← Book details Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 30

Sashe 3

Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin ƙanƙanin lokaci su Aabid suka gama duk abinda ya kawo su suka yi sallama da Alhaji Kabiru suka tafi. Godiya sosai Malam Sallau ya dinga yi kamar zai kwanta wa Aabid a ƙasa. A haka Aabid ya sauke shi a daidai wajen da zai samu mota ya koma gida shi kuma ya wuce gidansu dake cikin unguwar Ɗanladi na Sidin. A waje ya ajiye motarsa ya shiga cikin katafaren gidan nasu wanda da wayonsa mahaifinsa ya siyi gidan a hannun gwamnati ya rushe shi ya sake ƙera kalar wanda yake so. Gida ne da ya amsa sunansa gida mai part biyu da manyan filayen da aka yi shuke-shuken ƴaƴan itatuwa da flowers domin ƙayata wajen. Gefe ɗaya kuma ƙaton waje ne da aka yi kitchen irin na gargajiya tare da ɗakuna uku na masu aiki. Zagaye Aabid ya dinga yi a gidan yana kallon kowanne lungu da saƙo na gidan yana tuna memories masu daɗi da marasa daɗi da suka faru a gidan. A ƙofar wani ɗaki ya tsaya yana bin ƙofar da kallo. Wani irin abu ya ji ya daki zuciyarsa har sai da ya sanya hannu ya dafe ƙirjinsa.

"Dijahna"

Shi ne sunan da ya ambata kafin ya tura ƙofar ya sanya ƙafarsa ta dama a ciki. Nan take hotunan rayuwar da yayi a baya ta hau gilmawa a idanuwansa. Kansa ya ji yana sara masa kamar zai tsage. Babu shiri ya fita daga ɗakin ya ja ƙofar ya rufe. Da sassarfa ya isa ɗakin Hajiya wadda ke kwance ita kaɗai tana firfita. Kallonta yayi fuska a haɗe kamar bai taɓa dariya ba ya ce.

"Ina wannan yarinyar take na ganki ke kaÉ—ai?"

Da sauri Hajiya ta tashi zaune daga kishingiɗar da ta yi ta kalli Aabid cike da so da ƙauna irin na ɗa da mahaifiya. Murmushi ɗauke a saman fuskarta ta ce.

"Salimah? Ta fita samo mana gawayi mu É—an É—ora ruwan koko a samu a karya tinda gari ya waye."

Rintse idonsa yayi yana jin jiri na ɗibansa. Mahaifiyarsa ce fa,matar da ko Custard za ta sha sai ya koma fari fat saboda madarar da take zabga masa,ta saka ta ruwa sannan ta ƙara da ta gari,ita ce yau take neman gawayin da za ta dama koko. Mahaifiyarsa wadda take rayuwa kamar sarauniya komai sai an yi mata saboda dukiya da gatan da mahaifinsa da shi kansa suke bata. Kyaɓe baki yayi sannan ya zaro dubu biyu ya ajiye a nesa da ita ya kurɗa kansa cikin ɗakinta,da wani irin farinciki Hajiyan ta ɗauki dubu biyun tana jin kuɗin kamar dubu ɗari biyu a wajenta,yaushe rabon Aabid ya zo gare ta? Yaushe rabon ta samu arziƙin samun wani abu daga gare shi? Lallai wannan babbar nasara ce a gare ta wadda take fatan watarana komai ya koma kamar yanda yake a baya. Bincike yayi sosai kafin ya samu abinda yake so sannan ya fito yana zufa kamar wanda yayi wani aikin wahalar. Kai tsaye ya fice ya bar gidan ba tare da ya ce mata kanzil ba ya faɗa motarsa ya fige ta. A hanya ya haɗu da Salimah hannunta riƙe da tarkacen itacen da ta yo da kanta saboda rashin samun gawayin da bata yi ba. A gabanta ya tsayar da motarsa ya kalle ta ya ce.

"Ke wannan yayin haukan da kika É—ebo fa na meye?"

Cike da jin tsoronsa bakinta ya hau rawa,tsawa ya daka mata tare da sake tambayarta abinda ke hannunta na meye. Cikin rawar murya ta kalle shi ta ce.

"Ƙirare ne na samo dan mu yi amfani da shi."

"Ina gawayin da kika je siyowa?"

"Ban samo ba."

Tsaki ya ja mai tsawo sannan ya ja motarsa ya bar wajen a guje kamar zai tashi sama. A hankali ta waiga ta kalli ƙurar da motar ke tadawa sannan ta girgiza kanta ta wuce gida.

Washegari da sassafe ko tashi daga bacci su Hajiya basu yi ba suka ji ana buga gate ɗin gidan nasu da ko arziƙin mai gadi babu. Hajiya da kanta ta sanya mayafinta ta nufi ƙofar gidan da makulli a hannunta tana tambayar waye. Wata murya ta ji wadda bata waye da ita ba tana faɗin.

"Mu ne."

Gabanta ne ya faɗi har sai da ta dafe ƙirjinta kafin ta ce.

"Ku su wa?"

"Alhaji Aabid bai sanar da ke zuwan mu ba ne? Ina ga zai fi kyau ki kira sa a waya ki tambaye sa su waye za su zo war haka."

Cike da jarumta Hajiya ta buɗe ƙaramar ƙofar gidan ta tsaya tana kallon mutanen da bata taɓa gani ba sai a wannan ranar. A guje Malam Sallau da ya tsaya bawali ya ƙaraso yana gyara wandonsa tare da fyace majina ya ce.

"Barka da safiya Hajjaju."

Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke sannan ta É—an yi dariya ta ce.

"Malam Sallau ai har na ji tsoro,ashe ku ne ke tafe. Bismillah ku shigo."

Da jin haka sai suka ɗunguma suka shiga cikin gidan gaba ɗaya su na sake gaisawa. Alhaji Kabiru Mai Tumbin Nera kuwa kallon gidan yake yi yana girgiza kai tare da washe baki. Tafe yake yana buɗe duk wani ɗaki ko ƙofa da ya gani kamar gidansa. Cike da mamaki Hajiya ta ke kallon ikon Allah,ba ta katse da lamarin Alhaji Kabiru ba har sai da ta ga ya nufi ɗakinta ya saka hannu zai buɗe ƙofa. Da ƙarfi ta ce.

"Malam lafiya wai naga kana ta buɗe min ƙofofin gida kana kalle-kalle?"

Malam Sallau ne ya sosa ƙeya sannan ya ce.

"Hajiya wai ko dai kina nufin Alhaji Aabid bai sanar dake abinda ke faruwa bane?"

Cike da mamaki Hajiya ta juya tana kallon Malam Sallau sannan ta ce.

"Malam Sallau me ya samu É—ana? Me yake faruwa wanda ba a sanar dani ba?"

"Baki da labarin Alhaji Aabid ya siyar da wannan gidan Hajiya? Ai jiya da yamma ya kai wa Alhaji Kabiru takardu muka je wajen Mai Unguwa aka saka shaidu ya biya kuÉ—i da ..."

Wani irin duhu ne ya mamaye ganin Hajiya,nan take ta yanke jiki ta faÉ—i. Alhaji Kabiru na ganin haka ya hau sauri yana son barin gidan,domin shi mutum ne mai tsananin tsoro da kiyaye duk wani abu da zai haÉ—a shi da hukuma. Banda nishi babu abinda yake yi a haka ya isa waje ya shige motarsa ya zauna yana yarfe zufa.

Sallau kuwa sunan Salimah ya dinga kira ta fito a gigice kanta babu ko ɗanƙwali. Ganin Hajiya a zube a ƙasa ne ya gigitata ta nufi wajen da gudu ta zube a gefen Hajiyan tana jijjiga ta. Hankalin Sallau ba ƙaramin tashi yayi ba dan haka sai ya miƙe ya lalubo wayarsa ya dannawa Aabid kira. Cikin rashin sa'a kiran ya shiga a daidai lokacin da wayar Aabid ɗin take hannun Aabida tana duba mutanen da yayi waya da su a jiya;wanda murnar ganin gingimemen alert ɗin kuɗi ya mantar da ita dubawa. Ɗauka ta yi cike da gadara. A kiɗime Malam Sallau ya labarta mata abinda ke faruwa. Rai a ɓace Aabida ta ce.

"Idan ta faɗi mutuwa ta yi? Malam idan za ku yayyafa mata ruwa ta tashi ku yayyafa mata,idan ba za ku yayyafa mata ba ku kuka sani ku barta ta ƙarasa ai dama ta kwana biyu,babu inda mijina zai fito da sanyin safiyar nan yana hutawa."

Tana gama magana ta katse wayar ta ci gaba da abinda take yi..........

MUGUWAR MACE.

NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH. ✨✍️

*Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.*

*Slimming Tea 6k.*
*Slimming oil 3500.*
*Body scrub 3500.*
*Skin oil 2500.*
*Location Kano.*
*Phone No 09031416423.*

PAGE 3.

A rikice Malam Sallau ya kira Yah Maheer ya sanar da shi abinda ke faruwa. Hankali tashe Yah Maheer ya roƙi Malam Sallau da ya nemo abun hawa ya kai Hajiya asibiti ya na nan tafe zai same su a can. Da ƙyar Malam Sallau ya iya barin Hajiya a kwance a ƙasa ya fita saboda tsoron kada ta mutu kafin ya dawo.

Sai da ya É—auki kimanin mintuna shida kafin ya dawo da É—an sahu,su biyu suka É—auki Hajiya suka saka ta a adaidaita sahun sannan suka ja suka tafi asibitin da ake duba Hajiyan a duk lokacin da ciwon ta ya tashi. Su na zuwa likitansu ya fara bata taimakon gaggawa. Kafin Yah Maheer ya iso Hajiya ta dawo tana numfashi yanda ya kamata,sai dai a wannan lokacin bata san wanda yake kanta ba. Har ofishin likita ya je suka zauna,likita yayi ta masa faÉ—a akan yanda suke wasa da lafiyar Hajiyan. Cike da rashin jin daÉ—in lamarin likita ya ce.

"Haba Maheer wai me yake faruwa ne kuke wasa da lafiyar Hajiya haka? Ko ka san cewa tashin ta lafiya ba tare da shanyewar ɓarin jiki ba babban lamari ne da za a gode wa Allah akai? Ina Aabid? Ta na farfaɗowa sunansa ta fara kira. Don Allah ku maida hankali ku kula da lafiyar ta. Yanzu ga wannan ka je ka siyo a fara bata,sannan a kawo mata abinda za ta ci,dan har da ciwon ulcer ke damun ta."

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Yah Maheer ya sauke kafin ya miƙa hannu ya karɓi takardar da likita ya bashi,cikin sanyin murya ya ce.

"Mun gode Dr. Anas. In Sha Allahu za mu kiyaye daga yau Hajiya ba za ta sake samun attack irin wannan ba."

"Allah Ya bata lafiya."

"Amin Ya Allah."

Da haka Yah Maheer ya karɓi takardar hannun likita ya wuce pharmacy. Malam Sallau na ganin shi ya ruga da gudu ya nufe shi,cike da damuwa ya ke tambayar jikin Hajiya,murmushin yaƙe Yah Maheer yayi masa kafin ya ce.

"Da sauƙi Malam Sallau,da yardar Allah Hajiya za ta tashi lafiya. Na ɗauki alƙawari daga yau Hajiya ba za ta sake shiga damuwa ba in dai ina raye."

Ƙwalla Malam Sallau ya share kafin ya ce.
Chapter 3 · 0% Book details