Sashe 17
Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ɓangaren Abdulwahab kuwa bai koma Kano ba sai da Baffansa Habu da Kawunsa Sale. Kai tsaye gidan su Mudassir suka je suka nemar masa auren Layuzah. Babu ɓata lokaci Iyayensu Mudassir suka amince da auren nasu,domin kuwa sun jima da sanin aiken da Abdulwahab ɗin yake yi wa Layuzah ta wajen Mudassir. Sannan kuma sun yaba da tarbiyyarsa da riƙonsa da addini. Sosai iyayen Abdulwahab suka ji daɗin tarbar da aka yi musu.
Tin daga wannan ranar Abdulwahab ya riƙe wuta wajen zuwa zance da kafa gwamnatinsa a wajen Layuzah. Ita kuwa dama ta jima da yaba wa da abokin Yayan nata ba ta dai nuna alama ba ne kawai saboda kunya irin ta ƴa mace.
Bayan wata ɗaya da zuwan iyayen Abdulwahab,ya shirya ya je ƙauye ya siyar da filayensu gaba ɗayansu da duk wata kadara da kiwon iyayensu aka raba musu gado shi da Salma. Kasonsa ya ɗauka ya gyara gidan iyayensa aka yi musu ginin zamani,a ciki ya yi lefe ya kuma aje na sadaki. A wannan lokacin ne ya haɗu da Malam Sallau.
Malam Sallau mutum ne mai riƙon amana,ya ƙware a harkar gini da dillancin gidaje da filaye. Tin daga wannan lokacin suka fara ƙulla alaƙar kasuwanci,domin kuwa Malam Sallau Abdulwahab ya ba wa kuɗin Salma aka siya mata fili ma daidaici,sai ya bada hayarsa wa manoma,duk shekara idan sun yi noma su na ba da kuɗin hayar gona. Ya na zuwa Kano sai ya buɗe mata account a bankin da yake ajiyar tasa dukiyar.
Bayan watanni uku aka ɗaura auren Layuzah da Abdulwahab. Aure ne da ya samu halartar dangin iyayensu Abdulwahab ɗin baki ɗaya. Sai dai abun mamaki ta ɓangaren Malam Bala bai je ba,haka ma Hasiye ta ƙi zuwa kuma ta hana yaranta ko ɗaya zuwa. Kande kuwa abun bai dame ta ba,sai ta shiga cikin danginta ta dinga farinciki da murna har aka yi taro aka tashi lafiya,amarya ta tare a ɗakinta cike da gara mai tarin yawan da ba a taɓa irinta a ƙauyen Kura ba. Nan fa mutane suka dinga zuzuta arziƙin iyayen Layuzah wasu ma sai suka dinga yi mata ladabi da biyayya saboda ita ɗin mace ce mai yawan kyauta da ihsani.
Layuzah na yin wata biyu a gidan aure Abdulwahab ya ɗauke ta ya mayar da ita Kano,gidan da suka kama haya ya mayar da ita ta ci gaba da zuwa makarantar bokonta. Da gari ya waye suke raba aikin gidan saboda su gama da wuri. Su na gamawa sai su yi wanka su shirya ya ɗauke ta a babur ɗinsa ya kai ta makaranta ya wuce shagonsa da ya bunƙasa ƙwarai da gaske.
Sosai Mudassir ya riƙe amana,haka sauran ma'aikatan wajen ma suna son ubangidansu dan baya yi musu mugunta,shi yasa su ma suke kyautata masa suke yin aiki tuƙuru da ransu da lafiyarsu.
Cikin ikon Allah duk yanda mutane suka dinga surutun Layuzah bata haihu ba bai dami Abdulwahab ba. Hasali ma gode wa Allah ya dinga yi da bata samu ciki ya katse mata karatu ba. Saboda yanda mutane ke damun Layuzah da zancen haihuwa a Kura sai Abdulwahab ya dena zuwa da ita. Idan ya tashi sai ya je ya yi musu hutun ƙarshen mako ya koma. Duk wanda ya yi masa zancen haihuwa sai ya ce.
"Allah bai kawo ba har yanzu tinda tasa ce shi ke bayarwa wanda ya so ya hana wanda ya so. Wanda ya ba wa kuma muna taya su murna da fatan su samu damar yi wa kyautar da Allah ya basu kyakkyawan riƙo."
Halin ko in kular da yake nunawa na damun dangin mahaifansa,har meeting suka haÉ—a akansa amma ya je ya faÉ—a musu komai lokaci gare shi ya tashi ya yi tafiyarsa.
Ana haka Mudassir ya ɗora idanuwansa akan wata Buzuwa da ke zuwa wajen su ta na siyan gero. Tinda Mudassir ya ɗora idonsa akanta ya ji ya kamu da ƙaunarta amma yana jin tsoron ko matar aure ce saboda yanayin yanda take shiga cikin mutunci. Ganin yanda ita ma idan ta je shagon bata gansa ba take tambayarsa ne ya sanya shi binta har gidansu a ɓoye dan ganin inda take, Sai da ya bari ta shiga sannan ya aika yaro gidan dan ya kira masa Buzuwar. Lokacin da ta fito ta ga Mudassir sai ta ce.
"Wataƙila rabo ne yake kiranka. Domin kuwa daf mahaifina yake da bada ni."
Ƙirji Mudassir ya dafe ya ce.
"Ki ce da na yi jinkiri da an yi babu ni?"
Murmushi kawai ta yi ta rufe fuskarta. Shi É—in ma mayar mata da martanin murmushin ya yi ya ce mata.
"To ya sunan masoyiyar tawa?"
"Ammabuwa."
"In Sha Allahu ke mallaki na ce,ke ce za ki zamo uwar yarana. Ni suna na..."
"Mudassir. Kada ka yi mamakin yanda aka yi na san sunan ka."
"Lallai kuwa ba zan yi mamaki ba,tinda yanzu sunan shagon namu ma na neman ya koma shagon Mudassir."
Gyaɗa kai ta yi tana murmushi. A haka mahaifinta ya dawo ya tarar da su. Cike da girmamawa Mudassir ya durƙusa har ƙasa ya gaida shi,shi ma cikin mutuntawa ya amsa ya shige gida. Ya na shiga Ammabuwa ta bi bayan mahaifinta ta shige gida ta na ɗaga wa Mudassir hannu.
A wannan ranar Mudassir ya tunkari Abdulwahab da zancen Ammabuwa,shi kuwa babu ɓata lokaci ya sanya musu albarka,sannan ya yi masa alƙawarin kashe masa duk wani kuɗi da zai buƙata domin aurensa. Cikin lokaci ƙanƙani aka yi auren Ammabuwa da Mudassir,inda suke zaune a gida ɗaya da shi da amininsa da ya zamo masa tamkar Ɗan'uwa.
Matansu sai suka zamo kamar Hassana da Hussaina,sosai Ammabuwa ke girmama Layuzah,saboda Layuzah ta girme ta da shekara ɗaya,kuma bayan haka mijin Layuzah shi ne mai arziƙin da suke raɓe suke ci ta kowacce siga ita da mijinta.
Bayan watanni uku da auren Ammabuwa da Mudassir....
MUGUWAR MACE.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨âœï¸
*Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarÆ™aÆ™iyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman duniya. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k É—inki ta wannan account É—in 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel É—in nan ne da niyyar ki yaÉ—a shi a group É—in da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haÆ™uri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaÉ—a kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨âœï¸
PAGE 13.
Bayan watanni uku da auren Ammabuwa da Mudassir ta fara laulayi mai matuƙar wahala,har sai da ya zamto ba ta iya yi wa kanta komai sai an taimaka mata. Da safe kafin Mudassir ya fita kasuwa shi yake taya ta wanka ya sauya mata kaya. Su na tafiya Layuzah za ta shiga ta kwashe kayan wankin Ammabuwa da na Yayanta ta wanke musu,ita ke dafa mata duk wani abu da take son ci sannan ta zauna ta yi mata hira. Sosai take farinciki da samun cikin da Ammabuwa ta yi,ita kuwa Ammabuwa tsoron kada ta haihu jikinta ya lalace Mudassir ya ƙara aure shi ne ya janyo mata tsanar cikin jikinta. A kullum idan Layuzah na murna ta na faɗin irin gatan da za ta bawa yaro ko yarinyar da Ammabuwa za ta haifa sai Ammabuwa ta ce.
"Ni da ma ke ce kika samu cikin nan ba ni ba,domin gaskiya ba zan iya da ɗawainiyar yara ba. Ko a gidanmu ni kaɗai ce bani da wa bani da ƙani,bana son hayaniyar yara ballantana hidimarsu."
Cike da sanyin murya Layuzah ta ce.
"Ki gode wa Allah,domin shi kaÉ—ai ne ke bada kyautar É—an mutum ga wanda ya so,wannan maganganun naki sam basu dace ba."
A haka suka ci gaba da zama cikin aminci da mutunta juna har cikin Ammabuwa ya cika watanni biyar a duniya. Daga nan ne maƙota masu gulma suka fara shige da fice suna ƙoƙarin raba kan Layuzah da Ammabuwa saboda ganin yanda suke zaune lafiya,Layuzah na bawa Ammabuwa girmanta a matsayinta na matar Yayanta,ita kuwa Ammabuwa na ba wa Layuzah girma a matsayinta na wadda mijinta ke kula da su da duk wata ɗawainiyarsu. Sai dai cikin hukuncin Allah babu wadda ta yi nasarar dasa musu tsanar junansu. Daga ƙarshe da Layuzah ta fuskanci masu shige da fice a gidan na neman yi musu yawa,kuma ba da alkhairi suke zuwar musu ba,sai suka fara zama a waje ɗaya a duk sanda ɗayarsu ta yi baƙuwa. Ganin haka sai mutanen unguwar suma suka fara ja da baya suka rage zuwa,ko sun zo sai dai a gaisa a tsakar gida babu mai kai su ɗakinta su tashi su tafi,sosai su Ammabuwa suka toshe duk wata kafa da za a raba kansu. Wannan abun da suka yi ya faranta ran mazajen su ƙwarai da gaske.
Lokacin da cikin Ammabuwa ya kai wata takwas Abdulwahab ya sauya musu gida suka koma Ƴankaba da zama. Komawarsu Ƴankaba ya sake zuwar musu da sabon arziƙi;har sai da ta kai ta kawo Abdulwahab ya fara fitar da kayan hatsinsa zuwa ƙasashen Nijer,Ghana,da Chadi. Sosai arziƙinsa yake ta bunƙasa har ya sayi ƙaton fili a cikin garin Kanon.
Har sun manta da sun miƙa takardunsu wajen neman aiki,sai gashi Abdulwahab ya samu aikin da yake buri da fata. Murna sosai Mudassir ya taya shi ya ce.
"Ka ga shikenan ni sai na ci gaba da kula da ɓangaren kasuwancinmu na nan kai kuma kana zuwa aikinka na gwamnati."
"Ai kuma sai abubuwan su yi maka yawa abokina,tinda aikin gwamnatin da na samu duk ya shafi harkar noma wannan kasuwancin namu ma ba zai gagare ni ba. Wataƙila idan na tura kayanmu ma sai ka ga sun samu shiga a wajen gwamnati."
Haka su Abdulwahab suka dinga tattaunawa suna samawa kansu mafita akan ci gaban rayuwarsu.