Sashe 14
Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abdulwahab na zana jarabawarsa ta Æ™arshe a sakandire mahaifinsa majinginarsa kuma katangarsa ya faÉ—i ya rasu. Sosai mutuwar Malam Musa ta girgiza mutanen garin Kura da kewaye. Domin kuwa shi É—in mutumin kirki ne,kuma su na amfana da shi matuÆ™a gaya a É“angaren noman rani da damuna. Rasuwar Malam Musa ta sanya Abdulwahab zamowa yaro mara son magana da kuma kaÉ—aice kansa daga cikin al'umma. Lokuta da dama yafi tafiya cikin gonar mahaifinsa ya kwanta ya sha kukansa,daga Æ™arshe bacci ya É—auke sa,sai idan an aika yara nemansa ne ake samo shi a gona. Sosai Gwaggo Kande take tausayawa rayuwarsa saboda ta fi kowa sanin irin gata da kulawa tare da soyayyar da iyayensa suka bashi. Ganin yana neman ya lalata rayuwarsa ne ya sanya mijin Gwaggo Kande shige masa gaba a lokacin da sakamakon jarabawarsa ya fito; Result ya yi kyau sosai,sai ya biya masa kuÉ—i ya rubuta JAMB a wannan shekarar. Cikin ikon Allah ya samu makin da ake nema domin shiga jami'a. Malam Bala shi ne yayi tsaye tsayin daka ya saka Abdulwahab a makarantar jami'a ta kano wato Ado Bayero University Kano State. Ranar da Abdulwahab zai tafi makaranta Gwaggo Kande da Salma sai kuka suke yi,shi kuma yana jin wani irin farinciki a ransa zai bar garin Kura ya je wajen da zai yi nesa da inda ya yi rayuwa da iyayensa da ya rasa. Har tasha Malam Musa ya É—auki Salma suka raka Abdulwahab da kayansa a cikin Ghana most go da leda ViVa.Â
Bayan tafiyar Abdulwahab makaranta Malam Bala ya ci gaba da kula da shi da buƙatunsa har ya kai level 200. Sai dai zugar abokai da danginsa ce ta sanya shi fara ja da baya tare da cire duk wani tallafi da yake bawa Abdulwahab. Lokacin da Abdulwahab ya samu hutu ya leƙa garin Kura mutanen garin suka gansa fes da shi gwanin sha'awa,sai suka ƙara tinzira Malam Bala suna yi masa nuni da ya zauna yana ta kashe kansa shi da yaransa su na gina yaron da bai san zafin nema ba. Tin suna maganar a ɓoye har magana ta shiga kunnen Abdulwahab. A lokacin da ya ji sai ya ƙi amincewa Malam Bala zai ɗauki zugar masu zuga har ya daina tallafa masa kamar yanda ya saba. Lokacin komawa makaranta na yi ya tinkari Malam Bala da maganar kuɗi,a nan ne fa Malam Bala ya murza wa idonsa toka ya ci wa Abdulwahab mutunci tare da yi masa gori kala-kala. Sosai kalaman Malam Bala suka ƙona wa Abdulwahab zuciya,amma sai ya tuno da alkhairin da ya yi masa a baya. Godiya ya yi masa ya shiga wajen Gwaggo Kande ya sanar da ita zai koma. Sanin halin da ake ciki ne ya sanya ta miƙe wa ta shiga ɗakinta ta ɗakko wata baƙar leda ta dawo ta zauna a gefensa ta ajiye masa a saman cinyarsa ta ce.
"Karɓi wannan,kuɗin awakin mahaifiyarku ne da na sa a siyar tin wancan satin. Kasancewar na fuskanci Malam ya fara ɗaukar zugar mutane ya sa na ce to meye amfaninsu? Shine na ba wa Kawunka Sale na ce a siyar a kawon kuɗin. Ka ƙara haƙuri Audu watarana sai labari. Allah Ya yi maka albarka Ya sa a mori wannan ilimi da kake ta fafutukar nema."
"Amin Ya Allah Gwaggo na gode,Allah Ya ƙara miki lafiya da nisan kwana mai albarka in kai ki makka da Madina ke da Baba da Salma."
Guɗa Gwaggo Kande ta zabga tana murna,domin ko Abdulwahab bai kai ta Makka da Madina ba ya biya ta tinda ya sa hakan a niyyarsa. A wannan karon Abdulwahab da kansa ya nemi Salma ta yi masa rakiya tasha ta riƙe masa ƴar ƙaramar jakarsa ta goye suka tafi su na hira tana ta zuba masa surutu irin na yara masu wayo da baki. Da za su rabu ya siya mata kayan kwalama irin na yara a tasha ya tsaya a bakin tashar har ta ɓacewa ganinsa. Gani yayi ana ta loda shinkafa a bayan manyan motoci,gefe ɗaya kuma ga wake,gero,alkama,da maiwa tare da sauran kayan amfanin gona ana ta siyarwa. A hankali Abdulwahab ya matsa kusa da wani shago mafi kusa da shi,sallama ya yi wa mai shagon suka gaisa sannan ya furta masa buƙatarsa na son siyan shinkafa buhu ɗaya. Babu ɓata lokaci suka yi ciniki Abdulwahab ya sa ɗan dako ya ɗaukar masa shinkafar ya kai masa wajen lodi.
Ya na isa garin kano........
*Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarÆ™aÆ™iyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman gidan aure. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k É—inki ta wannan account É—in 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel É—in nan ne da niyyar ki yaÉ—a shi a group É—in da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haÆ™uri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaÉ—a kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨âœï¸
MUGUWAR MACE.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨âœï¸
*Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarÆ™aÆ™iyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman duniya. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k É—inki ta wannan account É—in 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel É—in nan ne da niyyar ki yaÉ—a shi a group É—in da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haÆ™uri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaÉ—a kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨âœï¸
PAGE 11.
Abdulwahab na shiga garin Kano ya samu abun hawa ya ɗaukar masa buhun shinkafarsa ya kai masa har bakin makaranta,daga nan ya samu machine ya loda masa kayansa ya shigar da shi har ƙofar shiga hostel. Ya na isa bakin gate ɗin hostel ya sauke shinkafa ya sallami mai machine. Abokinsa kuma ɗan ɗakinsu ya kirawo wato Mudassir ya roƙe shi ya taimaka masa suka shigar da shinkafa. Sai da ya yi wanka ya huta ya ci abincin da Mudassir ya gabatar masa sannan ya labarta wa abokin nasa duk abinda ya faru a gida. Ajiyar zuciya Mudassir ya yi kafin ya saki murmushin takaici ya ce.
"Allah Ya kyauta. Ai mutane yanzu suna daga cikin masu hana alkhairi,su basu yi ba sannan basu bar wani ya yi ba. Ni ai tinda na samu dangin Ummanmu na riƙe min Layuzah da amana bayan rasuwar iyayenmu sannan tana zaune cikin gata bani da wani takaici,yanzu haka fa ta na aji uku na ƙaramar sakandire,sannan ƙanin Ummarmu ya biya mata kuɗin bikin saukar ƙur'ani da za a yi musu a ƙarshen watan nan. Shi yasa ka ga ina faɗi tashi ina neman abinda zan rufa wa kai na asiri ba tare da na sake ɗora musu wani nauyin ba,amma fa su ba sa son ina wahala ba tare da na tambaye su taimako ba,ni kuma ina duba halin yau da gobe ne kada azo tin ana yi maka abu ta daɗin rai a gaji da kai,kamar yanda aka yi maka yanzu abokina. Allah dai Ya ƙara shiga lamuranmu. Dama bahaushe ai ya ce babu maraya sai rago,wannan dabarar da ka yi ta yi kyau,bari ma ka ga me ya kamata mu yi tin yanzu."
Da sauri Mudassir ya miƙe ya ɗauki kwanon silver da spoon ya fita tsakiyar saman baranda ya hau kiɗa da kwanon yana kiran mutane. Kafin kowa ya bashi hankalinsa ya rage murya ya tambayi Abdulwahab farashin kwanon shinkafa, Abdulwahab na sanar dashi ya fara tallata wa abokan karatunsa shinkafar akan farashi mafi sauƙi akan yanda suka saba siye a gari. Da yake suna cikin lokacin da wasun su sun dawo da kuɗin shopping daga garuruwansu,wasu kuma sun zo da kayan provision amma basu yi awo ba. Dan haka sai suka dinga rububin zuwa siyen shinkafa. Sai da mutane suka taru Mudassir ya ce.
"To ƴan'uwana ɗalibai ga fa sabuwar sana'ar abokina na siyar da kayan hatsi ko wanne iri mutum yake so,kawai ya faɗa masa in dai da kuɗi hannu ba bashi ba za ku samu akan farashi mai sauƙi. Ni kuma ina nan zan ci gaba da yi muku wanki da aikace-aikacenku kuna biyanaaaa."
Shewa matasan suka ɗauka,wasu na faɗin a basu shinkafa kada ta ƙare. Cikin sauri Abdulwahab ya hau neman kwanon da zai yi awo da shi,da ƙyar suka samu aron kwanon awo a hostel ɗin ya hau auna wa mutane shinkafa Mudassir na karɓar kuɗi ya na ƙirgawa. A haka shinkafa ta ƙare tas wasu na buƙata dan basu samu ba. Cike da murna da farin ciki Mudassir ya yi musu alƙawarin za su samu a cikin satin. Su na koma wa ɗaki ya kwaso kaf kuɗin da aka sayi shinkafa ya damƙa a hannun Abdulwahab yana taya shi murnar siyar da shinkafa da ya yi a ranar farko da ya fara kawo ta. Cike da tsantsar farinciki Abdulwahab ya rungume Mudassir yana yi masa godiya. Daga baya kuma ya yi jimm kafin ya ce.
"Amma na ji ka ce musu za su samu wata shinkafar a cikin satin nan,kada fa ka manta da karatunmu abokina."
"Ai babu abinda zai taɓa mana karatunmu abokina. Da an tashi daga lectures ranar alhamis kawai ka je Kura ka ƙaro shinkafa. Ka ga daga nan ma sai kai ma ka shiga jerin mutanen da za a dinga kawo wa hatsi ba tare da sun je har garin ba,tasha kawai za ka je ka ɗauki saƙon ka kamar yanda na ga wasu ƴan kasuwan na yi."
"Eh kafin na samu wannan damar dole sai na je mun tattauna akan yanayin yanda zan dinga biyansu kuÉ—insu,da yanda nima zan dinga samun nawa kayan."
"Kada ka ji komai abokina Allah Yana tare da mu,fatana dai Allah Ya sa ka fara cikin nasara Ya sa hanyar arziƙinka ce."