← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 11 OF 51

Sashe 11

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 6 min read

KIRA
mu mata munada al'adar cewa sai mun auri mai kud'i, kuma hakan ba daidai bane, kedai amatsayinki na d'iya mace kamata yayi kiyi addu'a ALLAH yabaki miji nagari mai 'kaunarki da gsky.
Wlhy masu kud'innan damuke hari ba kowane yadamu da fita ha'k'kin iyalinsaba.
Musamman ma mazan hausawa, idan suna samun kud'i sunfi maida hankalinsu ga neman kud'in fiyeda 'ya'yansu da matansu.
Wani saiya had'a wata uku zuwa hud'u baya 'kasar, yabar matar cikin damuwa da kewa, shikuma yanacan tareda karuwai a hotel, to dan ALLAH miye ribar auren irin wanan mai kud'in.
Idan baki kai zuciya nesaba saiki fara bin mazan waje da aurenki, ALLAH ya kiyayemu.
Idan kuwa kika auri talakannan daba kiso, duk inda yafita zuwa yamma yadawo, zai kula dake zai kula da 'ya'yanku, UBANGIJI ALLAH yasa mu gane amin.

Yasmeen kuwa tana cikin damuwa, tanaso ta koma makaranta amma abba ya ce, "tabari mijinta yazo ta gaya masa, tayi kukan harta gaji dan tanaso takoma makaranta gashi anata wuceta a lectures.
Yau suna zaune afalo harda umma da abba, sunata hirar gida, abba yana cewa lokaci kad'an yarage suje kwangwalan dansuga dangi dangi su gansu, yaseer yanata murna, amma yasmeen ko motsi batayiba.
Abba ya ce, "mamana lafiya dai??, tai firgigit tana fad'in lafiya lao abba, ya ce, "inafa lafiya munata magana amma ba'kya tare damu, zonan mamana naji damuwarki kinji.
Jiki a sanyaye yasmeen ta tashi taje kusada 'kafafun abba ta zauna, yadafa kanta yana fad'in mike damunki? fad'amin!.
Saida ta matso hawaye sanan ta ce, "abba makaranta ta.
Tofa, abba ya fad'a, yanzunan dama saboda bokonnan kika takuri kanki, to aii na ce, "ki bari mijinki yazo saikuyi magana.
Babansa yakirani d'azu ya ce, "gobe zasuzo insha ALLAHU, dama baya nanane shiyyasa bai zoba.
Cikin sigar lallashi ya ce, "kiyi ha'kuri kinji mamana, ki d'auki duk abinda ya sameki amtsayi 'kaddara.
Yasmeen ta d'aga kai tana hawaye,. Abba ya ce, "yauwa mamana ALLAH yay muku albarka kunji, ya tsare mana ku.
Umma da yaseer sukace amin.
Daga nan yasmeen tad'an saki jikinta tana d'an saka baki a hirar tasu, amma ba sosaiba.

NAWAFF
yau da yamma Nawaf ya iso kano, zaid'an kwana biyu ya koma abuja, kafin aci gaba da wasa.
Sunyi murnan ganinsa, momcy ta shafa kansa cikin hausarta dabata gama nuna ba ta ce, "my dear duk ka rame wlhy, mike damunka haka??.
Nawaf yad'an cije leb'ensa na 'kasa ya ce, "momcy wanan auren da papa yay min mana, ALLAH bazan 6oye mikiba bana son aurenan momcy, ya'karasa fad'a cikin raunin murya.
Momcy ta kwanto dashi gefen kafad'arta ta ce, "kayi ha'kuri Abbuna ina ji ajikina wanan auren Alkairine a gareka, kuma yanda su Abdallah suke bani labarin matar taka da gidan data fito duk masu mutuncine, da tarbiyya.
Banaso akan aurennan kabari sa6ani yashiga tsaka ninka da papan ku, ka danne zuciyarka ka koyi son matarka tunkafin tadawo hannunka.
Zanta tayaku da addu'a insha ALLAHU, itama ALLAH yacusa mata sonka kaji, dukda nasa modeebbona abin sone ga kowacce mace, babu macen dazata gansa ta ce, "bataso, momcy ta 'karashe maganar da tsokana.
🙈hannu yasa ya rufe idanunsa don kunya.
Momcy tayi dariya, ato idan kuma bakaso mutafi saudia kaza6a cikin dangi, gama ummuhabeba nan kullum damuwarta tana kanka, kaga sai kawai musha biki.
Nawaf ya zaro idanu😳 ya ce, "momcy yi shiru kar papa yaji, danni bana ra'ayin zama da mata biyu, kuma ma bana son ummuhabeeba tacika 'kyau dayawa nikuma bana son macen data cika 'kyau gsky.
Tofa, momcy tafad'a, wanan kuma wani sabon idea ne na rashin son auren 'kya'ky'kyawar mace??.
Nawaf yay murmushi har fararen ha'koransa suka fito, ya ce, "A'a my sweet mom ra'ayina ne nidai!!!....
Abdallah ya shigo da sallama, Nawaf ya ce, "ka amso mini?, eh yaya na amso, na kaimaka d'akinka banyi zaton kana nanba aii.
Okey babu damuwa, amma yau miya hanaka zuwa islamiyya ne??, Abdallah yad'an sosai gefen wuyansa yagyara zama zai shararo 'karya.......Nawaf ya dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu🖐🏻kaga basai kafad'aba, dan nasa 'karya zakamin.
Momcy ta ce, "aii dama jira nake kadawo na sanar maka kwata2 Abdallah baya son zuwa islamiyya, danshi bai biyo halinkaba, tun kana shekara sha biyar ka sauke ALKUR'ANI, amma Abdallah har yanzu baikai ko izufi 50 ba nakula Anwar ma yakusa kamosa.
Harara Nawaf ya watsa masa, ya ce, "wato kai nakula kaine mara ji d'in gidanan ko?, wlhy ka maida hankalinka kajiko, ku a tunaninku karatun boko shine wayewa ko??, amma ai baka ta6a fashin makarantar bokoba ko??.
Kun manta karatun bokon iyakarsa nan duniys, karatun islamiyyar dabaku basa muhimman cinba shine zai zame mana tudun dafawa awata rana mai cike da rud'ani.
Wlhy daga yau nasake jin bakaje islamiyyaba sai ranka yayi matu'kar 6aci, tashi kabani waje sakarai kawai.
🚶🏼sum sum Abdallah yatashi yashige d'akinsa yana zum6ura baki.

WASHE GARI
Tunda wuri umma da ameena suke hidimar had'a abubuwan tarbar ba'ki amma banda yasmeen data shige d'aki wai batada lfy.
Dan haka umma taje ta nemo Ameena 'kawar yasmeen d'in dan ta tayata.
Yasmeen kuwa tana d'aki cikin fargaba da damuwa, wai yau zataga mijinta, ko zaizo mata da mutuncine?, kokuma sa6anin hakan??.
Har zuwa azahar tana d'aki tana kullawa da kwancewa, dakuma fad'uwar gaba.

a wannan lokacin kuwa Nawaf yanacan anci kwalliya cikin 'kananun kaya, ya fito shida mas'ud sai zabga 'kamshi suke, 6an garen su momcy suka nufa, afalo suka iske momcy da papa dasu Anwar.
Papa ya ce, "kunyi 'kyau sai dai modeebbo koma ka canjo kaya wad'anan basu yiba.
Nawaf yabi jikinsa da kallo, papa miye aibun wad'anan kayan yafad'a cikin shagwa6a.
Papa ya ce, "aibunsu dasuka kasance 'kananun kaya, kai bakaga shigar da d'an uwanka yayi ba mas'ud.
Gidan surukai zakujefa, kuma yau zasu fara ganinka, sai kaiwai suganka da 'kananun kaya kamar d'an yahudawa, maza kaje ka canjo shadda ina nan ina jiranka, dan kuna 'kara 6ata lokaci.
Badan Nawaf yasoba yakoma ya sako farar shadda 'kal d'inkin zamani, harda saka hula, kai yayi 'kau wlhy, saiya fito asalin balarabensa, dan dakaga Nawaf dole ka kirashi ci kakken balarabe.
Nawaf dogone sosai yanafa jikin 'karfi sabida training dayakeyi, yana da suffa irinta kosashshen xaki, daga sama 'ka'k'karfane sosai cikinsa ad'ame tamkar baya cin abinci, farine amma ba tas ba, kalar fatarsa irinta larabawace jaa kenan zamuce, yanada suma mai yawan gske mai kuma laushi d 'kalli dukda tanashan gyara da mayuka masu tsada, yanada d'an saje wanda ya tsaya iya kumatinsa dai dai kunne, ida nunsa masu 'kyau da haske ga girar ido zara zara, kai komaidai yaji d'ammmmm.
Papa yay murmushi yauwa ko kaifa modeebbo, yanzu kaga shine mutuntawa, sai kuje banaso naji wani abinda zai 6ata mini rai, kuma ku sayi wani abu akai mata kar aje hannu rabbana, ku gashe mana dasu.
Mas'ud ne kawai ya amsa.
Abdallah ya ce, "yaya dan ALLAH zanje.
Harara Nawaf ya watsa masa wadda tasakashi saurin rufe baki.
Sukuma suka fice.
Papa ya ce, "huum d'an yanzu saka barsa da halinsa kawai.
Chapter 11 · 0% Book details