← Book details Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 30

Sashe 27

Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da yake ango ba yaro bane shi kaɗai ya zo abunsa;hannunsa riƙe da leda. Ya na shiga ya ji hayaniyar yaran da yake yi wa kallon ƴan kucakucin yaran da ko magana basu gama iyawa ba.

Mairo ce zaƙaƙurar da ta isa gabansa ta ci ɗamara ta miƙa masa hannu ta ce.

"A cake mana kuÉ—in siyan baki kafin mu barka ka je wajen amaryarka."

Murmushi kawai Malam Rabi'u ya yi ya zira hannunsa a aljihu ya ƙirgo dubu ɗaya ƴan hamsin-hamsin ya miƙa wa Mairo dake wata jijjiga da harare-harare. Ya na bata ya naɗe hannunsa ya na kallon ta yana jiran ya ji kuma me za ta ce. Baki ta washe cike da murna ta ce.

"Ku taso mu tafi ango ya yi sallama. Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki sai mun zo da safe cin abincin amarya."

Cikin sauri Malam Rabi'u ya haÉ—e fuska tamau ya ce.

"A kul na ga ƙafar wata yarinyar a cikin ku ta sake zuwar min gida."

Cike da jin tsoronsa suka ranta a na kare suka bar gidan. Su na tafiya Malam Rabi'u ya samu waje ya raba kazar nan gida biyu,ba tare da ya ce da Salma komai ba ya ajiye mata nata kason a gabanta ya ja gefe da nashi ya hau ci. Jin ɗakin ya yi shiru ne ya sanya Salma durƙusawa ta ce masa.

"Ina yini."

Murmushi ya saki mai sauti ya ce.

"Lafiya ƙalou,ki yi haƙuri na shigo ban yi miki magana ba,a zato na ke ɗin irin yaran nan ne masu rawar kai,ni kuma bana son hayaniya shi yasa na tsuke baki na."

Kai Salma ta sake sauke wa ƙasa ta rakuɓe a jikin gadon da take ta mamaki a cikin ranta wai nata ne. Malam Rabi'u kuwa bai sake ce mata komai ba,ya na gama cin kazar sa ya yi gyatsa mai ƙarfi sannan ya ce.

"To sai da safe,ina fatan kin san inda bayi yake. Dan bana so ina bacci ki katse ni ki ce za ki zaga,ni da kika ganni idan ina bacci ba a tashi na."

Kai kawai Salma ta gyaɗa masa ba dan ta san akan me ta gyaɗa kan ba. Ita dai babban buri da fatan ta bai wuce na ta ganta ta keɓanta ita ɗaya ba ta samu damar yin kukan da ke danƙare a ƙirjinta. Waje Malam Rabi'u ya fita ya nufi wani ɗaki dake kallon na Salma ya buɗe da makulli ya shiga. Fitilar tocilan ya kunna ya ke haska ɗakin da ita, daga nesa Salma ke hango Malam Rabi'u ya na cire babbar rigarsa,gabanta ne ya faɗi sai ta yi saurin kawar da kanta gefe ta sake takure wa a waje ɗaya. Salma bata da ilimi ko na sisin kwabo akan rayuwar aure,a bakin su Mairo da ƙawayenta ne ta ji wasu abubuwan a lokacin da aka barsu tare. Babban buri da fatanta bai wuce Allah Ya sa kada Malam Rabi'u ya zamo daga cikin ƴan isakan mutanen da ke taɓa jikin ƙananan yara ba. Wani irin kuka ne mai cin rai ya turniƙe ta. Nan take ta hau yinsa ta na faɗin.

"Gwaggo don Allah ki zo ki taimake ni tsoro nake ji."

Haka ta dinga kuka a hankali ta na toshe bakin ta gudun kada wani ya ji ta. Ganin hasken ɗakin Malam Rabi'u ya mutu ne ya sanya ta miƙe wa a hankali ta rufe ƙofar nata ɗakin da sauri. Wani irin tsoro ne ya ke shigarta a hankali. Gado ta haye ta takure a waje ɗaya ta na jin kamar ta ɓace ta ganta a ɗakin Kande. A haka bacci mai daɗi ya ɗauke ta.

*************************

A ɓangaren su Abdulwahab kuwa sai ƙarfe goma na dare suka shiga cikin garin Kura. Su na isa Mudassir ya kafe sai sun je gidan Malam Bala a daren an yi wacca za a yi. Da ƙyar Abdulwahab ya danne shi ya bashi baki kan su bari safiya ta waye a yi komai a ilmance,domin ya kula faɗa da tashin hankali ba zai bashi abinda suka zo nema ba.

A daren suka shiga cikin kasuwa suka samarwa kansu abinda za su ci suka koma gida. Abdulwahab wanka ya yi ya gabatar da shafa'i da wutiri kafin ya nemi waje ya kwanta. Malam Sallau kuwa da Mudassir na nan zaune su na hira kamar ba su ne suka sha gajiya tuɓus ba akan gyaran mota

Washegari da sassafe bayan sun dawo daga masallaci Abdulwahab ya riga su shiga wanka,ya na fitowa Mudassir ya watsa ruwa ya fito. Malam Sallau kuwa gidan su na gado ya wuce dan Æ´an'uwansa basu san ya shigo gari ba a daren jiyan.

Ko karya wa ba su tsaya yi ba suka nufi gidan Malam Bala. Su na zuwa suka yi sallama a bakin ƙofa kafin Abdulwahab ya sa kai ya shiga gidan kai tsaye. Hasiye da ke bakin murhu ta na hura wuta ce ta fara arba da fuskar Abdulwahab da ya tamke ta tamau kamar bai taɓa dariya ba. Yaƙe ta fara yi ta hau ƙwala wa mijinta kira da duk wanda sunan sa ya shiga bakinta. Sai take jin ba za ta iya motsa wa ba kada Abdulwahab da ya fusata ya sa ƴan sanda su harbe ta.

Kai tsaye ɗakin Gwaggo Kande Abdulwahab ya shiga. Zaune ya tarar da ita akan abun sallah idanuwanta sun koɗe sun yi jawur saboda kuka. Ta na ganinsa ta sunkuyar da kanta ƙasa ta fashe da wani sabon kukan da yake jinsa a cikin ransa. Durƙusawa ya yi a gabanta ya kamo hannuwanta ya ce.

"Gwaggo ki kalle ni,ki dena saukar da kanki ƙasa kamar wadda ta aikata wani laifi."

Cikin kuka Gwaggo Kande ta ce.

"Na aika babban kuskure Abdulwahab. Na yi nadamar zamowata matar Malam. Ji nake yi kamar na mutu saboda baƙinciki. Ina soyayya da tausayin da Malam ya nuna min a tsawon rayuwarmu? Me ya sa ya zaɓi ya ƙuntata wa zuciya ta a cikin ƙanƙanin lokaci irin wannan? Salma ita ce farinciki na ya kuma san da hakan,sai gashi ya yi amfani da ita wajen rusa wannan farincikin nawa na shekara da shekaru kamar wanda dama can yana jin haushi na. Babbar damuwata yanzu bata wuce zaman Salma da Samira a waje ɗaya ba,Samira bata ƙaunar Salma ko kaɗan,tun su na nan gidan ta saka ta a gaba ban dai taɓa faɗa bane saboda nima bana bari idan ta yi mata abu,to yanzu da suke su kaɗai wa zai rama mata idan Samira ta zalunce ta?"

"Allah shi ne zai rama mata Gwaggo,ina so ki dena damuwa dan ba laifinki bane abubuwa suka kasance a haka. Na san laifi na ne ya shafi Salma,ko kin manta ni ne na ƙi auren ƴarsu? Shi ya sa suka biyo ta nan dan su rama abinda na yi musu."

A hasale Mudassir dake tsaye yana kallon su ya ce.

"To ana so dole ne? Wa ye ya basu dama da ƴancin aurar da yarinya ƙarama babu izinin magabatanta?"

Muryar Malam Bala ce ta daki dodon kunnen Mudassir dake tsaye a bakin ƙofa;kamar saukar aradu.

"Ni ne nan na ba wa kai na izinin aurar da ita,domin a ƙarƙashi na take,idan tarbiyyarta ta yi kyau ni ne,idan tarbiyyarta ta ɓaci ni ne. Me ya sa lokacin da nake kula da ita cinta,shanta,suturarta da duk wani abu da ya shafi rayuwarta baku ce wa ya bani izinin yin hakan ba,sai yanzu da na ga dacewar na aurar da ita ga mutumin da na san zai kula da ita ko bayan ranmu shi ne na yi laifi?"

"Tsohon da ko yau ana iya sanar da mutuwarsa kake maganar zai kula da Salma ko bayan ranmu? Kai Malam ka fa yi son zuciya dole ne kuma a warware wannan auren ko kana so ko baka so."

"Kai kuma a wa da kake ta baloƙoƙo kamar wani kwarton ƙadangare?"

A hasale Mudassir ya isa gaban Malam Bala yana huci kamar zai kai masa duka,sosai hakan ya tsorata Malam Bala da Hasiye da ke laɓe a jikin labule ta na sauraron duk abinda ke faruwa. Baya Malam Bala ya ja Mudassir ya ƙara binsa ya na zaro ido waje,ji yake yi ba dan tsufan Malam Bala ba da tini ya ɗaga shi sama kamar yanda suke wa buhun shinkafa ya lafta shi da ƙasa. Sai da Abdulwahab ya gama lallashin Gwaggo Kande da bata baki sannan ya fito ya tarar da fusataccen amininsa da Malam Bala a tsaye carko-carko kamar zakarun dake shirin kacame wa da dambe. Tsakiyar su ya shiga ya raba kallon kisan kan da Mudassir ke bin Malam Bala da shi. Sassanyar ajiyar zuciya Malam Bala ya sauke ya yi gyaran murya. Kafin ya ce wani abu Abdulwahab ya ce.

"Na ji labarin a gaban sarkin garin nan aka ƙulla auren Salma da Tsohon da ka zaɓa mata ko?"

Da sauri Malam Bala ya ce.

"To abinda Sarkin ne ma ya wakilci É—aurin auren tare da sanya masa albarka? Ai kada ka...."

Katse masa hanzari Abdulwahab ya yi ya ce.

"To ya kamata mu je gaban sarki domin a warware abinda aka ƙulla babu son yarinya da danginta."
Chapter 27 · 0% Book details