawaf yana 'kofar gida cikin danginsa anata hira da wasa da dariya, dan kokaďan baya 'kyamarsu, yanason danginsa sosai, ya kira musu papa a waya sukasha hira, sai wajen karfe tara suka shigo kowa yanufi ďakin matarsa.
Yasmeen ma harta fara barci a ďakin hajiya iya, Nawaf yashigo da sallama hajiya iya dake gyangyaďi ta buďe ido, Nawafa ina kashiga kabar yarinya ita kaďai ga gajiya ga ba'kunta, baywar ALLAH harma ta fara barci anan.
Nawaf ya ce, "hajiya iya aii anan zata kwana dama, miyasa bataje wajensu kuluwa tayi hiraba?, A'a ni ce, "na hanata dan naga tagaji wannan garin naku mai nisan tsiya.
To shike nan ni bari naje na kwanta, sai da safe.
Kaga dawo ka tada ita, saitafi sakewa acan, anan aii takura zatayi, dan yaran su hanne fitsarin kwance sukeyi, kuma anan suke kwana, dan haka tada ita kuje can, itama zatafi jin daďi aii.
Batare da ya ce, "komai ba, yashiga kiran yasmeen! Yasmeen!!, ahankali ta buďe adanunta, danji take lamarin kamar amafarki, yauce rana tafarko dataji ya kira cikakken sunanta, amma "k shine sunan dayake kiran ta dashi, koyace mara kunya.
Ya ce, "tashi mana, tami'ke tana murza idanu, hajiya iya ta ce, "bita ahankali mana, saida safenku, nasa salmanu yakai muku kayanku tun ďazu.
Nawaf ya ce, "to saida safe, yay gaba yasmeen tabishi abaya tana tangaďi, ahanya tayi karo da bishshiya dalbejiya, Nawaf ya ri'ke hannunta yana faďin waike idan kina barci saiki zama tamkar 'yar kwaya??.
Itadai batace masa komaiba saima 'kara matse hannunsa datayi cikin nata.
Wani 6angare suka shiga agefe da alama shine 6angaren papa, idan kuma sunzo nan suke sauka.
Ďaki ďaya yanufa, wanda aka kunnawa fitilar kwai, 'katuwar katiface aďakin, dan haka suna shiga yasmeen ta kwace hannunta ta kwanta, dan barci takeji sosai.
Nawaf ya girgiza kai, yana faďin yarinya kamar 'yar kwaya?, ya canja kayansa zuwa na barci, "k kitashi ki cire waďannan kayan mana!.
Yasmeen ta gyara kwanciyarta dan ALLAH kabarni ALLAH na gaji barci nakeji, tsaki yayi ya ce, "dallah ca akayi kitashi ki cire waďan nan kayan, yasmeen ta tashi tana murza idanu, ya hawo katifar ya kwanta, yana mita, zaki wani ishi mutane da faďin kin gaji to waye bai gajiba?, nida nakawo mu nan bance nagajiba saike!!.
Banza tayi masa, tasaka hannu ta kashe fitilar kwan dakeci.
Nawaf ya ce, "wane irin iskanci?, ne wanan zaki kashema mutane fitila?, saida ta murguďa baki kamar yana ganinta, ta ce, "to kaya zan cire.
Tsaki yaja yakoma ya kwanta, aikin banza ubanmiye abin kallo ajikinki dazaki wani rainama mutane wayo, ya 'kare maganar da kwafa, kyaaaaaak!!!
Yasmeen ta ce, "oho dai nidai baza kayi daniba agidan mutane, shiru yayi kamar bai jiba.
Tagama shiryawa tai tsaye tana tunanin inda zata kwanta, dan bazata haďa makwanci da 'katoba, ta ce, "kabani bargon na shinfiďa a'kasa na kwanta.
Ya ce, "zoki kwata mana.
Shiru tayi bata tankaba, azatonsa ta kwanta a'kasane, yaďauki wayarsa ya kunna fitila, saiya ganta gefensa tsaye jingine da bango, ya ta6e baki yakashe fitilar ya juya mata baya.
Ta saka hannu da niyyar yaye bargon, caraf ya dam'ke hannunta, ya mirďe, ta kwalla 'kara, ya fincikota ta faďo jikinsa.
Ya ce, "ni wai sa'ankine??.
Tai masa shiru tana hawaye, fitilar wayarsa yasake kunnawa, ya haske mata idanu, ta rintse idanunta kam.
Ya ce, "matsoraciyar banza, nizaki yayema bargo, ta ce, "nifa ba ďauka zanyiba, ya ce, "to mizakiya.
To kasakeni basai na gaya makaba., ya ce, faďi ahaka mana.
ALLAH zan cijeka idan baka sakar mini hannuba,, hhhh yaro man kaza, ki cijeni mana, aii kinsan halina sarai.
Shiru tayi masa, gata ajikinsa ga hannunta amurďe, damma yau bai murďeba sosai, ganin bashida niyyar sakinta saikawai ta maida kanta saman 'kirjinsa ta kwanta, dan barci takeji.
Nawaf ya lumshe idanu tareda sakin sassanyar ajiyar zuciya, yasmeen tana jinsa.
Ahankali ya janyeta daga jikinsa, dan yanda yakejinsa ďinnan zai iya aikata mata aika2 wlhy.
Kwanciyarta yagyara tacigaba da barci abinta.
Ya haska fuskarta yana murmushi, wanda shi kansa baisan na miyeba, dahaka barci yay awon gaba dashi shima.
Chapter 25 · 0% Book details