Sashe 21
Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Lallai kuwa za ka je duk masallaci ko ƙofar gidan da aka ɗaura wannan ƙaddararran auren a kunce shi;dan ba zan taɓa amincewa a cuci yarinya ƙarama a aura mata tsoho kamar Malam Rabi'u ba."
Tsayuwa Malam Bala ya gyara ya ce.
"Kayya! Kande wai dika-dika Malam Rabi'un nawa yake? Ƙanin ƙanin bayana ne fa."
A hasale Kande ta ce.
"Mutumin da ko za ka girme shi bai wuce ka bashi shekara uku zuwa huÉ—u ba shi ne yaron? Kada fa ka manta Salma bata wuce shekara sha biyu zuwa sha uku ba."
Cikin sauri Malam Bala ya É—aga wa Kande hannu ya ce.
"To kin ga kenan ta yi gadon ki. Ai idan ban manta ba kema da waɗannan ƙananan shekarun aka aura min ke."
"Malam wancan zamanin da wannan da muke ciki akwai banbanci,sannan kuma lokacin da muka yi auren ina da ƙananan shekaru ai kai ma ba wani babba bane."
"Banbancin na menene Kande? Tuwon hatsin aka dena ci ko kuwa shinkafar? Ko kuma kwanciyar sunnar aka canja? Matan ne suka koma na gwal ko me? Bayan haka Kande indai da kara ba karaya ba ni ai uba nake a wajen Salma,a zato na zan iya zartar da komai a kanta. Dama Hasiye ta faÉ—a min idan kika dawo sai kin yi tijara na karyata ta saboda na sanki da biyayya. Ashe ta sauya zani ban sani ba."
"Malam babu zanin da ta sauya,har gobe da jibi ina nan a Kanden da ka sani mai yi maka biyayya akan dikkan umarninka matsawar bai saɓawa Allah ba. Amma wannan abinda ka yi ba zan taɓa yi maka biyayya akansa ba ballantana kara,yanda ka je aka ɗaura aren nan babu sanin dangin uwa da uban yarinya dole ka je a warware."
A hasale Malam Bala ya tsaya a gaban Kande ya na zazzaro mata ido waje ya ce.
"Ke ba na son shashanci fa. Wa ya faɗa miki dangin uwa da uba basu sani ba. A gaban kawunanta, Sarkin garin nan liman da duk wani mai faɗa a ji na ƙauyen nan aka ɗaura,kada ki so ki ga yanda akai ta saka miki albarka da ita kanta yarinya,ko babu komai kun yi taimakon musulunci "
"Ka ce haka mana Malam tinda an ɗaura wa yarinya aure da tuzuru. Ina son ka sani duk wani mummunan abinda ya sami Salma ba zan zauna da kai ba na gama auren ka kenan Malam. Habaa ta ya za a yi wa yarinya aure sai kace wata ƴar tsana? Idan gaskiya ne abun naka ai ka na da wata ƴar ka bashi mana,sai a haɗa ta da ƴar'uwarta gida ɗaya su yi zaman aure,amma ba wai a ɗauki marainiya a kai ta gidan da na san da biyu ka ƙulla auren dan kawai a cutar min da ita ne."
Ta na gama maganarta ta fito waje fuuuu cike da fushi. Karo ta yi da Hasiye da ke yi musu laɓe ta na jin duk abinda suka yi magana akai. Cike da borin kunya Hasiye ta tsugunna tana ɗaukan duk abinda hannuwanta suka hau kai. Murmushin takaici Kande ta yi ta ce mata.
"Na dawo na ga tuggu da munafurcin da kika ƙulla Hasiye,dan kuwa na sani sarai ke ce za ki zuga Malam ya yanke wannan mummunan matakin akan Salma. Ina so ki sani da yardar Allah Salma za ta ba ki mamaki. Sai kin yi nadamar wannan haɗin auren da kika yi ko ba jima,ko ba dade."
Harara Hasiye ta banka wa Kande ta tsirtar da yawu sannan ta ce.
"Eh ɗin ni ce nan matar da ta isa da miji da gida,uwar magada mai mulkin gidan Malam Bala. Har ke kin isa Ƴata ta nuna tana son auren jikanki ki hana ta? To bari ki ji Samira ba ta yi auren tsoho a banza ba,kema dole ne taki jikar ta je can ta ɗanɗani zama da sa'an ubanta. "
"Ba kanta farau ba Hasiye,kuma na tabbata ba za a gama akanta ba,dan ta auri tsoho ba shi ne yake nufin ƙarewar numfashinta ba. Kuma ina so ki dinga tinawa da mugunta dai fitsarin fako ce,kuma idan za ka gina ramin mugunta ka gina shi gajere."
Haka su Kande su ka dinga musayar yawu ita da Hasiye har ta ga rashin dacewar biye mata su yi ta hayaniya. Ɗaki ta shiga ta killace tsarabar da ta zo da ita ta zari mayafinta ta saka ta kulle ƙofarta ta nufi gidan Kawu sale. Ta na zuwa ta dinga doka sallama a tsakar gida domin ko ɗaki bata jin za ta iya shiga. Yanda suka haɗa kai da Malam Bala aka aurar da Salma ba da saninta ba dole ne su je duk inda za su je a warware wannan auren. Ta na nan tsaye Kawu Sale ya fito ya na suɗe hannu tare da haɗe su waje ɗaya ya murtsuke. Washe baki ya yi yana kallon Kande ya ce.
"Ah ah Gwaggo yau ke ce a gidan namu war haka?"
Harara ta banka masa sannan ta ce.
"Da abinda ya fi war haka ma za ka ganni Sale,tinda baku ƙulla gaskiya ba da kai da wancan azzalumin. Yanzu Sale amanar da aka bar mana ita kuka wulaƙanta? Ina laifin ku aura wa Salma matashi wanda ƙarfinsu zai yi ɗaya, kurum sai ku aura mata sa'an ubanta?"
Tsayuwa Kawu Sale ya gyara sannan ya tsotse haƙorinsa ya ce.
"Don Allah Gwaggo Kande ki yi haƙuri da abinda ya faru. Matsala aka samu gagaruma . Wato auren Malam Rabi'u aka fasa saboda yarinyar da zai aura iyayenta sun ji labarin Yayansa dika yara mata yake haifa,kuma yaran ne ke zuwa masa gona su yi duk abinda yaro namiji zai yi,watarana ma har marigayiyar matarsa yake ɗauka ya kai ta gona su yi aiki su dawo. A taƙaice dai sun ji ƙishin-ƙishin ɗin aikin gona da na gida ne ya yi ajalin matar wansa. To shi ne fa Malam Rabi'u da be taɓa aure ba hankalinsa ya tashi da jin wannan mummunan labari sai ya yanke jiki ya faɗi. Da ƙyar aka zuba masa ruwa ya farfaɗo aka kai shi can asibiti aka saka mas ruwa. Ni dai ban san ya aka yi ba bayan kwana biyu an tashi sallar Juma'a sai ga Malam Bala ya zo muna tare da Sarki a idar da sallah ya ce wa Malam Rabi'u ya bashi ƴarsa Salma ya aura idan yana so."
"Shine kuka amince ba tare da yin tunanin zaluntar yarinya marainiya da ake son a yi ba ko?"
Kai Kawu Sale ya sosa ya na faÉ—in.
"A yi haƙuri Gwaggo ƙaddara dai ta riga fata yanzu."
"Humm Allah Ya kyauta,gobe da sassafe zan koma Kano na sanar da ɗan'uwanta duk abinda kuka ƙulla."
Gaban Kawu Sale ne ya faɗi,nan take nadamar ƙin hana auren Salma da Malam Rabi'u ta kama shi. Sai dai ya baro gini tin ran zane. Kande gida ta koma ta na matsar hawaye tare da hango irin tarin kalubalen da Salma za ta fuskanta a cikin wannan auren. A haka ta kwana da zullumi da fargaba. Washegari da safe ta shirya tsaf da nufin tafiya Kano ta sanar da Abdulwahab abinda yake faruwa. Sai dai lokacin da ta je ta sanar da Malam tana neman izininsa na zuwa Kano sai ya ce.
"Babu inda za ki je ki hure wa yarinya kunne ta bijire wa mijinta. Nan da jibi Hasiye da matar Sale za su je su yi barka sannan su taho da ita."
Hawayen da Kande ke ta riƙewa kada su zuba a gaban maƙiyinta Malam Bala ne suka zubo mata. A daren jiya ta raɗa masa sunan maƙiyi,domin kuwa babu wanda zai aitaka abinda Malam Bala ya aikata a kira shi da masoyi. Ba dan ta so ba dole ta haƙura ta bar ɗakin nasa ta koma ɗakinta ta na sharar hawayen takaici.
A kan idonta Hasiye ta dinga rawar kan zuwa Kano. Tin da safe ta tsefe kanta ta je aka rangaɗa mata sabon kitso,sai kuma ta ɗaura jan lalle a ƙafarta da dare. Gari na wayewa Hasiye ta sheƙa wanka ta saka atamparta sabuwa da suka ci bikin Suwaiba da ita ta fito ta na kallon kanta a ƙaramin madubin hannu ta na gyara zaman mayafinta a kafaɗarta. Washe baki Malam Bala ya yi ya ce.
"Har an fito kenan?"
"Allah Ya yarda Malam. Tinda a yau za mu je mu dawo a yau,ai gwanda mu gaggauta mu yi abinda ya kamata."
"Haka ne Hasiyatu matar fir'auna,waii matar Malam Bala. Kin ga kyan da kika yi har ya ruÉ—a ni zan sauya miki sunan miji. To ga wannan a yi na mota ko?"
Hannu ya sa a aljihu ya zaro kuɗin mota ya bata yana dariyar samun nasara. Har cikin ransa yake jin daɗin rama wulaƙancin da Abdulwahab ya yi masa na ƙin auren Samira. Sosai ya yaba da shawarar da Hasiye ta bashi na aura wa Malam Rabi'u Salma dan yin ramuwar gayya. Ɗaki ya koma kai tsaye ya zauna ya fara karya wa.
A tasha su Hasiye suka haɗu da matar kawu Sale. Gaisawa suka yi da juna suka samu mota suka shige. A mota banda zuzuta gidan da su Abdulwahab suke a Kanon babu abinda Hasiye take yi,ita a dole ta san kan waje Matar Kawu Sale bata sani ba. Haka suka dinga hira har suka isa garin Kano. Su na isa suka sauka daga mota suka samu taxi suka shiga. Da kwatance motar ta kai su har gidan Abdulwahab. Su na zuwa suka hau buga ƙofa suna faɗin.
"Ohh mutanen birni,su fa yanzu bacci suke yi ko?"
Hannu Hasiye ta sa ta sake buga gidan da ƙarfi. Su na nan tsaye wani ƙaton mutum ya buɗe gidan jikinsa ko riga babu ya kalle su ya na muzurai ya ce.
"Kai ku su wanene kuke damun mutane?"
Yawu Hasiye ta haÉ—iya a tsorace ta ce.
"Wajen Jikana Abdulwahabu muka zo."
"Waye me wannan sunan kuma? Malama ku ware daga nan nan gidana ne ni ban san wani Abdulwahab ba."
Ƙirji Hasiye ta dafe ta ce.
"Kai É—annan don Allah kada ka yi mana wasa..."
A hasale mutumin ya zabura ya ce.
"Na yi miki kama da abokin wasanki ne?"