← Book details Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 2 OF 51

Sashe 2

Nawaff Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Ab'an garen su NAWAFF kuwa, sai mas'ud ne ya tuk'a motar, dan NAWAFF ya kasa saboda b'acin rai, tunda ya zauna akujerar gefen direba ya lumshe idanunsa masu haske, bai sake cewa uffan ba.
Mas'ud yanufi hanyar gida dasu dan yasan ran 'yan maza ya b'aci, kosunje inda sukayi niyyar zuwa NAWAFF bazaya sakeba, saboda yana cikin b'acin rai.
K'ofar wani matsaikai cin gida mas'ud yay hon, da sauri mai gadi yabud'e get d'in, mas'ud ya danna hancin motar zuwa ciki.
Ba laifi gidan yanada d'an k'yau kuma daga ciki babbane, NAWAFF ya fito yanufi cikin gidan, kai tsaye gidan ya shiga, amma babu kowa a falon, fitowa yayi yanufi b'an garensa wanda baikai girman inda yafara shigaba.
Ya fad'a saman doguwar kujera ya lumshe idanu, mas'ud yashigo ya bishi da kallo kawai.
NAWAFF ya mik'e yashige bedroom d'insa, bayi yafad'a batareda ya cire kayan jikinsaba ya sakarma kansa shawa, yakai tsawon minti goma ahaka, sannan ya cire kayan jikinsa yay wanka yafito.
Jalla biya kawai ya zura ya dawo falon, mas'ud na kwance a kan kujera mai zaman mutum biyu, ida nunsa nasaman tv yana kallon.
NAWAFF yafito yazauna batare da yayima mas'ud maganaba.
Mas'ud yad'ago yana kallonsa, dan shima yasan bazai tanka masa d'inba, yako bushe da dariya yana kallon NAWAFF.
Nawaff ya d'ago yana hararar sa, yaja tsaki, tareda d'aga goran ruwa ya kwankwad'a, har sannan mas'ud yana kunshe dariya.
Cikin masifa Nawaff ya ce, "dallah malam wai miye hakane??, zaka wani tasa mutane gaba kana musu dariya.
Mas'ud ya ce, "kajimin mutum, ina ruwanka da dariyata, ko kaji na ambaci sunan kane??
Ammafa wlhy d'an uwa kun dace da yarinyar nan gsky.
Wata uwar harara ya yasakar masa, batareda ya tanka masaba ya mik'e ya fice.
Mas'ud yacigaba da dariyarsa, kamar wani mahaukaci................✍🏻

Ina godiya ga d'umbin masoya, dasuka turomin sakwannin taya murnan kammala book d'in NI DA AMINIYATA ngd ALLAH yabar k'auna😘❤❣👈🏻

Kuyi hak'ura daga nan zuwa wani lokaci, zaku cigaba da samun page 1 ne kullum arana, kawai, kafin komai ya daidaita ngd.

💞bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞LUV U OLL😘😘😘😘💞💞
©2016
[1/12, 8:53 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾NAWAFF🎾
☆☆☆☆☆☆☆

NA BILKISA IBRAHIM💞

Page👉🏻4

Yasmeen tafito sanye cikin jan les, d'ikin riga da siket, ta nad'e kanta da d'auri mai k'yau sai zabga uban k'amshi take, ga farin mayafi da farin takalmi, abin sai wanda yagani.
Mahaifiyarta ta bita da kallo, ta ce, "kai yasmeen d'in abba kinyi k'yau, kamar kece amaryar.
Hannu tasaka ta rufe fuska🙈 ta ce, "kai umma.
Umma tayi dariya ta ce, "to nabari, yanzu ke dawa zaki tafi, koda yaseer zakuje.
Yasmeen ta turo baki gaba, ta ce, "ALLAH umma bazanje dashiba, kina ganin jiya abinda yay min aii.
Yaseer dake zaune yana cin abinci ya ce, "nima ba zuwa zanyiba, dan haka maida wuk'ar, ni nan dakike gani kallon kwallo zani.
Yasmeen ta harareshi, aii kallon kwallo kawai ka'iya, mara aikinyi.
Yaseer ya tab'e baki, ke kuma zuwa biki kawai kika iya, ni wlhy nak'agara abba ya aurar dake abar mini filin ma.
Yasmeen ta kai masa duka, ya kauce yana dariya, cikin shagwab'a ta ce, "umma kin gansa ko?, umma tayi dariya, ta ce, "nikam babu ruwana, tunda kekika zauna yaseer ya rainaki, wanima saiyace shine yayanki aii.
Yaseer ya ce, "to umma ba'ita ta tsaya shagwab'a ba, shiyyasa akecewa nine yayanta, yafad'a yana mata 😜.
Yasmeen tabishi zata daka, suka fara zagaye falon, umma te ce, "kinga mamana k'yaleshi, zokiyi tafiyarki, kinga karkije ki fad'i da wannan takalmin mai tsinin tsiya.
Yasmeen ta tsaya tana turo baki, yayinda yaseer yake tsaye bakin k'ofa yana dariya, ta harareshi, habawa yaro wlhy zan dawo nasameka, saika gayama aya zak'inta.
Yaseer ya ce, "saidai mu fad'ama ayar tare, yana gama fad'a ya fice.
Itama dai sallama tayima umma, ta ce, "zataje su tafi da ameena, umma ta ce, "to hakanma yayi, amma kudawo da wuri.
Yasmeen ta ce, "to umma za'a kiyaye.

Tana fita gidan su Ameena ta shiga, gsky gidansu ameena yafi nasu yasmeen k'yau sosai, a get suka had'u, ameena ta ce, "yauwa garama haka, dama bana son nashiga mu b'ata lokaci.
Yasmeen batace komaiba taja hannun ameena suka shiga mota balarabe yaja.
Wani had'ad'en guri aka kaisu, bazan fad'i gurinba dan karsu teema suce zasu itada deexerh😜, wajen yayi matuk'ar had'uwa, anshirya komai, yanda yakamata, yasmeen ta ciro waya a jakarta takira wata no.
Ana d'auka ta ce, "Asmy ALLAH ke 'yar is... ce, kince babu African time amma gashi waje babu kowa.
Daga can akace sorry my dear gamunan, wlhy laifin Safwan ne shida abokansa, wai sun tsaya jiran babban aboki, kuma har yanzu bai isoba, amma gamu nan zuwa.
Yasmeen tayi d'an tsaki ta ce, "inji dai ba d'an iskan jiya bane daya shanyamu.
Amaryar ta ce, "wlhy shine.
Yasmeen taja tsaki, tswww, sai kuma akace dole saidashi za'ayi komai, cikin haushi ta kashe wayar batare da tajira amsar Asmy ba.
Ameena ta ce, wai mitace miki??, yasmeen ta yatsine fuska, wai d'an iskan jiya suka tsaya jira, saikace wani d'an gwal, kina ganin yanda ya shanyamu jiya, daga k'arshe dan rainin hankali saiya aiko mana direba.......
Yasmeen bata rufe bakiba motocin su Asmy suka fara shigowa.
Bayan tsayawar su mutane suka fara fitowa, kowa yana neman wajen zama, saida kowa ya zauna sannan yasmeen ta je tafito da Amarya, ango ma yafito, 'yammatan amarya da abokan ango suka take musu baya har inda aka tanadar musu.
Sai kujeru biyu a gefe wanda babbar k'awar amarya zata zauna, da babban abokin ango.
Yasmeen ta zauna kusada asmy amarya suna magana kus2, yayinda aka fara gabatar da abinda yatara mutane.
Zuwa can mai gabatarwa ya fara wasa babban abokin ango da aka dad'e ana jira, gaba d'aya hankalin mutane yakoma kan had'ad'd'iyar motar data tsaya kalar jaa da ratsin fari, gsky motar ta d'auki hankalin mutane, sai dai banda yasmeen, da waya ta d'auki hankalin ta.
Tunda yafito ake ihun fad'in sai modeebbo! Sai modeebbo!!. Shikam hannu kawai yake d'aga musu yana murmushi, har wajen zamansa aka rakashi wato kusada ango.
Bayan anyi shiru, akayima babban abokin ango barka da zuwa, ya k'ara d'agawa mutane hannu yana murmushi.
Ango ya ce, "mutumina ina ka mak'alene haka, tuni kai ake jira, cikin muryarsa mai dad'i ya ce, "ayimin afuwa my friend wlhy matsaya jiran mas'ud ne, baima dawoba hakanan na hak'ura na taho.
Ongo yay murmushi ya ce, "anyi maka modeebbo, sukai murmushi tareda yin musabaha.
Yasmeen koda tagama wayar bata damu kanta da son ganin waye babban abokin angonba, dan haushinsa takeji sabida b'ata musu lokacin dayayi jiya.

Mai gabatarwa yafara kwala kiran sunan yasmeen Abubakar habeeb, tazo ana gayyatarta.
Yasmeen ta dad'e zaune bata motsaba saida Asmy ta ce, "plz dear kitashi mana, yasmeen ta ce, "ALLAH kunya nakeji dear.
Asmy ta harareta lallai dear awajen aurena kike jin kunya.
Aka cigaba da yayata sunan yasmeen dole ta mik'e tsam tanufi inda aka tanada.
Ya mik'a mata abin magana🎤, tareda fad'in munaso ki gabatar mana da kanki, dakuma tarihin amarya.
Jiki a sanyaye ta karb'a, 🎤👩🏻duk ta takura saboda kallon da mutane suke mata, ta d'auki hankalin yawancin gays d'in wajen, ahankali tafara magana, cikin murya mai zak'i, aii wasu saida wutar kansu ta d'auke, harda babban abokin ango (modeebbo) yak'agara yaga fuskar mamallakiyar muryar nan.
ta fad'i sunanta da alak'arta da amarya, bayan tagama aka shiga yimata tafi.
mai gabatarwa ya ce, "itace zata gayyato babban abokin ango zuwa wannan waje.
Batare da musuba takarb'a takardar tafara kiran NAWAFF SA'ED MODEEBBO.
Takira yakai sau biyar amma bai ko motsaba daga inda yake, tajuyo dan ganin wai waye wannan d'an rainin wayon abokin angon.
Karaf idanunsu suka had'u a k'ar kashin inuwa d'aya, zumbur NAWAFF yamik'e tsaye.
Yasmeen ta ce, "taf tsuntsu daga sama gasashe, azuciyarta take maganar.
shima dai NAWAFF raya abinda zai faru yakeyi dan yasan dole sukwashi 'yan kallo, amma yasan maganin ta..........................✍🏻
Hahahha yauda budiri tsakanin YASMEEN DA NAWAFF.😂😂😂😂😜

💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞LUV U OLL😘😘😘😘💞💞

©2016
[1/12, 8:53 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆

NA BILKISA IBRAHIM💞

Assalamu alaikum.
Alhmdllh 'yan uwana kamar yanda nafad'a muku natsaya da rubutu sabida wani dalili.
To Alhmdllh yanzu komai ya dai daita, in farincikin kasancewa daku😘😘😂.

Page👉🏻5

.....Nawaff ya tsuke fuska, itama yasmeen ta tsuke tata fuskar.
Yak'araso gareta cikin wani taku na isa da tak'ama, wajen yayi tsit ana kallonsu, yayinda masu hotuna suketa haskasu.
Yak'araso daf da ita, tamkar zai shige jikinta, tayi saurin ja baya, ya had'a yatsunsa biyu yana bugawa, yay k'asa da murya yanda ita kad'ai zata iya jinsa, ya ce, "wlhy kika yimini hauka awajennan saina aikata miki abunda 'yan jaridu da mujallu zasu buga a safiyar gobe juma'a.
Dukda tsoro mai tsanani yashigi yasmeen wannan bai hana ta hararar saba, ta rik'e k'ugi cikin tsiwa ta ce, "kai baka isa kasa 'yan jarida yad'aniba, kuma ALLAH shizaimin tsari da sharrinka.
Nawaff modeebbo yad'an d'ago yana kallon yanda hankalin mutane yadawo kansu, saiya saki murmushi na basarwa.
Gaba d'aya gurin yad'auki sowa da fad'in sun dace da juna.
Nawaff yaja tsaki tareda fad'in shashashu kawai, ta ina na dace da wannan mai kama da aljanar.
Yasmeen ce kawai taji furicinsa saikuma mai gabatarwa dayake kusada su tsaye.
Yasmeen tai murmushin takaici ta ce, "ai basu bane shashashun kaine babban shash............kafin tarufe baki ya damk'o hannunta ya murd'a da k'arfi, wani tsananin zafi yaratsata har kwakwalwa, ALLAH yasota fitilar gurun Blue ce tana kuma kunnawa ta kashe, dan haka ba kowa yaga muguntar da Nawaff yake mataba.
Zafin ya ratsata sosai, afusace ta watsa masa mari, da sauri yasaketa yana murza kumatu, itama takoma kusada amarya da sauri ta zauna tana haki.
Nawaff yad'ago da sauri danjin andafa shi, mas'ud yagani tsaye.
Mas'ud ya ce, "plz my bro's ka share kawai, karka bari wani yagane wani abu dake faruwa.
Nawaff ya kalli mas'ud da idanunsa dasukayi jaa, ya ce, "wlhy Mas'ud saina yima yarinyarnan abinda zatayi dana sani arayuwarta, kamar yanda ka buk'ata zan barta ammafa had'uwarmu tagaba batada k'yau ko kad'an, kuma ka rubuta ka ajiye.
Yana gama fad'a yakoma mazauninsa dake kusada ango, mas'ud ne ya wakilcesa, wajan fad'ar duk abinda ake buk'ata.
Chapter 2 · 0% Book details