← Book details Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 30

Sashe 7

Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ni dai da za ki yi haƙuri a bar yaron nan haka Aabidah da ya fi. Me kike so ne ki mallaka daga gare shi wanda baki gama mallaka ba? Baki da kishiya a yanzu,kin raba shi da iyayensa da danginsa,ma'aikatansa ma sai wanda kika so yake hulɗa da su,kin raba shi da abokansa,ke mai aiki wannan baki da ita a gidanki shi yake yi miki komai,tsabar ƙulumboto da neman asiri babu inda bamu je ba,daga nan ƙasar hausa har ta yarabawa sai da muka taka da ta fulani. Ka da fa ki manta har Akwa'ibom garin inyamurai sai da muka ratsa aka yi masa mugun ɗauri da gawa mai kimanin shekaru ɗari a duniya saboda auren ku ya zamo mutu ka raba. Ki na da tabbacin za ki kai shekara tamanin ne a duniyar nan ma ballantana ɗari Aabidah?"

A sheƙe Aabidah ke kallon mahaifiyarta da ke roƙarwa Aabid salama a wajen matarsa da yake masifar so kamar ransa. Cike da gatsali da isgili ta ce.

"Innaji kin dai san ko da ke ko babu ke zan nausa duniya na ci gaba da neman asirin da zai kafe min Aabid ya zamo nawa ni kaɗai;ta yanda ko mutuwa na yi ba zai taɓa kallon wata ƴa mace a matsayin mace ba ballantana har ya aure ta ko? Innaji zan shiga ruwa na faɗa wuta sannan na yi ninƙaya a teku na dawwamar da fatalwata a cikin kabarin Aabid domin ko a kushewa bana so mu rabu,ina so mu kasance a tare har a aljannah. Bayan haka kina tunanin duk wannan mugun abun da nake yi a wajen wa na gado su? Ko har kin manta ke wacece? Kishiyoyi goma sha uku cif kika kora a gidan naki mijin,wasu ma fa kashe su kika sa ayi,wasu kin haukata su,wasu sun ɓace ba a san inda suke ba har yau,to shikenan ni daga farawa ta sai a ce na dakata? Sam ba zai yu ba,idan zaki tashi mu je ki tashi kawai."

Waro ido mai aikin Innaji ta yi kafin cikin sauri ta kwashe kayan da take mopping ta bar wajen. Ta na zuwa kitchen ta ajiye bokitin mopping ɗin ta dafe ƙirji ta ce.

"Kai ku ji min ja'irar mata,ta na irin wannan shirkar da manyan arna ke yi amma take tunanin wai a haka za ta shiga aljannah. Hummm maji ma gani ai idan tusa za ta hura wuta."

Aikinta ta ci gaba da yi ta na mamakin yanda su Innaji da ƴaƴanta suke rayuwa kamar basu san kalmar la'ilaha'illallah ba. Ta na tsaka da aikinta ta jiyo Innaji na ƙwala mata kira,da sauri ta saki soson wanke-wanken ta nufi parlourn ta durƙusa har ƙasa. Ta gabanta Aabidah ta shige ta na rausaya ƙugunta da ke a cike da manyan mazaunai da cinyoyi. Muryar Innaji ce ta katse mata hanzari ta ce.

"Sannu sa'idawa masu bacci da ido ɗaya,ana ruwa kuna ƙirgawa,idan kun ga hayaƙi kun san me ake dafawa a maƙota. To ina so ki buɗe kunnenki da kyau ki jini, za mu fita yanzu ki kula da gidan,idan na ji kin shiga maƙota yawon gulma a bakin aikinki,dan ba a kan ki na fara sallamar masu aiki ba,kuma ba a kan ki zan gama ba. Idan waccan gantalalliyar ta dawo ki sa ido kada ta shigar min ɗaki ta yi min sata.shi kuwa wancan shashashan ki ce masa ya jira ni na dawo kada ya sake ya sake sa ƙafa ya bar gidan nan ba da izinina na balle ya sake jawo min magana. Sai na dawo."

Gyaɗa kai kawai Laure ke yi tana amsawa da "To Hajiya,a dawo lafiya." Su na fita Laure ta samu waje ta kame a kujera ta na ƙarasa shanye sauran furar da Hajiya ta bari. Cike da jinjina kafurci irin na su Innaji ta jinjina kai ta ce.

"Wato a ƙiyama ba dan kowa ta kansa yake yi ba,da na roƙi Allah Ya nuna min yanda za a yi wa waɗannan bayi hisabi. Ni yanzu ina ni ina tinkarar wannan da'un na ce masa kada ya sake fita? Ai ni ya fitar min da kaina daga gangar jikina idan ban yi wasa ba,ita kuwa wannan kinfi karuwar taɓargaza ta zo ta yi duk abinda taso babu ruwan Laure,ita da gidan ubanta meye nawa a ciki? Ke kanki Hajiya ba jin maganarki suke yi ba balle wata Laure ƴar aiki. Mtswww."

A ɓangaren su Aabida kuwa suna fita kai tsaye hanyar barin cikin garin Kano suka ɗauka. Kasancewar ta kwana biyu bata je wajen bokan nata da ke yi mata aiki ba,gashi a kwana biyun tana yawan fama da mafarkan da bata gane kansu,shi yasa take so su koma ya bincika mata goben ta ya ga me yake shirin tunkaro rayuwarta......

MUGUWAR MACE.

NA : HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️

*Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.*

*Slimming Tea 6k.*
*Slimming oil 3500.*
*Body scrub 3500.*
*Skin oil 2500.*
*Location Kano.*
*Phone No 09031416423.*

PAGE 6.

A bakin ƙofar gidan boka Aabidah ta tsayar da motarta sannan ta sake fesa turare a jikinta,dariya sosai Innaji ta hau yi dan ta san dalilin da ya sa Aabidah ke fesa turare. Harara Aabidah ta banka mata,sai ta saka hannu ta zuge bakinta ta yafa mayafinta ta fice daga motar tana ci gaba da dariya. Itan ma dariyar ta yi sannan ta yafa mayafinta a kafaɗa ta ɗauki jakarta da wayoyinta ta fita. Kulle motarta ta yi sannan suka shiga gidan bokan ba tare da sallama ba. Zaune suka tarar da shi ya na ta yin wasu abubuwa kamar mai ciwon farfaɗiya. Ya jima a haka kafin ya dawo hayyacinsa yana sharce zufa. Wani ɗaki ya shige su Innaji suka bishi ba tare da kowa ya tanka wa ɗan'uwansa ba.  Su na shiga suka tarar da bokan ya tanƙwashe ƙafa jan ƙallen dake jikinsa ya rufe masa iya gabansa,jikinsa ya rabu da ƙasa kamar wanda yake zaune a saman iska. Jajayen idanuwansa da ke a kulle ya buɗe ya zuba wa Aabidah su kamar zai fasa jikinta ya hango zuciyarta. Ba tare da jin tsoro ba Innaji da Aabidah suka fara yi wa bokan nasu da suka yi matuƙar imanin in dai yana raye babu su babu jin kunya kirari. Sun jima suna jinjina masa akan mugayen ayyukan da yake yi musu kafin ya ɗaga musu jelar damisar dake hannunsa yayi musu nuni da wasu ƙwarya guda biyu. Da baya da baya suka isa wajen ƙwaryar suka zauna kamar yanda suka saba. Ido ya kulle ya hau yin surkulle kafin daga baya yayi shiru. Su na jin yayi shiru suka miƙe tsaye daga saman ƙwaryar kowaccensu ta kafe ƙwaryar da ta zauna akai da ido. A gaban idanuwansu ƙwaryar farko wato wadda Innaji ta zauna ta buɗe kanta ta isa gaban boka ta tsaya a saman iska kamar yanda yayi. Kallon ƙwaryar yayi sosai sannan ƙwaryar ta juya kanta tana fuskantar Innaji. Cikin wata iriyar murya mara daɗin sauraro boka ya kalli Innaji ya ce.

"Da alama yaranki bana sun yi nisan kiwo,saƙon da kika bayar a basu zai jima bai isa kunnuwansu ba."

Tagumi ta zabga tana jin wani irin zafi a cikin ranta. Sosai take son ƴaƴanta bata son abinda zai taɓa rayuwarsu, shi yasa a koda yaushe take ta faɗi tashi dan ganin ta inganta musu rayuwarsu ko ta halin ƙaƙa,sai gashi rayuwar Aabidah ce kawai ta inganta a cikinsu har suka raɓu da ita suke yin walwala, Junaid da Jauhara a kullum cikin ɗakko mata magana suke. Hannu ta sanya a jakarta ta lalubo kuɗi ta jefa a cikin ƙwaryar ta koma gefe tana matsar ƙwalla. Kafin ta gama daidaita tsayuwarta ƙwaryar da Aabidah ta zauna ta buɗe kanta ta isa gaban Boka ta tsaya,ya jima sosai yana kallon ƙwaryar kafin ƙwaryar ta koma gaban Aabidah ta tsaya,shiru ta yi tana kallon ƙwaryar cike da rashin fahimta. Kai Boka ya jinjina mata sannan ya ce.

"Ƙwarai da gaske. Ni ma abinda ke damu na kenan a cikin ƴan kwanakin nan game da aikin ki Aabidah. Na rasa gane dalilin da ya sa idan dai wannan mutumin ya shiga cikin aikinmu bama ganin komai sai wannan hasken mai kashe idanu. A yau ina so na baki shawara ba wai dan na gaza a aiki na ba;sai dan kawai ina so kema ki yi wani yunƙurin da zai taimaka mana ta ɓangaren ki,ina so ku sani ba koda yaushe ne ake dogara da sihiri ba. Ina so daga yau ki jawo wannan mutumin jikinki ba da tirsasawa ba ya amince ya dinga zuwa gidanki da kansa,sauran bayanin zan yi miki shi daga baya. Ke dai abinda zaki yi kawai shine ki tabbata kin gama naki ɓangaren."

"Ya kai babban Boka...."

"Kada ki ce komai,domin wannan na daga cikin fassarar mafarkanki. Ki je ki yi naki ɓangaren ni ma zan ci gaba da yin nawa ɓangaren kamar yanda na saba."
Chapter 7 · 0% Book details