Sashe 19
Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Au haka ne? Dama duk ƙarya kike zuba min da kike cewa ba kya son in dinga yin nisa da ke? To ai shikenan,Aboki ni fa daga yanzu na koma ɓangaren zirga-zirgar ƙasa da ƙasa."
Dariya sosai suka yi gaba ɗayansu,sannan suka ci gaba da hira mai cike da nishaɗi da barkwanci. A wannan ranar basu rabu da junansu ba sai misalin sha ɗaya da rabi na dare. A daren kuma Ammabuwa ta haɗa wa Mudassir kaya a ƴar ƙaramar jaka ta saka masa duk abinda zai buƙata. Sannan suka kwanta suka raya daren nasu cike da soyayya.
Washegari ana idar da sallar asuba Malam Sallau ya zo da tawagar da za su yi tafiyar a mota. Sallama Mudassir ya yi wa su Ammabuwa da Layuzah dake riƙe da Maheer da ya tashi tun asuba bai koma bacci ba,banda kuka babu abinda yake yi. Su na gama sallama ya bi Abdulwahab suka tsaya a zaure ya bashi wasu ƴan kuɗaɗen da zai yi amfani da su ko da buƙatar hakan ta taso. Rungume junansu suka yi sannan suka yi musabaha hannunsu na riƙe da na junansu Mudassir ya shiga mota yana ɗaga wa Amininsa hannu........
MUGUWAR MACE.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨âœï¸
*Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarÆ™aÆ™iyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman duniya. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k É—inki ta wannan account É—in 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel É—in nan ne da niyyar ki yaÉ—a shi a group É—in da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haÆ™uri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaÉ—a kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨âœï¸
PAGE 14.
Zuwan Mudassir ƙasar Ghana ya sanya idamuwansa sake buɗewa akan kasuwanci ƙwarai da gaske. Lokacin da za su dawo gida Nigeria bai yi shawara da kowa ba ya saro wasu daga abubuwan da suke da shi a can wanda mutanenmu na Nigeria ke da buƙata suka kamo hanya da sauran yaran Abdulwahab suka dawo. A wannan lokacin ne ɗaya daga cikin yaran Abdulwahab mai suna Iliya ya kai masa gulmar yanda Mudassir ya dinga facaka da dukiyarsa a Ghana. Nan take shaiɗan ya yi uwa ya yi makarɓiya ya dasa wa Abdulwahab wani ƙulli a cikin zuciyarsa game da aminin nasa kuma Yaya ga matarsa. Tin daga wannan ranar alaƙarsu ta fara sauyawa,sai ya zamana kafin Abdulwahab ya kira Mudassir sau ɗaya ya kira Iliya sau biyar. Mudassir na kula da hakan sai ya ja baya ya koma yin ayyukan da ba lallai ne sai ya nemi izinin Abdulwahab ba,sannan ya kame bakinsa bai sanar da matarsa ko ƙanwarsa sauyin da yake gani a tattare da abokin nasa ba.
Sosai Mudassir ya kai zuciyarsa nesa game da yanda Abdulwahab ya dinga ɗaure masa fuska da nuna masa iyakarsa,sai Mudassir ya nuna sam bai ma gane abinda yake yi ba,harkar gabansa kawai ya sa a gaba tare da ƙoƙarin kawo cigaba a cikin kasuwancin da suka sha wahala wajen ginawa. A hankali Malam Sallau ya kula da abinda ke faruwa a tsakanin aminan junan. A matsayinsa na amintaccen yaron Abdulwahab sai ya tsaya ya tsananta bincike akan lamarin,babu jimawa kuwa ya gano abinda ke faruwa. Ba tare da sanin kowa ba ya ɗana wa matashin dake son ya ture Mudassir daga rayuwar Abdulwahab shi ya kafa tashi kujerar tarko.
Watarana Malam Sallau ya karɓo takardun wasu filaye da ya siyo wa Abdulwahab sai ya je shago ya bawa Mudassir a gaban Iliya da mutanen shagon ya ce ya bawa Abdulwahab,babu ɓata lokaci Mudassir ya karɓa ya saka su a cikin jakar da yake zuwa da ita shagon nasu da niyyar idan Abdulwahab ya taso daga aiki ya biyo shago sai ya bashi,idan kuma bai biyo ba in sun je gida sai ya bashi,daga nan sai ya ci gaba da harkar gabansa. Malam Sallau na zaune ya na ta hirarsa amma gaba ɗaya hankalinsa ya na kan Iliya da ke ta kallon mutane ya na zuge jakar Mudassir. A hankali ya zare takardun ya fita daga shagon da sauri ya nufi shagon da suke kwana ya ɓoye,ya na gama ɓoyewa ya dawo ya ci gaba da aikinsa kamar babu abinda ya aikata. Da ganin haka sai zargin da Malam Sallau yake yi akansa ya tabbata. Sai da ya bari an tafi sallar magrib ya shiga shagon su Iliya ya ɗauke takardun. Da dare bayan Abdulwahab ya koma gida Malam Sallau ya je ya bashi labarin duk abinda yake faruwa da kuma hasashen da yake yi akan Iliya. Cike da tsantsar nadama da danasani tare da jin nauyi da kunya Abdulwahab ya ce.
"Bana tamtama akan abinda ka sanar da ni Malam Sallau,amma ina so don Allah ka taimaka mini domin kama Iliya hannu da hannu domin na ji daÉ—in hukunta shi akan abinda ya sa na aikata."
"Yauwaa Alhaji an zo wajen. Ina so gobe da safe a gaban Iliya ka tambayi Malam Mudan takardun nan da na nuna maka,da ka tambaya ka bar min komai a hannuna."
Sallama suka yi da Malam Sallau Abdulwahab ya koma cikin gida cike da nadama,a wannan ranar ya gane cewa lallai matansu sun yi ƙoƙari da suka riƙe zumunci suka ƙi ba wa ƴan gulma damar shiga tsakaninsu. Tunani ya fara yi ta yaya ma har ya bari wani bare zai raba shi da mutumin da ya fara taimaka masa a rayuwa? Duk dukiyar da ya tara yake alfaharin zamowarta tasa da taimakon Mudassir ya tara ta. A wannan daren kasa bacci Abdulwahab ya yi. Asuba na yi ya watsa ruwa ya yi alwala ya tafi masallaci. Bayan an idar da sallah kafin Mudassir ya fito daga masallacin Abdulwahab ya gudu gida,domin kunya yake ji ya haɗa ido da shi ballantana har su yi magana. Ya na kwanciya bacci mai daɗi ya ɗauke shi har Mudassir ya shirya ya samu Layuzah ya tambaye ta ko Abdulwahab ya farka kuwa? Sanar da shi ta yi bai farka ba,dan haka sai ya tafi kasuwa da zummar idan Abdulwahab ya je zai bashi takardun a can.
Abdulwahab na farkawa Layuzah ta sanar da shi zuwan Mudassir,shiru ya yi kamar wanda ruwa ya cinye,gani yake yi kamar kowa ya san abinda ya aikata a gidan. Sai kawai ya É—akko mata zancen zuwan Gwaggo Kande domin ta kula da ita har ranar da za ta haihu. Cike da jin kunya Layuzah ta ce.
"Ni dai gaskiya bana son Gwaggo Kande ta zo ta karɓi haihuwa ta. Dama ina a can Kuran ne idan ta karɓi haihuwar babu komai,amma ina a nan gaskiya ni dai a barta kawai,idan na sauka lafiya sai ta zo ta dinga yi wa jariri wanka."
Murmushi ya yi ya shafa ƙaton cikin nata da suke wa laƙabi da cikin ƴan biyu. Ba tare da ya ce komai ba ya ƙarasa shirin fita ya buga babur ɗinsa ya wuce kasuwa.
Ko da ya isa ya tarar da manyan shagunan nasa guda huɗu dake jere da juna sun ɗauki harami ana ta cinikayya. Shigarsa wajen ke da wuya yaransa suka je suna ta gaishe shi yana amsawa. Malam Sallau dake zaune a gefe ma ya gaishe shi yana kallon Mudassir dake zuwa shagon hannunsa riƙe da jakar bakkonsa da yake saka kayansa a ciki. Ya na zuwa ya fara gaishe da Abdulwahab wanda sai a wannan lokacin ya gane irin sauyawar da ya yi ashe ba kaɗan bace. Su da suke caccafkewa da abokinsa kuma amininsa su zauna a waje ɗaya,yau shi ne Mudassir ke risinawa ya na gaishe shi a ɗarare gudun kada a ce ya yi wani laifin. Nan take ƙwalla ta taru a idanuwansa yana jin kamar ya kurma ihu. Da ƙyar ya danne abinda ke taso masa a rai ya ce.
"Aboki ina takardun da Man Sallau ya baka jiya ka bani."
Cikin rawar jiki Mudassir ya isa gaban Abdulwahab ya na duba jakarsa ya hau neman takardun. Wani irin tausayinsa ne ya kama Abdulwahab. Kafin ya dawo cikin hayyacinsa Iliya ya isa gaban Abdulwahab ya ce.
"Ai Alhaji ba zai iya baka waɗannan takardu ba. Domin kuwa jiya ya zaci na wuce gida sai wani mutum ya zo ya bashi takardun shi kuma mutumin ya bashi maƙudan kuɗaɗe. A nan ne ma na ji shi Malam Mudan ya na cewa ai shi ne silar arziƙinka to shi ma zai je ya kafa kansa ya gaji da wahalta maka."
Salati Mudassir ya yi ya duƙar da kansa sai ga hawaye na zuba daga kwarmin idanuwansa. Ya kasa kare kansa domin bashi da kalaman da zai yi amfani da su ya kare kan nasa. Addu'a ya dinga yi Allah ya kare masa mutuncinsa kada ya ba wa maƙiya damar tozarta shi a gaban amininsa. Iliya na gama zuba miyagun kalamansa a kunnen Abdulwahab ya ji saukar mari ta inda bai taɓa zato ba. Idanu ya zaro waje ya na kallon Abdulwahab da ya miƙe tsaye ya na huci kamar wani zaki. Cikin tsananin ɓacin rai ya ce wa Iliya.
"Ka je na sallame ka daga aiki a ƙarƙashi na,sallama ta har abada Iliya. Sannan ka sani idan har baka nemi tafiya akan abinda ka aikata ba alhakin bawan Allah'n nan da ni kai na ba zai barka ka ji daɗi a rayuwarka ba. Sallau maza ku je da shi ya ɗakko takardun filaye na ya baka ka kawo min,ka karɓe duk wani makullin shago na da yake wajensa. Ga wannan kuɗin sallamar ka ne,domin ba zan riƙe maka haƙƙinka ba."
Kuɗi ya ƙirgo a drawer dake kusa da shi ya miƙa wa Iliya da kunya ta gama baibayewa. Malam Sallau kuwa a gaba ya saka shi suka shiga shagon masu aikin,nan fa Iliya ya hau duba kayansa ya na neman takardun da ya adana a cikin kayan amma bai gani ba. Dariya Malam Sallau ya yi sannan ya zaro su daga aljihunsa ya na kaɗa wa Iliya a gaban fuskarsa ya ce.