Sashe 26
Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Makullin É—akin Kande Salma ta lalubo a lalitarta dake jikinta ta buÉ—e musu É—akin suka shiga. A gado Kawu Sale ya kwantar da ita ya na yi mata sannu. Cike da tsananin damuwa Kande ta kalli Salma ta ce.
"Lokacin da kika gudu kin tuna da ni Salma? Kin yi tunanin halin da zan shiga ko kuma irin zargin da mutane za su É—ora akan ni ce na ce ki gudu?"
Da sauri Salma ke girgiza kanta tana kuka. Wani irin tausayinsu ne ya lulluɓe Kawu Sale ba tare da ya shirya wa hakan ba. Cikin ransa yake ayyana.
'Anya na yi wa zumuncin ƴar'uwata adalci kuwa? Nawa ne dubu ashirin har da zan karɓi kuɗi na yi ja gaba wajen kassara rayuwar yarinyar da bai kamata ta shiga irin wannan ƙuncin ba da ƙarancin shekarunta? Salma fa yarinya ce sa'ar Isuhun wajena,yanzu idan ni na tsugunna na haife ta zan so a ƙwace mata ƴancin ta na walwala a doron ƙasa?'
Da sauri ya girgiza kai ya miƙe ya bar ɗakin. A tsakar gida ya tarar da Baffa Aƙilu ya na faɗin.
"Ai na ji labarin irin kuɗaɗen da Rabi'u ya sakar muku shi yasa kuka amince kuka aura masa ƙaramar yarinya tinda ba ƴarku ba ce. To ku tsaya ku ji da kyau,na aika saƙo wajen Abdulwahabu,dan haka ku tsammaci zuwansa a kowanne lokaci daga yanzu. Kai kuma Sale ka bani mamaki,akan abun duniya ka ci amanar ƴar'uwarka,tir da ɗan'uwa irinka."
Baffah Aƙilu na gama magana ya bar gidan,kan dole Kawu Sale ma ya ja guiwarsa da ta yi masa sanyi ƙalau ya tafi nashi gidan. Ɗakin Kande Malam Bala ya nufa ya ɗage labule ya na bin Salma da wani irin mugun kallo ya ce.
"Ke kuma daga yanzu kika sake saka ƙafa kika bar ɗakin nan ba da izinin Hasiye ba,sai na lahira ya fiki jin daɗi,munafukar yarinya kawai me fuska biyu,ina ce jiya har da kukan ki kika ce kin ji kin amince za ki yi biyayya ki yi zaman aure? Yau wanne shaiɗanin ne ya ziga ki ki gudu kuma? To ina so ki buɗe kunnen ki da kyau ki ji ni,idan har ɗan'uwanki ya zo ya ce zai raba auren nan kamar ya raba auren ta da ni ne gata nan kwance gabanki,dan haka sai ki zaɓa zaman aure ki yi ibada ko kuma auren mariƙiyarki ya guntule."
Labulen ya saki ya wuce ɗakinsa ya na masifa kamar zai ari baki. Ya na shiga ɗakin Hasiye ta bishi hannunta riƙe da kwanon koko da fanken da suke ta soyawa ita da Mairo da Shamsiyya. Ta na ajiye masa ta zauna a bakin gado ta ce.
"Wannan hukuncin da ka É—auka Malam shi ne daidai,dan idan ba haka ba Abdulwahab na zuwa zai sa a raba auren."
Cike da takaici Malam Bala ya ce
"To ai abinda zai baki takaici Hasiye shine;da ƙyar fa muka danne Rabi'u ni da Jamilu,da tini ya saki yarinyar nan mu kuma asirinmu ya tonu,dan kuwa a yanzu bani da kuɗin da zan biya shi abinda ya bamu duk na zuba su a noman rani."
Haɓa Hasiye ta kama ta na sallami ta ce.
"To ai Malam dama fa shi bai baku kuÉ—i dan rufe muku baki ba,ya bayar ne kawai ba tare da wani sharaÉ—i ba."
Jinjina kai Malam Bala kawai ya yi ya kora kokon da ya kwaso a ludayi. Nan dai Hasiye ta zauna ta ci gaba da zuga Malam Bala tare da bashi mugayen shawarwari.
Da azahar mata suka fara cika gidan Malam Bala su na taya Hasiye da Kande murnar auren Salma. Kande dai ta na ɗaki ta na kallon kowa ranta babu daɗi,ruwan farau-farau ta kora ta koma ta kwanta ta na nishin azabar da ƙirjinta ke yi mata. A haka mata suka dinga cin shinkafa dafa duka da zoɓo,su na surutai akan auren Salma kamar a gabansu wasu abubuwan suka wakana.
Bayan an yi sallar la'asar Mairo ta shigo gidan ita da ƙawayen Salma da ta gayyato na makaranta,Salma na ganinsu ta ɓuya a bayan ƙofar ɗakin Kande ta na sharɓar kuka. Duk yanda suka so su ja ta a yi party ƙi ta yi,kan dole suka haƙura suka ƙyale ta. Rediyon Hasiye Mairo ta ɗakko ta loda mata sabon batir suka saka kaset suka kunna kiɗa su na ta rawa abunsu cike da nishaɗi da jin daɗin ƙawarsu na aure.
*********************
Saƙon da Baffah Aƙilu ya bayar bai iske Abdulwahab da wuri ba. Domin kuwa sai da ya dawo daga aiki ya shiga kasuwa da yamma ake sanar da shi mummunan labarin da ya tayar masa da hankali ƙwarai da gaske. Da yammar ya kira Mudassir ya labarta masa kaf abinda ke faruwa,ko gida basu je ba Malam Sallau ya ja su a ƴar ƙurƙurar motar da suke amfani da ita ta zirga-zirga. Tafe suke su na tattauna lamarin, jinin Mudassir har ya fi na Abdulwahab tafasa,domin shi dama mutum ne mai sanyin halin, Mudassir kuwa ya na da zafi sosai idan aka taɓo shi. Cike da ƙosawa su isa Kura da wuri Mudassir ya ce.
"Malam Sallau ba wa motar nan wuta lokaci na ƙurewa."
"Tom Malam Mudan a bi komai a sannu,da yardar Allah babu abinda zai samu Salamatu sai alheri."
Haka suka ci gaba da tafiya kamar kurame kowa da abinda yake saƙawa a cikin ransa. Gudu suke tsulawa a mota cikin rashin sa'a Malam Sallau ya taka wani abu mai tsinin da ya yi sanadiyyar fashewar tayar motar. Salati Mudassir ya dinga yi ya na jin zuciyarsa na tafasa kamar ta kama da wuta. Gaba ɗayansu fita suka yi suka hau neman taimako ko za su samu wanda zai taimaka musu Malam Sallau ya shiga gari ya samo musu mai gyara.
***********************
A can ƙauyen Kura kuwa mata sun ci sun sha sun yi hani'an,hakan sai ya sake tabbatar wa da Kande cewar Hasiye ce ta ƙulla wannan auren dan kawai ta ƙuntata mata. Tabbas kuwa ta yi nasarar sanya ta a cikin baƙin cikin da tinda take a duniya bata taɓa shiga irinsa ba. Ta na daga ɗaki ta na hango yanda Hasiye ta sha shadda ruwan ɗorawa an yi mata jan aiki da jan zare sai shewa take yi ta na taya su Mairo tiƙar rawa kamar wata ƙaramar yarinya.
Dare na yi Balaraba da Tafisu da sauran ƙawayen Hasiye ne suka shiga har ɗakin Kande suka ja Salma suka yi waje da ita. Wanka suka saka ta a saman turmi suka yi mata da ruwan lalle da magarya suna ta wanke-wanken amarci irin na ƙauye. Ita kuwa Salma ta gaji da kuka ta tsaya kawai ta na kare ƴan matasan ƙirjinta tare da matse ƙafafuwanta da Balaraba ke buɗawa ta na kwara mata ruwan lalle. Su na gama wanke ta tas suka kaita ɗakin Hasiye suka shirya ta cikin atampar da bata san lokacin da aka ɗinka mata ita ba. Tana juya wa bayanta ta ga akwatina guda uku a ɗakin Malam Bala har da takalmi da jaka a cikinsu. Cike da mamakin lokacin da aka kawo su ta kawar da kanta tana jinjina lamarin da take ɗaukan sa kamar wasa.
Turare Balaraba ta fesa mata Tafisu ma ta ƙara mata wani suma suka shafa suna yaba ƙamshin turaren. Anan take jin wannan akwatunan dika nata ne. Mayafi fari ƙal suka yafa mata tare da damƙa mata farar jaka,har ƙasa Tafisu ta duka ta saka mata takalmi fari ƙal sannan suka gyara mata zaman sarƙar dake wuyanta suka kamo hannunta suka fito.
A tsakar gida suka tarar da dangin Malam Rabi'u sun zo ɗaukan amarya,ciki har da Samira da ke cike da matsanancin farincikin da ta kasa ɓoyewa. Wajen Hasiye ta je suka tafa a ɓoye su na magana da ido tare da nuni da bakunansu da hannayensu. Har cikin ɗakin Kande su Balaraba suka shigar da Salma suka zaunar da ita a gaban Kande da ke zaune ta zabga tagumi ta na kallon ikon Allah. Guda mata suka kaure da yi da hayaniya kamar ba su kula da halin da Kande da jikarta ke ciki ba. Cike da hayaniya mata suka ce.
"To Kande lokacin rabuwa da Æ´ar gaban goshi ya zo;sai a yi mata nasiha a wuce da ita É—akin miji dare na yi."
Kasa cewa komai Kande ta yi da ya wuce danne hawayen dake ƙoƙarin ƙwace mata;sakamakon jin irin kukan da Salma ke yi. Ganin dare na yi Kande ta ƙi cewa komai sai mata suka ɗauki Salma dake turjewa ta na ihu suka yi waje da ita. A ƙafa suka nufi gidan Malam Rabi'u da Salma suna tafe su na waƙoƙin amare irin na ƙauye.
Su na isa gidan Samira ta dawo baya ta ce.
"Ai ya kamata ku bar amarya ta fara taka cikin gidanta da ƙafarta kafin kowa ya shiga ko?"
Ai kuwa babu musu Balaraba da Tafisu da ke riƙe da Salma suka sauke ta ƙasa su ka tura ta cikin sashen nata wanda aka katange shi da ginin ƙasa aka yi masa filasta tare da shafen koren fenti mai haske. Salma na saka ƙafa a cikin gidan ta ji kanta ya yi wani irin sara mata kamar zai rabe gida biyu,hannu ta sa ta dafe kanta ta ce.
"Washhh Allah na kaina."
Cikin yi wa Salma tsiya Samira ta ce.
"Ai ko bayanki ne ke ciwo amarya yau dole ango ya sha mai,ku shigar da ita É—akinta ta ga irin dukiyar da mijinta ya kashe mata."
GuÉ—a matan gidan suka kacame da ita kafin su shiga cikin É—akin da yake shine mallakin Salma. GuÉ—a Balaraba ta sake rafkawa ta ce.
"Ahhh yarinya kin yi goshi barakallah masha Allahu. Inyeee har da sif da dibaida. Allah Ya bada zaman lafiya to,ya kawo ƙazantar ɗaki,amma ba ta ƙin shara ba."
Nan fa mata suka dinga yi mata addu'o'i su na lelleƙa sauran wajen su na sam barka. Bayan sun gama ne Mairo da ƙawayen Salma suka zauna mata domin jiran zuwan ango da abokansa dan su basu kuɗin siyan bakin amarya............
MUGUWAR MACE.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨âœï¸
PAGE 19.