Sashe 15
Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Amin abokina. Allah Ya sa hanyar arziƙinmu ne baki ɗaya,domin da alama ba zan iya kasuwancin nan ba idan babu kai a gefe na. Na gode sosai da wannan taimakon da ka yi min,Allah Ya jiƙan Innah da Abbah."
"Amin Ya Allah,kai ma Allah Ya jiƙan Baaba da Baba."
Zama suka yi suka ƙirga kuɗi suka ware riba da jari. Su na kammalawa suka adana kuɗin da kyau sannan suka ci gaba da shawarwarin yanda za su dinga samun kuɗi ta hanyar halal domin biyan kuɗin makarantarsu da kuma buƙatunsu na yau da gobe.
Tin daga wannan ranar kasuwa ta buɗe wa Abdulwahab ya ke samun kuɗaɗen kashe buƙatunsa. A wannan gaɓar ya dinga amfani da ilimin da ya ke koya ta ɓangaren kasuwanci ya dinga bunƙasa kasuwancinsa. Ana haka sai aka samu ƴan gulmar da suka kai gulmar Abdulwahab da Mudassir wajen hukumar makaranta akan sun mayar da hostel wajen sana'ar sayar da hatsi,da fari an yi musu gargaɗi,sai dai hakan bai yi wa duk wanda ya kai gulmar daɗi ba,bai huta ba har sai da aka kore su daga hostel ɗin gaba ɗaya.
Ana korar su suka kama hayar shago a wajen makaranta,a nan suke kwana kuma suke siyar da kayan hatsinsu. Sai ya zamana bayan ƴan makaranta da suka san suna siyar da kayan hatsi akan farashi mai arha har mutanen gari ma suna zuwa siyan kayan hatsi a wajen su Abdulwahab. A hankali kasuwa ta fara buɗe masa sosai tin yana ɗakko buhunan hatsi guda uku,ya koma biyar,daga baya ya koma ya na sauke buhuna goma. Wani lokacin ma mota zuwa take yi har gaban shagon ta sauke kayan ta wuce,ganin kayan na ƙaruwa kuma basu da wajen ajiya;sai Mudassir ya ba wa Abdulwahab shawarar ya kama wani shagon ya zauna a matsayin store,idan ya so wannan da kowa ya san su da shi sai ya zama na siyar da kayan hatsin. Da hidima ta ƙaru akansu sai Abdulwahab ya samu yara guda biyu masu kular masa da shagon,shi kuma da abokinsa sai suka mayar da hankalinsu akan karatunsu.
Da haka Abdulwahab da Mudassir suka samu suka kammala karatunsu,domin daga ƙarshe Abdulwahab shi ya ci gaba da ɗaukan nauyin karatun Mudassir. Sosai Malam Bala ya yi mamakin yanda Allah Ya sanya wa kasuwancin Abdulwahab albarka. Tin daga wannan lokacin sai ya rage matsanta masa da yake yi,domin har kyautar kuɗi Abdulwahab ɗin yake bashi da kuma yi wa iyalansa hidima domin kyautatawa. Ana haka Salma ta isa sawa a makaranta, Abdulwahab da kansa ya ɗauke ta ya kai ta makarantar boko da islamiyya ya yi mata register sannan ya kai ta wajen siyar da yadin uniform ya siya mata wanda zai isa a yi mata har kala uku-uku. Daga nan ya kai ta wajen masu siyar da jaka da takalmi ya zabar mata masu kyau da ƙwari,sai suka wuce shago ya yi mata ƴar siyayyar ƙwalama irin ta yara suka koma gida. Ko da suka koma gida suka sanar da Malam Bala ya so ya turje ya ƙi amincewa da zuwan Salma makaranta. Sai Gwaggo Kande ta murzawa idonta toka ta ce sam bai isa ba. Kan dole ya haƙura ya fita ya bar gidan ya na sababin sisinsa ba zai yi ciwon kai ba a zuwan yarinyar mace mai ƙaranci lokaci a rayuwarta makaranta. Cike da sababi Gwaggo Kande ta ce.
"Shi ma ɗan'uwanta da kansa ya ƙarasa biya wa kansa kuɗin makarantar,tinda kai ka ce ladan ya ishe ka ka biye wa zigar abokan banza ka janye daga biya masa."
Da ƙyar Abdulwahab ya taushe ta ta bar sababi,ya zauna suka hau hirar yaushe gamo. Su na tsaka da hirar ne Gwaggo Kande ta ce.
"To yanzu tinda an gama makaranta sai kuma a zo a yi aure ko? Ka ga shikenan sai ka rushe tsohon gidan iyayenka a siyar da filin Babanku ɗaya ko biyu kai ko dika ukun ma;ka danƙara gininka ku zauna daga kai sai matarka."
Da jin haka ƴar gidan kishiyar Gwaggo Kande mai suna Suwaiba da ke gaban murhu tana iza wutar kalwa da mahaifiyarta ke siyarwa ta tashi ta na wata tafiya ta na karairaya kamar maburgi ta wuce ta gabansu. Kai tsaye ɗakin mahaifiyarta ta shiga ta saka mata kuka tana sake yi mata tuni akan batun soyayyar da ta jima ta na yi wa Abdulwahab. Haƙuri ta bata tare da yi mata alƙawarin a daren nan za ta shawo kan mahaifinta dan ya ƙulla aurenta da Abdulwahab ko yana so ko baya so,tinda ya isa da shi. Da jin haka sai Suwaiba ta hau murna ta fito daga ɗakin ta na yanga ta wuce ta gaban su Abdulwahab ta ci gaba da sauraron hirarsu;wadda ta kasance duk ta samun nasarorin da yake ta yi ne akan kasuwancinsa. Albarka Gwaggo Kande ta dinga saka masa sannan ta tashi Salma da ta fara bacci ta ce ta je ta yi alwala dan an kusan kiran sallar magariba.
Bayan Abdulwahab ya koma gidan iyayensa inda yake kwana ne ya kwanta ya na nazarin maganar da suka tattauna da Gwaggo Kande. Murmushi ya saki mai laushi sannan ya cire rigarsa ya rataye ya fita zuwa makewayi. Ya na fitowa ana kiran magariba,sai kawai ya ɗaura alwala ya koma ɗaki ya saka kaya ya kulle ɗakin ya fita zuwa masallaci. A can masallacin ya dinga haɗuwa da abokan mahaifinsa suna gaisawa,da sun gama gaisawa sai su ce za su masa nasiha akan saka Salma makarantar boko da zai yi. Ina laifin ya ƙyale ta tinda ita mace ce;ta na bin yaran Malam Bala zuwa gona itama ta na taimaka wa da wasu abubuwan,lokacin aurenta na yi Malam Bala ne zai tsaya mata ya samar mata da miji ɗan gaske ya aurar da ita,a cewar su rayuwar ƴa mace bata da tsayi. Da sun gama koro wa Abdulwahab jawabi yake bin su da murmushin nan nasa da suke kira na rainin wayo,ko murmushin ajali. Da takaicin yamaɗiɗin da Malam Bala ya yi masa ya koma gida,domin a ganinsa ko auren Salma ne ya tashi ai suna da dangin uban da za su karɓa mata aure,ko Ƴan'uwan mahaifiyarsu,Malam Bala mijin Goggwan mahaifiyarsu ne shi kawai wanda yake ruƙon ƙanwarsa.
Ya na komawa sai ya tarar da Suwaiba ta kai masa abincinsa ta na jiransa a ƙofar gida ta sha ado da irin kwalliyar ƴan matan ƙauye sai karairaya take yi. Ya na zuwa ta kashe murya ta durƙusa har ƙasa ta gaishe shi sannan ta miƙa masa kwanon abincin ta na wani sunne kai. Dariya ta bashi sosai,sai ya kawar da kai ya na murmushi,da ganin haka sai Suwaiba ta kwasa da gudu ta yi gida, zuciyarta cike da farincikin Abdulwahab ya kamu da ƙaunarta. Tinda ta koma gida take bawa Innarta labarin irin murmushin da Abdulwahab ya yi mata har Babansu ya dawo daga majalisa ya shige turakarsa.
Da yake Innar Suwaiba ke da girki,sai ta tashi ta nufi ɗakin nasa inda ta ajiye masa duk wani abun buƙata ta zauna. Mafifici ta ɗauka ta hau yi wa Malam Bala firfita. Baki ya kyaɓe ya ce.
"Da dai Kande ce ke yi min firfitar nan da na ce Allah Ya yi mata albarka. Dan ita ba ta yi min biyayyar son zuciya ko ta wata manufa. Dan haka ina jinki, faɗi buƙatarki na ji ki ƙara gaba."
Tura É—ankwali ta yi gaba ta na fari da ido ta ce.
"Ka dai ji da shi Malam,ni ba zan biye maka ba a cikin daren nan da na ƙunso abun alkhairi a baki na mu yi faɗa da kai. Dan haka ka karkaɗe kunnuwanka ka kuma bani hankalinka nan dan jin abinda nake tafe da shi."
Hannu Malam Bala ya siÉ—e ya na mai ture kwanon tuwon gefe ya kalli Innar Suwaiba ya ce.
"Ikon Allah! Ke kuwa wanne irin abun alkhairi ne haka ya risinar min da ke?"
Sai da ta yi ƙasa da muryarta sannan ta ce.
"Malam bana dai Suwaibar mu an yi miji,irin mijin da kake nema,mai kuɗi wanda zai dinga miƙo wa ba wanda zai siyi akuya ta dawo ta na ci maka danga ba."
Baki Malam Bala ya washe ya kalli matar tasa ya ce.
"Ke ki bari dan manzo? Shi kuwa wannan surukin nawa a ina yake?"
Dariya Innar Suwaiba ta yi cike da jin kunya ta ce.
"Ai abun ƴar gida ce Malam. Tuwona mai na za a yi. Wato dakan ɗaka shiƙar ɗaka tankaɗen bakin gado ba."
"Ke ni ki yi sauri ki sanar da ni ɗan wanne gida ne a kaf ƙauyen nan na ji ko ubansa na da arziƙin da zan iya bawa ɗansa auren ƴa ta."
"Malam ba fa wani bane face Abdulwahabu É—an gidan marigayiya Atine ta Malam Musa Manomi."......
MUGUWAR MACE.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨âœï¸
*Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarÆ™aÆ™iyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman duniya. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k É—inki ta wannan account É—in 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel É—in nan ne da niyyar ki yaÉ—a shi a group É—in da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haÆ™uri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaÉ—a kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨âœï¸
PAGE 12.
Ganin irin kallon da Malam Bala ke yi mata ne ya sanya ta muskutawa kusa da shi ta yi ƙasa da muryarta ta ce.
"Malam kada ka ce komai game da wannan maganar,kai dai kawai ka saka wa lamarin nan albarka. Ko ka manta yanda haihuwar yaron nan ta zamo silar arziƙin ubansa kafin ya bar duniya? Sannan ka duba ka ga yanda arziƙi ke shigo masa ko ta ina daga fara sana'ar saye da siyarwar hatsi. Na tabbata nan gaba sai ya fi haka arziƙi domin da dikkan alamu ya na da ƙashin arziƙi. Idan aka ce wannan yarinyar kuwa ta aure shi ai ba ita da take a matsayin matarsa ba;mu kammu iyayenta sai mun huta."