← Book details Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 30

Sashe 18

Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Watarana Abdulwahab ya samu Mudassir da shawarar yana so ya biya wa Gwaggo Kande kujerar Makka kamar yanda ya yi mata alƙawari,domin kuwa ita yake gani a matsayin iyayensa a yanzu,dan kuwa ita ce macen da ta yi masa riƙo na gaskiya da amana. Sosai Mudassir ya ƙara ba shi ƙwarin guiwar yin hakan. A tare suka je Kura suka sanar da Malam Bala ƙudirin Abdulwahab na kai Gwaggo Kande Makka,wani irin kishi,hassada da ƙyashi ne ya taso ya lulluɓe zuciyar Hasiye,ji take yi kamar ta zuga Malam Bala ya hana Kande zuwa Makka,sai dai tana ji ta na gani Malam Ya amince su Abdulwahab suka ɗakko Gwaggo Kande da Salma suka kawo su Kano. A cikin satin suka kai ta aka yi mata international passport da duk wani abu da ya dace. Su na dawowa suka tarar da Ammabuwa na naƙuɗa Layuzah na ta kuka saboda bata san da me za ta taimaka mata ba,gashi zamanin babu waya ballantana ta kira mijinta ta sanar da shi halin da ake ciki.

Ko ajiye hijabi Gwaggo Kande bata yi ba ta kori su Mudassir da suka rikice su na faɗin ta fito a tafi asibiti. Su na fita Gwaggo Kande ta taimaka wa Ammabuwa har ta haifi sankacecen ɗanta kyakkyawa fari tas mai kama da ita. Kukan jaririn ne ya sanar da su Mudassir Ammabuwa ta sauka ƙalau. Murna sosai suka dinga yi shi da Abdulwahab. Layuzah kuwa hamdala ta dinga yi tana maimaitawa bakinta ya ƙi rufuwa. Da yammar Gwaggo Kande ta hura wuta a murhu, nan da nan ta ɗora ruwan wanka ta wanke jariri da mahaifiyarsa. Kafin su gama shiri Abdulwahab ya je wajen mai gashin nama ya siyo nama mai yawa da madarar shanu da dabino ya kawo. Yanda ya dinga hidima da Ammabuwa da jaririnta sai ka rantse Layuzah ce ta haihu. Mudassir har kuka ya dinga yi yana ji a ransa zai iya bada rayuwarsa saboda Abdulwahab. Washegari ya je gidansu Ammabuwa ya sanar da haihuwarta, mahaifiyarta ta so ƙanwarta ta je ta kula da Ammabuwa,amma sai ya ce ai akwai mai kula da ita,domin Ammabuwa da kanta ta sanar da shi bata son kowa ya zo saboda gudun gutsiri tsoma na mutane har a yi abinda zai taɓa zumuncinta da Layuzah.

Abdulwahab shi ne ya sayi ragunan suna manya guda biyu. Dan haka ranar suna Mudassir ya ce yaro ya ci sunan Abdulwahab. Sosai hakan ya yi wa Abdulwahab daÉ—i sai Layuzah ta ce za su dinga kiransa da Maheer. Ita dai Ammabuwa har a wannan lokacin yaron bai wani shiga ranta ba,shi yasa ko kuka yake idan Layuzah ta kawo mata shi dan ta shayar da shi,sai ta dinga kuka ta na faÉ—in zai mayar da ita tsohuwa. Sai da Gwaggo Kande ta yi mata wankin babban bargo sannan ta ce za ta je har gidan iyayenta ta faÉ—i iyashegen da take yi,sannan ta rungumi yaronta ta na bashi kulawar da ta dace duk wata uwa ta ba wa É—anta.

Bayan suna da sati biyu Gwaggo Kande ta tafi Makka,sosai Salma take taya Ammabuwa rainon Maheer. Idan aka goya mata shi bata sauke shi har sai ya yi kukan yunwa,ya na shan mama za ta ce a goya mata shi,sam bata gajiya da É—awainiyarsa.

Layuzah na matuƙar jin daɗin zama da Salma,domin yarinya ce ita mai matuƙar natsuwa da hankali tare da sanin ya kamata. Satin Gwaggo Kande biyu a Makka ta dawo cike da tsaraba mai tarin yawa. Domin kuwa duk wasu ƴan kuɗaɗen da za ta ci abinci da Abdulwahab ya bata bata saki jiki ta kashe su ba,Salma kanta sai da ta samu riguna da takalma bakwai. Sannan ta yi wa mutanen Kura tsaraba musamman Malam Bala da dangin mahaifan Abdulwahab na uwa da uba. Kwanan ta uku ta kafe sai ta tafi Kura,kuma da Salma za ta tafi,domin amana ce Atine ta bata,ba za ta rabu da ita ba sai aure ko mutuwa. Salma na jin maganar aure kunya ta kama ta,sai ta dena rikicin ba za ta bi Gwaggo Kande ba ta wuce ta fara haɗa kayanta. Washegari da sassafe Abdulwahab ya saka su a mota suka koma Kura.

Gwaggo Kande na tafiya Mahaifiyar Ammabuwa ta matsa akan sai Ammabuwa ta koma gida wanka,domin ta gano babu wani babba da ke yi mata wanka shirmen su kawai suke yi ita da Layuzah a gidan. A daidai wannan gaɓar Layuzah ta shiga damuwa saboda tafiyar Ammabuwa,sai take jin gidan shiru babu Salma,babu Maheer,ga Ammabuwa ƙawa kuma aminiyarta ta koma gidan iyayenta. Wannan damuwar da ta shiga ne ya sanya Abdulwahab bata lokacinsa sosai,har ya zamana watarana ma baya fita aiki ko kasuwa, Mudassir ne kawai yake tafiya ya ji da komai. Ana haka Layuzah ta fara yawan cin abinci da kwaɗayin tsiya,bata yin wani ciwon kuma bata amai ballantana zazzaɓi. Gaba ɗaya basu gane abinda ke faruwa da ita ba har sai da Ammabuwa ta gama wankan gida,danginta suka dawo da ita cikin kwalliya irin ta Buzaye da kayan gara irin na al'ada da ake yi a duk haihuwar fari. A lokacin da za su tafi ne wata Innar Ammabuwa ta ke cewa.

"To Gwaggon Maheer kema Allah Ya sauke ki lafiya. Ku ci gaba da haƙuri da junanku domin zaman ku lafiya na faranta mana rai mu iyayenku. Allah Ya yi muku albarka."

Da haka suka tattara suka tafi suka bar Ammabuwa cikin murnar dawowa kusa da aminiyarta. Bayan sun raka su sun dawo ne Ammabuwa ta ce.

"Ƴar'uwa wai meye sirrin ne na ga kin yi wani irin kyau sai kace yanzu ne kuke cin amarci ke da Yayana?"

Murmushi Layuzah ta yi ta ce.

"Ni kai na ban san me yake damu na ba,kin ganni nan babu abinda na saka a gaba da ya wuce kwaÉ—ayi da yawan cin abinci, sai kuma yawan bacci kamar wata kasa."

"To ko dai maganar Innahta ce za ta zamo gaskiya Maheer zai samu ƙani ko ƙanwa?"

Kunya ce ta kama Layuzah ta ce.

"Habaa babu wani ciki da nake É—auke da shi ni dai. Da duk ban samu ba sai yanzu?"

"Iyi mana,ai Baban Mudassir ya bani labari irin soyayyar da kuke zubawa a gidan nan kamar wasu tattabaru."

Dariya kawai Layuzah ta yi, ta wuce ciki ta ɗakkowa Ammabuwa abicin da ta dafa mata na musamman. Nan suka zauna su na ta hira Layuzah na riƙe da Maheer a cinyarta ta na jin son yaron na ƙaruwa a cikin ranta saboda kyau da girman da ya sake yi.

Su Layuzah basu tashi sanin tana dauke da ciki ba har sai da cikinta ya kai watanni huɗu a duniya. Ranar da ta fara jin motsi ta gigice ta gigita kowa a gidan. A wannan ranar kuwa Abdulwahab baya gari tafiya ta kama su daga wajen aikinsa. Mudassir ne ya ɗauke ta a kan babur ya kai ta asibiti aka duba ta. Bayan gwaje-gwaje likita ya tabbatar musu da cewar ta na ɗauke da juna biyu har na tsawon watanni huɗu. Murna sosai Mudassir ya dinga yi,ita kuwa Layuzah sai ta ji kunyar Yayan nata ta kama ta har ta ƙi hawa babur ɗinsa sai da ya samo mata bus ta hau aka mayar da ita Ƴankaba. Ta na zuwa gida ta tarar da Mudassir ya riga ta zuwa har ya sanar da Ammabuwa. A ƙofar gida ta tarar da Ammabuwa goye da Maheer ta na ta washe baki. Hijabi ta sa ta rufe fuskarta saboda kunyar da ta ke ji. A haka suka shige gida Ammabuwa na nan nan da ita. Har so take ta ji Layuzah na buƙatar wani abu ta gabatar mata da shi. Bayan kwana biyu Abdulwahab ya dawo daga tafiya aka sanar da shi wannan labarin mai daɗi,farinciki ya dinga yi ya na kumawa tare da godiya ga Allah da ya yi masa wannan kyautar.

Sosai mutanen nan uku suke nuna wa Layuzah kulawa har watarana ta kan rasa bakin yi musu godiya. Idan Mudassir na tsokanar Abdulwahab sai ya ce.

"Ni dai na shiga uku da surukin zamani,wai kai ba ka jin kunya ta ne don Allah?"

"Ina fa zan ji kunyar ka tinda dai ni ba a suruki na É—auke ka ba. Kai É—in abokina ne,aminina ne kuma É—an'uwana. Dan haka babu wata kunya a tsakaninmu."

Abdulwahab na jin daÉ—i a ransa idan ya ji Mudassir na bashi babban matsayi a ransa.

Ana haka cikin Layuzah ya shiga watan haihuwa,gashi Abdulwahab ya na so ya yi tafiya ƙasar Ghana saboda shigar da wasu kaya da suke son su yi. Da jin haka sai Layuzah ta hau kuka ta na faɗin.

"Gaskiya babu inda za ka tafi ka barmu ni da abinda ke ciki na,ko kana son ka tafi ka barni wajen haihuwa na mutu baka nan?"

Da sauri Abdulwahab ya kalle ta ya na jin zuciyarsa na tsananta bugawa. A duniya baya son ya ji Layuzah na kiran mutuwa ko rabuwa a tsakaninsu. Dan haka cike da rarrashi ya ce.

"Ki kwantar da hankalinki,babu inda zan je, bana Yayanki zan tura Ghana duk da baya son tafiye-tafiye,na rasa me yake jin tsoro,amma dai a wannan karon dole shi zai je,idan ba haka ba kuma sai dai mu haƙura da kai kayan gaba ɗaya,tinda ke kin ƙi amincewa na tafi."

Haka suka dinga hira Layuzah na sake jaddada wa Abdulwahab rashin son tafiyar da zai yi. Lokacin sallar Isha'i na yi ya tafi ya yi alwala ya wuce masallaci. Bayan an idar da sallah su na dawowa daga masallaci Abdulwahab ya kawo wa Mudassir buƙatarsa na tafiya ƙasar Ghana kai kaya da yake son ya yi. Ba dan Mudassir ya so ba kan dole ya amince da tafiyar. Su na zuwa gida ya dinga yi wa Layuzah masifa ya na cewa duk laifinta ne ta sa mijinta zai aika shi wata uwa duniyar. Dariya kawai ta yi ta ci gaba da yi wa Maheer wasa. Ammabuwa kuwa sai ta ce.

"To ai gwanda ka yi tafiyar ma ko mutum ya ɗan huta na wasu kwanakin. A yi mutum kullum ya na gida ko tafiyar kwana ɗaya baka taɓa yi ba fa."

Ƙanƙance ido Mudassir ya yi yana kallon Ammabuwa ya ce.
Chapter 18 · 0% Book details