← Book details Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 30

Sashe 8

Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai Aabidah ta yi cike da sarewar guiwa ta zira hannu a jakarta ta zaro kuɗi ta ajiye a cikin ƙwaryarta. Ɓacewar Bokan daga wajen da yake ne ya basu damar fitowa daga ɗakin da baya da baya suka bar gidan. Su na shiga mota Aabidah ta ja dogon numfashi ta shaƙi iskar cikin motar mai cike da oil perfumes da take sakawa da kuma turaren mota. Ganin Innaji na ta sharar hawaye ne ya sanya ta juya ido sama ta kunna motarta suka bar wajen. Kai tsaye gidanta suka nufa domin a ƙa'ida idan suka fita sai sun biya ta gidan Aabidah Innaji ta ci ta sha sannan ta yi guziri da duk abinda yayi mata. A bakin gate Aabidah ta tsayar da motarta tana ta danna horn kamar za ta tashi sama. A guje Laminu mai gadi ya isa ya buɗe mata gate ɗin wandonsa a hannu,da alama zagayawa yayi kuma bai gama uzirinsa ba ya taso gudun kada uwar ɗakin nasa ta balbale shi da masifa. Kamar za ta bi ta kansa da motar haka ta shige gidan da tana cin magani,juya baya Laminu yayi yana jin wani irin tsoronta na sake huda shi. A haka ya kulle gate ɗin ya tsaya yana jiran ya ji saukar ruwan masifa daga bakin Uwar ɗakin nasa. Sai dai shirun da ya ji ne ya tabbatar masa da bata da lokacinsa. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi sannan ya koma banɗaki yana tsine wa talauci da yayi sanadiyyar kawo shi gidan MUGUWAR MACE kamar Aabidah.

A ɓangaren su Innaji kuwa suna shiga cikin gidan ta ware ta na kalle-kalle kamar wata baƙuwa,kallon sauye-sauyen da ta gani a parlour ta hau yi tana tambayar Aabida lokacin da suka sauya wasu abubuwan tare da ƙara wasu abubuwan. Guntun tsaki Aabidah ta ja saboda yanda take jin ranta babu daɗi game da abinda boka yace mata,rai a ɓace ta ce.

"Wai ke Innaji yau kika fara zuwa gidan nan ki ga sabon abu ne? Ke komai kika gani sai kin yi magana akai haba ! Idan akwai abinda kike so kawai ki yi magana na siya maki irinsa. Ni bari na shiga ciki na huta idan kin gama ki wa Laminu magana ya mayar dake gida,in kuma za ki jira ni sai yamma mu tafi plaza tare to ki jira."

"To me nake yi a gidan idan na koma banda mugun tunanin halin da yaran can suka jefa kansu a ciki? Shiga ciki kawai ki yi hutawarki Æ´ar albarka da yamman kin ajiye ni a gida."

Ɗaki Aabidah ta shige tare da bugo ƙofa ta rufe. Kai tsaye kayan jikinta ta hau cirewa sannan ta faɗa wanka,ta jima tana dirzar jikinta kafin ta fito sanye da bathrobe a jikinta kalar  purple mai haske. Kanta ɗaure da ƙaramin towel kalar bathrobe ɗin jikinta ta samu waje ta zauna a kujerar dake gaban madubinta tana shafa mai tana tunanin ta inda za ta fara hilato Maheer zuwa gidanta. Ta sani idan umarnin kawo Maheer ta bawa Aabid cikin awa ɗaya zai kawo mata shi gidan ko yana so ko baya so,to amma ta ya za ta sa Maheer zuwa gidan da kansa kuma da son ransa ba tare da ta samu matsala ba? Sanin kanta ne ita da Maheer sun tsani junansu,rayuwa suke yi kamar wuta da audiga,ko kuma na ce wuta da ruwa,shi ya tsane ta saboda halayenta da abubuwan da ta aikata a baya da wanda take kan yi a yanzu. Ita kuma ta tsane shi saboda yanda yake shiga mata hanci da ƙudindine a dikkan lamuranta,gashi uwa uba sihirinta baya tasiri akansa,kowa na tsoronta har uwar da ta kawo ta duniya da mijin da yake aurenta amma Maheer baya jin shakkar gasa mata magana ko kuma ya nuna mata kuskurenta a bainar nasi. Wannan dalilin ne ya sanya suka zamo kamar wasu manyan abokan gabar junansu. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta samu turarukanta ta fesa ta shafa na shafawa tare da goga roll on a hammatarta. Tana gamawa ta isa gaban dogon ɗakin da ma'ajiyar sutura da takalma da jakarta suke. Buɗe ƙofar ta yi ta shiga tana duba kayanta dake hange kamar a shago. Tsaki ta ja tana duddubawa tana yin wurgi da duk wanda bai yi mata ba. Cike da damuwa a ranta ta furta.

"Bani da kayan sakawa ma ni,ina jin zuwa gobe zan sa Aabii ya kwashe kayan nan na zuba wasu."

Da ƙyar ta tsayar da hannunta akan wata yaloluwar riga mai kyau kalar purple mai cizawa,a wajen ta zame rigar jikinta tare da towel ɗin kanta ta sanya rigar ta fito tana ɗaure gashin dokin da ta saka ya zuba har gadon bayanta. Kai tsaye saman gado ta haye ta rufa tana hamma. A haka bacci mai cike da mugayen mafarkan Bokanta na saduwa da ita ya ci karfinta.

A can parlour kuwa Innaji ce zaune a saman dinning table tana ta cin abinda duk yayi mata,domin kuwa sam ba sa rabo da soyayyan naman kaza,naman rago da dambun nama wanda Aabid kan yi order akai-akai. Shayin da ta haɗa mai kauri take firfitawa da bakinta kafin ta kai kofin ta kurɓa tana girgiza kai cike da jin daɗi. Sai da ta ci ta ƙoshi ta samu mazubi ta kwashi abinda take so a gidan sannan ta koma ɗakin baƙi ta kwanta dan ta huce gajiya.

Kasa bacci ta yi,dan haka sai ta zaro wayarta ta kunna data ta shiga social media tana kallon videos tana sheƙa dariya cike da nishaɗi. A haka bacci ya ɗauke ta har aka yi azahar da la'asar duk basu farka ba. Da misalin shida na yamma Aabidah ta fito cikin shirin fita tana sauri,gaba ɗaya ta manta da Innaji a gidan har sai da idanuwanta suka sauka akan  kayan abinci da na ƙwalamar da Innajin ta ɗiba. Tsaki ta ja sannan ta shiga ɗakin da takan sauka idan ta zo ta hau buga ƙofar da ƙarfi. A firgice dattijuwar ta fito tana ɗaura ɗankwalinta da ya kunce. Ganin Aabidah cikin shiri ne ya sanya ta komawa ɗakin da sauri ta ɗakko jakarta da mayafinta tana faɗin.

"Ohh kin ga gari har ya risina ina nan ina bacci. Mu je na kwashi kayana ki ajiye ni a gida."

Yamutsa fuska Aabidah ta yi sannan ta kalli agogon hannunta ta ce.

"Gaskiya Innaji sai dai na wuce plaza da ke Isuhu ya kai ki gidan,kamar yanda kika ga lokaci ya tafi ni ba zan samu damar kai ki ba."

Washe baki Innaji ta yi ta ce.

"Ai hakan ma babu damuwa. Shi yasa na ce miki ki ajiye min direba da mota saboda irin haka."

"Hmmm ba zan sake yin wannan gangancin ba Junaid ya takaice ni."

Jinjina kai Innaji ta yi jiki a mace ta kwashe kayan da ta ɗiba ta yi gaba,ganin yanda Innaji ta shiga damuwa sai zuciyar Aabida ta risina kaɗan,cike da tura baki ta karɓi jakar Innaji ta yi gaba. Su na fita ta rufe gidan suka shiga mota suka bar gidan. Tin daga nesa Aabid dake dawowa ya hangi motar matar tasa na fita daga gida. Wani irin abu ne ya caki zuciyarsa wanda bai isa ya bayyana shi da fatar bakinsa ba. Jiki a mace ya ci gaba da tuƙi ya isa gidansa a gajiye. Sai dai ya na shiga cikin gidan ya tarar da aikin da bai isa ya kwanta ya huta ba face ya kimtsa ko ina gudun kada matar gidan ta dawo ta tarar da datti ta balbale shi da masifa........

MUGUWAR MACE.

NA : HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️

*Za ku iya fara payment É—in littafin MUGUWAR MACE da yake akan farashin 1k ta 9031416423,ku tura shaidar biya ta 09031416423.*

*Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.*

*Slimming Tea 6k.*
*Slimming oil 3500.*
*Body scrub 3500.*
*Skin oil 2500.*
*Location Kano.*
*Phone No 09031416423.*

PAGE 7.

A gajiye Aabid ya fito daga wanka ɗaure da towel a jikinsa ya haye gado ya kwanta yana lumshe idanuwansa. Yunwar da ta fara neman agaji a tumbinsa ce ta sanya shi jan dogon tsaki ya yi juyi tare da ɗakko wayarsa da ya ajiye a bakin gado tun a lokacin da ya shiga ɗakin. Zuciyarsa na suya saboda tinanin abinda zai iya tararwa a cikin wayar ya buɗe password ya shiga TikTok,kai tsaye sunan account ɗin Aabidah mai suna Aaby142 ya shiga. Wani irin yawu ya haɗiye mai tsananin ɗaci saboda ganin sabon posting ɗinta da ta yi ita da yaron shagonta Mai suna Isuhu. Ransa ne yayi bala'in ɓaci ya sake shiga video na gaba yana jin ransa na ƙara ɓaci. Aabidah ce ke tafe tana rausaya mazaunanta da ƙirjinta sanye da ɗaya daga cikin sababbin kayayyakin da ta yi order tana tallata wa mutane tare da yin juyi da fari kamar wadda bata da igiyoyin auren kowa akanta. A haka suka dinga zagaye plaza ɗin tana ci gaba da nuna wa mutane irin kayayyakin da take siyarwa. Videos ɗin su na baya ya koma yana sake gani cike da ɓacin rai. Jin kansa na yi masa matsanancin ciwo ne ya sanya shi tashi da ƙyar ya shiga wajen da kayansa suke ya samu na bacci masu santsi ya saka. Sai da ya feshe jikinsa da turaruka masu daɗin ƙamshi sannan ya sauka ƙasa ya nufi wajen dinning table, ya na zuwa ya buɗe ya ga babu fiye da rabin naman dake saman wajen. Murmushi ya saki kawai ya girgiza kai,cike da sanyin murya ya ce.

"Hajiya Innaji kenan."
Chapter 8 · 0% Book details