← Book details Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 30

Sashe 29

Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɓangaren su Mudassir kuwa sai da suka lallaɓa Gwaggo suka kwantar mata da hankali sosai tare da tabbatar mata sun tarar da Salma yanda basu yi zato ba,suna kuma fatan ta tabbata cikin farinciki a gidan nata. Daga ƙarshe suka ajiye mata ƴan kuɗaɗen da za ta yi wa Salma siyayyar duk abinda bata da shi suka tafi.

Haka rayuwar Salma ta kasance a gidan Malam Rabi'u cikin ƙuncin da shi kansa bai san ƴar ƙaramar amaryar tasa tana cikinsa ba. Domin kuwa duk wata hanya da Samira ta san za ta goge sawun musguna wa Salma da take yi a gidan ta goge. Dan haka Malam Rabi'u da Malam Jamilu har alfahari suke yi da zaman lafiyan da su Samira ke yi. Lokuta da dama idan ya kawo nama ko kifi Samira yake bawa ya ce ta yi musu dabge saboda Salma ta ci ta ji daɗi. Ba tare da saninsa ba sai dai ta zuba wa Salma romo kaɗan ta bata,ita ta zauna ta cinye naman ko kifin. A hankali Salma ta dinga rama mai muni,Samira kuma na narka ƙiba abunta kamar mijinta shine mai kashe kuɗin domin ta ji daɗi.....

MUGUWAR MACE.

NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️

Mai son ci gaba da karanta littafin MUGUWAR MACE ya saka 1k ta 9031416423 Hamidah Ahmad Sanusi Opay. Sai a tura shaidar biya ta 09031416423. Don tsarkin mulkin Allah kada ki sayi littafi na idan za ki yaÉ—a shi ba tare da kin bari na kammala ba,idan kika yaÉ—a kamar kin dakushe min sana'a ne.

PAGE 20. LAST FREE PAGE.

Dakan kayan yaji da za su yi miyar dare Salma ke yi a ƙaton turmin tsakar gidan nasu wanda marigayiya matar Malam Jamilu ta yi dakan furar sayarwa a ciki. Gaba ɗaya taɓaryar ta yi wa Salma nauyi da tsawo,a haka ta jure ta ke ta faman daka duk ta haɗa zufa;Samira na yi mata faɗan sanyin jiki da take da shi. Salma na gamawa ta duƙa ta kwashe kayan yajin ta nufi madafi da shi ta buɗe tukunyar dake kan wuta ta zuba. A gajiye ta shiga ɗakin Samira dake hango duk abinda take yi a tsakar gidan ta durƙusa har ƙasa ta ce.

"Yah Samira na gama,akwai abinda zan yi miki?"

Shiru Samira ta yi ta na wani nazari,a cikin ranta ta ce.

'Ya kamata fa na karɓi abinda zan bayar a sunan Hauwa a wajen yarinyar nan,tinda ita ce sabuwar amarya,na tabbata idan na sauka lafiya nima za su rama wa kura aniyarta.'

Muryar Salma ce ta katse ta daga tunanin da ta faÉ—a ta ce.

"Yah Samira miyar na kumfa me zan zuba?"

"Ki je ki buɗe murfin tukunyar ki saɓa bakin. Yauwa idan kin gama mu je ƙofarki ki buɗe min lefen ki akwai abinda zan ɗauka na kai wa Hauwa na barkatu."

"To Yah Samira."

Cike da ladabi Salma ta je ta saɓa bakin tukunyar kamar yanda Samira ta umarce ta,daga nan sai ta wuce sashenta ita da Samira,su na shiga Samira ta hau leƙe da dube-dube ko za ta ga wani abun da za ta yi faɗa akai ko ta ɗauke. Har uwar ɗaka suka shiga tare,da ƙyar Salma ta iya sakko da akwatunan ƙasa Samira na kallon ta;amma ta ƙi taimaka mata. Ta na saukewa Samira ta zauna a gaban kayan tana ɗagawa,tsabar son zuciya ji take yi da da hali da ta kwashe kayan dika,domin Malam Jamilu bai kashe mata kuɗi kamar yanda aka kashe wa Salma ba. Hannunta ta ɗora akan wata santaleliyar atampa mai kyau,da dikkan alamu ita ce ma mai babban kuɗi a cikin kayan. Turare da breziya Samira ta sake ɗauka sannan ta miƙe tsaye ta ce.

"Maza ki kwashe su ki mayar da su mazaunin su. Ki buɗe kunnen ki da kyau ki ji ni,ko sama da ƙasa za ta haɗe idan an tambaye ki inda atampa take ki ce baki sani ba,idan kika faɗi suna na sai na sa gabanki gabar na yanke da wuƙa. Shegiya mai ido kamar na mage."

Kan Salma ta dangwara sannan ta ɗaga rigarta ta soke atampar da turaren tare da breziya ta fita da sauri. Kai tsaye ɗakinta ta nufa ta cire kayan daga cikinta ta samu leda babba ta saka kayan ta ɓoye. Murna ta dinga yi domin ta samu hanya mafi sauƙi da za ta dinga bada kayan barkatu ba tare da sisinta ya yi ciwo ba.

A wannan azaba da uƙubar Salma ta yi wata biyu a gidan Malam Rabi'u. Watarana da daddare Malam Rabi'u da Salma su na zaune yana jefa lomar tuwon da Salma ta tabbatar masa cewa da kanta ta dafa masa. Murmushi ya yi ya kalle ta ya ce.

"Inyeee an Salamemen Gwaggo hannu yana ta faɗawa. To ga wannan ki sayi sha ka laɓe ki sha abunki."

Hannu ya saka a aljihunsa ya zaro nera É—ari sabuwa kar ya bata. Murna Salma ta dinga yi ta na yi masa godiya. A hankali Malam Rabi'u ya tsaya yana kallon ta shi ma yana murmushi, sai dai bai jima yana murmushi ba fuskarsa ta koma ta jimami,cike da kulawa ya kalli Salma ya ce.

"Salma ko dai akwai abinda yake damunki ne a gidan nan da baki sanar da ni ba? Gaba ɗaya kin rame kin yi baƙi kamar ba ke ba,ni kuma na san ina bakin ƙoƙarin na ga na kawo miki duk wani abu na jin daɗin rayuwa,domin a yanzu na yarda na amince bani da wata ko wani da ya dace da ya ci dukiyata da nake ta tarawa da ya wuce ki. Ki na da hankali,natsuwa da tarbiyya,ki na da kawaici da juriya akan halin da kike ciki,shin ko dai har yanzu ba kya so na ne na mayar dake wajen Gwaggo na haƙura da auren? A ƙalla dai duk wanda ya kalle ni zai tuna cewa na taɓa yin aure a rayuwata ko sau ɗaya ne."

Tinda Malam Rabi'u ya fara magana jikin Salma ya yi laushi idanuwanta ke zubar da hawaye. Tsabar azabar da Samira ke gana mata ko sunan ta aka kira sai gabanta ya faɗi ta zaci na Samiran aka kira. Ganin hawaye na zarya a kuncinta ne ya sanya Malam Rabi'u kiranta wajensa. Babu musu ta tashi ta isa gare shi ta zauna a saman cinyarsa kamar yanda ya fara sabar mata. Ba dan yana jin wata sha'awa ba haka kawai yake jin daɗi idan Salma ta zauna a jikinsa,ya na ƙaunarta sosai saboda natsuwarta da kamewarta,bata da hayaniya da kwaramniya irin ta yara. Cike da sigar lallashi ya ce.

"Sanar da ni abinda kike so Salamatuna. Ko akwai abinda yake damunki?"

Kai ta girgiza masa alamar babu komai,sake tambayarta ya yi a karo na babu adadi,da ƙyar ta iya buɗe baki ta ce.

"Ina so na ga Gwaggona. Tinda na zo gidan nan sau ɗaya ta zo ta kawo min kayana,ni kuma ban samu damar zuwa na ganta ba. Kuma ina son ganin Aabid,Aunty Layuzah ta yi min alƙawarin za ta zo yawon arba'in Kura amma bata zo ba gashi har sun yi wata uku zuwa huɗu."

Murmushi Malam Rabi'u ya saki,bai san dalili ba sai zuciyarsa ta ji daɗi da Salma bata ambato matsala a zaman su tare ba,duk damuwarta mai sauƙi ce a wajensa. Kanta ya shafa sannan ya ce.

"In dai wannan ne matsalar ki to ki shirya a daren nan zan kai ki wajen Gwaggo ba zan bari ki kwana baku gana ba. Wajen Aabid kuwa ki yi haƙuri ki ƙara ko da wata guda ne sai na kai ki,dan kin san al'adar garin nan amare ba sa yawo idan basu cika shekara ba. To mu dai za mu fara take doka daga yau ko?"

Bakinta ta rufe ta na dariya cike da ƙuruciya. Shi ma dariyar ya taya ta,daga ƙarshe ya ƙarasa cin tuwonsa ya na bata a baki har suka cinye. Salma ce ta kwashe kwanukan ta kai waje,ta na fita ta ji kamar an ruga da gudu an bar sashen nata,ta ji tsoro sosai a ranta,amma kuma ta tabbata ko ma wanene ba zai wuce Yah Samira ba,dan ba sau ɗaya ko sau biyu ta kama ta tana yi musu laɓe ba. Hannunta da bakinta ta wanke ta koma ɗakin. Malam Rabi'u kuwa sai da ya zaga bayi sannan ya wanke bakinsa ya kulle ko ina ya miƙa wa Salma sabon hijabi da takalmi ya ce.

"To bismillah amaryar Malam Rabi'u mu je ko?"

Bakinta ta toshe tana dariya ta yi gaba yana biye da ita. A haka suka isa har gidan Malam Bala. Malam Bala dake ƙoƙarin shiga gida ne ya ga Malam Rabi'u tafe da Salma su na hira a cikin hasken farin watan da ya mamaye ilahirin garin Kura. Sam ransa bai yi masa daɗi ba da ya gan su cikin nishaɗi. Sai ya kawar da kai ya yi kamar be gansu ba zai shige gidan. Cikin sauri Malam Rabi'u ya kira sunansa,washe baki Malam Bala ya yi yana fara'a kamar babu abinda ke damun zuciyarsa. A ɗarare Salma ta durƙusa ta gaishe shi,haɗe fuska ya yi ya ce.

"Ince dai Ja'irar yarinyar nan ba wani mugun abun ta gunguma ba ka dawo da ita gida? Ina so ki sani muddin kika kaso auren nan ba dai gida na ba,sai dai ki nemi inda za ki je."

Da sauri Malam Rabi'u ya tari numfashin Malam Bala ya ce.

"Allah na tuba me wannan halitta mai tsarkin za ta yi min na ɓacin rai? Yarinya kamar ba a cikin shekarun biri take ba. To ka ganta nan da zan ce mata ta haɗiye min ruwa in ji ƙoshi a cikina za ta yi tsabar yanda take yi min biyayya. Gwaggonta na kawo ta ta gani,ka san abun yaro sai ana lallaɓa shi."

Ƙwafa Malam Bala ya yi ya saki yaƙe ya ce.

"Maza ki tashi ki shiga ciki,kuma kada ki jima,tinda sarai kun sani ai mace bata fita daga gidan miji sai ta shekara,wata ma sai ta haihu idan za ta je wankan gida take zuwa gida ita da abinda ta haifa."

Da sauri Salma ta miƙe tsaye ta shige cikin gida cike da murna. Malam Rabi'u kuwa sai ya tuntsire da dariya yace.
Chapter 29 · 0% Book details