← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 30 OF 51

Sashe 30

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

Assalamu alaikum
Kuyi ha'kuri masoyana, kunjini shiru ko??, wlhy har yanzu banida lafiyane, saida nakwanta asibiti kwana biyu.
Ngd sosai.
Luv u oll❤❤❤😘

©2016

💞bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞luv u oll my fan's😘💞
[1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆

NA BILKISA IBRAHIM💞

Page👉🏻37 & 38

......Abdallah yakara wayar akunnensa tareda faďin Abi!!.
Nawaf ya daka masa tsawa kai!! Dallah yimin shiru mana, sai yanzu kaga damar yimini magana.
Cikin rawar murya Abdallah ya ce, "Abi kayi ha'kuri wlhy bana kusada wayar, aunty ce taďaga.
Nawaf yaja tsaki wace aunty??.
Aunty yasmeen mana, wayana tana hannunta ne, yanzu nashigo shine tabani.
Nawaf yaja wani gwauron numfashi ya ce, "tana ina??.
Da sauri Abdallah yajuya inda yasmeen take zaune amma saiyaga wayam ta tashi ya ce, "Abi ta tashi, bari na duba kotana falo.
Ya duba falo batanan har waje.
Ya ce, "Abi wlhy ta 6uya yauma.
Shiru Nawaf yayi danji yake kamar zuciyarsa zata fashe, ya kula da gayya yasmeen take 6uya aduk lokacin dayace abata waya, ya yanke wayar batareda yasake cewa komaiba dan haushi..
Abdallah ya girgiza kai, yana mamakin hali irin na Abi!, shi daban yake da sauran mutane, yata6e baki tareda jefa wayar saman gadon momcy yafice.
Yasmeen tabuďe Bayi tafito, dak wanda ya kalleta yasan tasha kuka, tafaďa saman gado tana share hawe, lokaci yayi dazata nemawa kanta mafita, dukma yanda za'ayi saita cire son Nawaf azuciyarta, bazata bari sonshi yacigaba dayin tasiri azuciyar taba, takuma fashewa da kuka tana dukan 'kirjinta, cikin kuka take faďin saika fita! saika fita!! saika fita!!! Daga zuciyata bazan yi dakon son wanda baya 'kaunataba, dolene na canja kaina kota halin 'ka'ka Tacigaba da kukanta.
Nagirgiza kai kawai nafito.

Nawaf kam dafe kai yayi dan ba'kin ciki, yashiga share zufar dake kwararo masa adukkan sassan jikinsa, dukda AC dake aiki acikin ďakin, ya 6alle murfin gorar yashiga kwan kwaďa, saida ya shanye duka sannan yamaida kai ya kwanta yana fitar da huci, kamar wanda yafito daga filin danbe.
Yaďanja tsaki waishi ya akayima ya faďa tarkon son wannan yarinyar?, dayasan inda son yake datuni yacireshi ya yarda ya huta, yana zaman zamansa amma yanzu ansakashi cikin wani yanayi, ya huro huci mai zafi daga bakinsa, wayarsa yajawo yashiga bincikar ma'ajiya hotuna.
Hotunan bikinsu yashagala da kallo, duk inda yasmeen take a hoton ta 'kayatar, takuma bada ma'ana, ya sumbaci wani hoto datayi masa 'kyau sosai, gawani 'kayataccen murmushi data saki a hoton, kamar kakirata ta amsa, ya lumshe idanu ahankali yana murmushi, tareda rungume wayar a 'kirjinsa tsam, jiyake kamar ya rungume yasmeen.
Na ce, "lallai su Nawaf modebbo an faďa tarkon SO!!!!!!.😜
_______________________________
Haka rayuwar take tafiya, kowannensu yana dakon soyayyar ďan uwansa, amma batareda sun sanar da junansuba.
Dan har yanzu yasmeen bata amince sunyi waya da Nawaf ba, dukda yana tsananin bu'katar hakan, yabi duk wata hanyar dazasuyi magana da juna amma yasmeen ta tosheta, hanya ďaya tarage masa itace momcy, itakuma yanajin kunyar tunkarar ta, yana gudun kuma kar allura ta tono garma.

Yau yasmeen antashi da murnar zuwa gida, tanata farinciki zataga ummarta da abba, mas'ud ne ya kaisu itada Ameena, bayan momcy ta haďa mata shatara ta arzi'ki takaima su umma.
Mas'ud yanayin parking ta shilla da gudu cikin gida, Ameena da mas'ud suka tuntsure da dariya.
Da gudu tashiga kuwa, ta rungume yaseer dake zaune afalo, suka shiga ihun murna su biyu, umma tafito daga ďaki danjin ihunsu, da sauri yasmeen ta saki yaseer tanufi umma ta rungume ta.
Umma ta ce, "nikam karki karyani yasmeen, yasmeen tasaki umma tana turo baki gaba, kai umma bakiyi kewataba ma kenan??, umma tayi dariya, haba ni na isa badole nayi kewar mamana ba, taja hannunta suka zauna.
Yasmeen ta ce, "umma ina abba??, abbanku yafita amma zuwa anjima kaďan zai dawo.
Bayan mas'ud yashiga sun gaisa da iyayen Ameena saiya shigo nan suka gaisa da umma, zuwa sannanma abba yadawo, daga nan saiya tafi akan anjima zai dawo ya ďaukesu.
Anan suka wuni suna mai jin daďin kasancewar su cikin 'yan uwansu, anan yasmeen takeji ashe Nawaf dazai tafi saida yazo yay musu sallama, kuma yana kiransu su gaisa, musamman ma abba da yaseer, dan ita umma tanajin kunyarsa sosai, wato itace yaraina, yamaida sakarai, baya 'kaunarta, itama zata nuna masa baya gabanta bai dametaba, duk a zuciyarta take maganar.
Sai dare mas'ud yadawo ya ďaukesu, yasmeen harda kuka, saida abba yay ta lallashinta sanan, amota su ameena sunata mata dariya, itadai shiru tayi musu, mas'ud yakira Nawaf yasanar masa.
Nawaf bayaso ya nunama mas'ud yafara son yasmeen danzai takura masa da tsokana, dan haka ya ce, "matsalarta ce, dama tasamu akace taje zata wani yima mutane kuka, kaika zauna take maka kuka a mota.
Mas'ud ya ce, "kai malam niba abinda nakiraka kaminba kenan, sai anjima, ďif yakashe wayar.
Nawaf ya rintse idanu, jiyake kamar mas'ud ya kwala masa 'karfe akai, yadafe kai tamkar zaiyi kuka, wai miya hanashi cewa ma abama yasmeen wayar, koba komai aida yaji muryarta, yasan zai rage wani raďaďin, shikaďai yasan yanda zuciyarsa take azalzalarsa a kan son yasmeen, amma ita bata damu dashiba, dolene yaďauki matakin goge soyayyar yasmeen a zuciyarsa tunkafin zuciyarsa tabuga abanza a word. .
Su yasmeen Suka isa gida, saida suka rakata har falon momcy sanan, bayan sun gaisa da momcy suka koma gida ita kuma yasmeen tazauna suka hau hira dasu Anwar.
_________________________________ yau tunda suka tashi su Abdallah suke ďokin ganin wasan su Nawaf dazasuyi, dansunce wasan mai zafine, 'kiri2 Anwar ya'ki zuwa islamiyya saboda ya kalli wasan, Abdallah sai tsokanarsa yake, wai yau su ustaz an ajiye ustazanci saboda kallon kwallo.
Anwar yay tsaki ALLAH kaga abi kabari, inba hakaba zan haďaka da papa wlhy, dakaine yanzu saikace zaka 6ata mini rai kuma, ya 'kare maganar yana turo baki gaba.
Yasmeen ta ce, "barsa kaji auta, ai akwai ranar ramuwa tana zuwa.
Momcy tafito daga ďaki tana faďin miya faru kuma??, Anwar yagaya mata abinda Abdallah yafaďa, ta ce, "to ya isa haka, amma Auta yanzu nan sabofa wasannan ka'ki zuwa islamiyya ko???..
ALLAH A'a momcy, yau 'kari za'a mana kuma na iya wajen shiyyasa, momcy tazauna tana faďin to shikenan aii.
Babu daďewa aka fara wasa, falon yayi tsit, kowa idonsa yana kan tv, yasmeen wani daďi takeji a zuciyarta dan ganin Nawaf, koba komai tarage raďaďin dake damun zuciyarta na son wanda bai damu da itaba.
Wasa yayi wasa, anata gwagwarmaya da juna dan kowa gwanine, har akaje hutun rabin lokaci babu wanda yaci.
Bayan andawo babu daďewa ASINAL ta zirama su Nawaf kwallo, wannan yasa suka dage suma da bada 'kaimi, to suma su Nawaf sun zurama Asinal kwallo ďaya a raga, ana gab da tashi Nawaf ya 'kara zirama Asinal kwallo araga, cikin jin haushin kwallon dasukacisu wani ďan wasan asinal ya taďe 'kafar Nawaf yafaďi.
Bisa tsautsayi wani yataka kafarsa da wannan mugun takalmin na 'yan kwallo.
Wata irin 'kara Nawaf yasaki, wadda tai daidai da wadda yasmeen tasaki afalon.
Da sauri momcy tari'ke yasmeen, su Anwar ma kuka sukeyi dan duk wanda yagani yasan Nawaf yaji takawarnan ajikinsa.
Masu taimakon gaggawa suka rufu akansa, daga bayama ďaukesa akayi daga cikin filin gaba ďaya.
Awannan lokacin hankalin duk wani masoyinsa atashe yake, musamman ma mutanen 9ja da saudia, harda sauran 'kasashen duniya, dan duk wanda yake abinda duniya zata sansa dolene yasamu ďunbin masoya aduniya dakuma ma'kiya.
Nima kaina saida nayi masa kuka, dan yana cikin jin jiki.
Arikice papa yashigo gidan dan shima yakalli wasan a office.
Wasu takardu yaďiba yafita yana mai bama iyalin nasa ha'kuri, airport yanufa wajen wani abokinsa, domin nema musu biza shida iyalinsa.
To dayake babban mutumne kuma mai alfarma, sai aka samu babu 6ata lokaci, zuwa gobe jirginsu zai ďaga.
Yadawo gida ya sanar dasu halin da'ake ciki, dan haka momcy da yasmeen suka fara shiri, sune zasu fara yin gaba, sukuma su Abdallah zasu taho abaya suma.
Ranar haka gidan aka wuni sukuku kamar anyi mutuwa.
Chapter 30 · 0% Book details