Sashe 23
Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Inyeee! wato bayan wancan gidan da suka shaƙe da kayan alatu suka barwa aljanu suna dabdalarsu a ciki a can ƙauye,nan ɗin ma sai da suka cika shi da dukiya. Lallai yaron nan ba ƙaramin baƙinciki ya yi mana ba. Yanzu da Samira ce a gidan nan ai mu da talauci sai dai mu hango shi a maƙota."
Zama ya yi a kujera ya ji ya lotsa saboda laushi,sai ya sake miƙe wa tsaye ya zauna da ɗan ƙarfi kamar wani ƙaramin yaro. Ya na nan yana zancen zuci da na fili Abdulwahab ya shigo parlourn cikin shirin fita office. Gaisawa suka yi cike da girmamawa sannan Abdulwahab ya ƙwala wa Salma kira ya ce a kawo musu abun karyawa shi da Malam Bala. Layuzah ce ta yi sallama riƙe da babban faranti ta shiga ta ajiye a tsakiyarsu sannan ta koma gefe ta tsugunna. Gaida Malam Bala ta yi tare da tambayar mutanen gida. Nan ya dinga shirga ƙarya ya na faɗa musu yanda Kande ta yi kewarsu har ta tashi da zazzaɓi ta na ta cewa a kawo mata Salma amanarta,shi yasa ya yi mata alƙawarin zuwa ya tafi da Salmar. Cike da tausayawa Layuzah ta tambayi jikin Gwaggo Kanden,Malam Ya ce da sauƙi,ya dai kula kawai kewar Salma ke damunta,da an kai mata Salma za ta ware,fatan samun sauƙi Layuzah da Abdulwahab suka yi mata ta miƙe ta fita ta basu waje.
Abdulwahab da kansa ya buÉ—e food flask É—in masa ya zuba wa Malam Bala,sannan ya É—auki kwanon miya ya zuba masa miyar gyaÉ—a da ta ji naman rago. Kunun gyaÉ—a Abdulwahab ya zuba masa a babban mazubi sannan ya saka madara da sugar mai yawa ya juya masa ya ajiye masa a gabansa. Yawun Malam Bala kamar zai zubo haka ya dinga magana yawun na tsartuwa. Babu ko bismillah ya danna hannu ya hau ci yana zuba surutu, a cikin surutun nasa ne yake sanar da Abdulwahab zai wuce da Salma gida idan ya bada izini. Ba tare da Abdulwahab ya kawo komai a ransa ba ya ce.
"Babu damuwa Baba,ai dama ko randa za ta tafi ta so ƙwarai ta tafi da Salman yarinyar ce ta ƙi amincewa."
"Ai sha'anin yaro sai shi,ka duba ka ga yanda suke da Kande,a gani na ai bai kamata ta ƙi binta ba ballantana har ga dinga nuna rashin jin daɗi dan za ta koma can,ta na abu sai kace wata wadda ake yi wa wani abun a can. Wa Salma take da shi yanzu dai a duniya da ya wuce kai da Kande? To sai kuma danginku na uwa da uba."
Murmushi kawai Abdulwahab ya yi ya ci gaba da cin abincinsa. A haka suka gama ba tare da kowa ya sake cewa komai ba. Sosai Malam Bala ya ci abincin nan har a ransa ya na tunanin da ace Abdulwahab zai ɗan fita da sai ya samu leda ya ƙulle sauran.
Kiran Salma Abdulwahab ya yi ya ce ta haÉ—a kayanta ta bi Baba. Cikin kuka ta tashi ta koma É—akin da ta sauka ta fara haÉ—a kayanta. A haka Layuzah da Ammabuwa suka same ta tana kuka. Tsaraba sosai suka haÉ—a mata sannan Layuzah ta rungumeta ta ce.
"Ki yi shiru ki dena kuka ƙanwata. Na yi miki alƙawari a Kura za mu yi yawon arba'in saboda mu nuna wa dangi Aabid. Ina komawa kuma zaki tattaro ki dawo waje na har sai mun yi watanni biyu ko uku sannan za mu dawo."
Ammabuwa ce ta kalli Layuzah ta ce.
"Inyee ashe kun gama tsara bari na ni kaÉ—ai a gidan ba tare da kun sanar da ni ba ko?"
"Haba ke kuwa ai kema kin san dole na sanar da ke,yanzun ma maganar ta zo ne ba tare da shiri ba."
"Humm shikenan Allah Ya nuna mana lokacin."
"Amin Ya Allah."
Da wannan lallashin Salma ta saki ranta ta fito saɓe da jakarta da su Layuzah suka shaƙe mata ita da kaya. Malam Bala ne ya fito daga parlour ya na ta tura hannu a aljihu yana zuba wa Abdulwahab godiya kamar zai kwanta. Shi kuwa sai ya bi bayansa kawai yana kallon Salma tare da karantar yanayin da take ciki. Ya riga ya gama tsara yanda zai ɗauke ƙanwarsa da zarar burinsa na gina katafaren gidan da za su tattare su koma ya cika.........
MUGUWAR MACE.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨âœï¸
*Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarÆ™aÆ™iyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman duniya. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k É—inki ta wannan account É—in 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel É—in nan ne da niyyar ki yaÉ—a shi a group É—in da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haÆ™uri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaÉ—a kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨âœï¸
PAGE 17.
A na kiran sallar asr su Malam Bala suka isa gida. Da sauri Salma ta yar da jakarta a tsakiyar ɗakin Kande ta isa wajenta ta na dariyar farincikin ganinta. Sai dai yanayin da ta gani a tattare da mariƙiyar tata ne ya sanyaya mata jiki har bata san sanda ta zube a saman guiwowinta ba ta ɗora hannuwanta a saman na Kande ta ce.
"Gwaggona da gaske kewa ta kika yi sosai shi yasa baki da lafiya? Bamu fa jima da rabuwa ba Gwaggo,don Allah ki dena damuwa gani na dawo wajenki ba zan sake yin nisa da ke ba har abada."
Hawayen da Salma ta ga Kande na share wa ne ya sake rikita ta ta kifa kanta a saman cinyar Kande ta na kukan da bata san dalilin yinsa ba. Bayanta Kande ta ke shafawa a hankali ta na shan majina tare da lumshe idanuwanta da suka gaji da zubar da ruwan hawaye. Wani irin zafi take ji a cikin ranta. Murya na rawa ta ce.
"Ba ina kuka saboda kewar ki bane Salma. Ina kuka ne saboda bani da hanyar da zan aika wa Abdulwahab saƙon ya nesanta ki da garin Kura nisa na har abada. Ina kuka ne saboda fin ƙarfin da aka nuna mana da ni da ke marainiyar Allah. A yau na tabbatar da cewa wasu dangin suna suka tara kawai,domin da namu dangin aka haɗa kai aka nuna min iyakata,Kawunanki sun nuna min cewa ni ba kowa bace a wajensu face ƙanwar ubansu dan haka bani da hurumi a yanke hukunci a rayuwarki. Dangin mahaifinku kuwa sam basu san me ya faru ba har sai da mai afkuwa ta afku. Salma ina mai neman gafarar ki ki yafe min saboda gazawa da na yi a wajen rikon amanar ki har ki girma a aura miki kalar mijin da kike so."
Gaba ɗaya Gwaggo Kande ta gama rikita ƴar ƙaramar ƙwaƙwalwar Salma. Cikin rashin fahimtar inda maganganun Kande suka dosa Salma ta ce.
"Don Allah Gwaggo ki yi min bayani dalla-dalla yanda zan fahimci abinda kike son sanar da ni."
Zama Gwaggo Kande ta gyara ta zaunar da Salma a gefenta ta hau zayyano mata duk abinda yake faruwa,daga ƙarshe ta ce.
"Ɗazun nan Baffanninku suka bar nan ransu a matuƙar ɓace,domin a zaton su da sahhalewa ta aka ɗaura miki aure da Rabi'u. Sai da na yi musu bayani sosai,sannan na tabbatar musu da cewa Malam ya ce da amincewarsu da Kawunnanku aka ɗaura miki aure,sannan suka sassauta suka ce za su dawo idan Malam ya dawo daga ɗakko ki;dan ba za su amince da wannan ƙaddararran auren ba."
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Salma ta sauke a cikin kukan da take ta sharɓa tinda Gwaggo ta bayyana mata abinda ke faruwa. Kasa cewa komai ta yi sai ta miƙe ta ja jakarta zuwa ƙuryar ɗakin ta koma gefen katifarta dake ɗakin ta zauna ta na ci gaba da kukanta. Gwaggo Kande na ganin haka sai ta dinga bata baki ta na nuna mata cewar dole ne a warware wannan auren,dan haka kada ma ta sa wa kanta damuwa ballantana wani ciwon ya kama ta. Jiki babu ƙwari Salma ta fita tsakar gida ta na sharar hawaye ta ɗauki buta ta nufi bayi domin kama ruwa. Ta na shiga banɗakin ta rushe da wani sabon kukan mara sauti. Da ƙyar ta iya danne matsananciyar damuwar da ta rikito mata a lokacin da Gwaggo na bata labari mafi muni a rayuwarta. Sosai tausayin kanta ya lulluɓe ta sai ta rakuɓe a jikin gini tare da ƙanƙanme jikinta ta na ci gaba da kukanta. Ganin za ta makara sallar asr da bata yi bane ya sanya ta wanke fuskarta ta fito daga bayin ta ɗaura alwala ta wuce Hasiye da ke zabga guɗa ta na faɗin.
"Ka ga amarya a gidan Malam Rabi'u Mai Shinkafa,babban manomin da ya ke ji da noman rani da ta damina,dattijo mai kamar yaro ga kuɗi ga tashen gayu. Yo kukan me kike yi kuma? Yarinya ki saki ranki ki je ki ci arziƙi ki bar arziƙi a mazauninsa. Yo ke in banda ma aljana ta aure shi ai ba sa'an aurenki bane,da sai dai ki zamo sa'ar jikarsa ta biyu ko ta uku."
Kallon Hasiye Salma ta yi a karo na farko a rayuwarta da ta ji ba za ta iya ƙyale ta ba ba tare da ta bata amsa ba ta ce.
"Alhamdulillah mu a kowanne hali gode wa Allah muke yi,dan haka na tabbata godiyar Allah ce ta kai ni ga matakin auren mijin da ban zaɓa wa kaina ba,da izinin Allah ba zan wulaƙanta ba idan ma kin zuga an aura min tsoho saboda mugunta ne."
Salati Hasiye ta saki ta na tafa hannaye tare da kama haɓa ta ce.
"Inyeeee! Ehh lallai ne yarinya wuyanki ya isa yanka. To Kande ga shi nan a gabanki yarinyar da kike ta kukan ta yi ƙarama da auren tsoho ta tsaya tana zaro kalaman da ko wata babbar albarka. Za kuma ki san kin kira ni da muguwa yarinya,baki ga komai ba a rayuwarki."