Sashe 16
Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fuskarsa da ya É—aure ya saki ya hau washe baki. Kwanon abincinsa ya ja gabansa ya yanko loma sannan ya ce.
"Ki je ki fara shirya yarinya lokacin aurenta ya yi."
Guɗa Innar Suwaiba ta kama hanci za ta zabga, Malam Bala ya riƙe mata hannun cikin sauri ya ce.
"Matsalata da ke hauka. Yanzu idan wani ya ji ki na guÉ—a ai sai a zo jin bahasi,daga nan shikenan kuma kin rusa mana duk wani tanadi. Dan na tabbata yaron nan sai an yi masa Æ´an dabaru zai yi mana biyayya,mugun taurin kai ne da shi kamar dutsen wuta."
Baki Innar Suwaiba ta kama ta na dariya ta fita daga ɗakin ta koma nata ɗakin. Zaune ta tarar da ƴar tata da ta gama yi musu laɓe ta ji komai,amma sai ta nuna sam bata san me yake faruwa ba. Ta na ganin mahaifiyarta sai ta miƙe tsaye cike da damuwar ƙarya ta na tambayarta yanda suka yi da Babanta. Nan Innah ta zauna ta sanar da ita komai cike da murna. Ihun murna Suwaiba ta sanya ta na ta tsalle tare da zayyano wa mahaifiyarta irin jin daɗin da za su samu idan har ta auri Abdulwahab. A wannan daren da ƙyar Suwaiba ta samu bacci ya ɗauke ta tsabar murna.
Washegari da sassafe sai ga Suwaiba an yi ciki tsami waje fes-fes an sha kwalliya kamar mai zuwa gidan biki. Ta na gamawa ta samu waje ta yi zamanta a É—aki kunnuwanta na baje a tsakar gida ta na jin mai shiga da kuma mai fita.
Da misalin takwas da rabi na safiya Abdulwahab ya shigo gidan cikin adonsa irin na ƴan birnin wancan lokaci. Kai tsaye ƙofar ɗakin Malam Bala ya nufa ya samu waje ya zauna a saman tabarmar da yake shimfiɗawa ya zauna da safe ya karya;tare da karɓar gaisuwar yaransa. Cike da ladabi Abdulwahab ya gaishe da Malam Bala. Malam Bala ma washe baki ya yi tare da jimƙe hannun Abdulwahab a nasa ya na amsa gaisuwar kamar zai kwanta a ƙasa. Su na cikin gaisawa. Suwaiba ta fito cikin kwalliyar da ke ba wa Abdulwahab dariya ta na karairaya ta zo gabansa ta dire kwanon sha. Cike da jin kunyarsa ta kashe murya ta gaida shi. Amsa wa ya yi yana binta da kallo ya na dariyar gayunta. Ita da Malam Bala sai suka ɗauki hakan a matsayin ƙyasawar Abdulwahabu. Ko buɗe kwanon be yi ba ya nufi ɗakin Gwaggo Kande inda yake jiyo kukan Salma ta na faɗin ita dai ba za ta je makaranta ba Baba ya hana. Ya na shiga ɗakin Salma ta nufe shi ta na shassheƙar kuka. Zaunar da ita ya yi a saman cinyarsa ya na shafa kitsonta da ya kwanta a kafaɗunta ya ce.
"Ai tun jiya mu ka yi magana da Baba ya amince ki je,ashe bai sanar da ku ba Gwaggo?"
"Humm ka san Salma yarinya ce mai biyayya kamar mahaifiyarku. Tinda ta ji ya ce baya so ta tsiri wannan iya shegen. Amma tinda ta ce ba za ta je ba a bada kayan nata a amshe jakar duk a bayar. Wannan kayan ƙwalamar da ka siyo mata ma sadaka zan yi da su,dan babu amfanin ajiye wa."
Salma na jin haka ta wuce ta hau saka uniform ta rataya jaka ta fice ta bar É—akin ba tare da ta ce musu komai ba. Dariya Abdulwahab ya yi ya ce.
"Ke ce maganin Æ´ar gidan naki Gwaggo."
"Ahaf ai maganin biri karen maguzawa Abdulwahab."
Gaisawa suka yi ta jawo masa abincinsa sannan ta fita daga ɗakin dan zuwa yin wasu ayyukan. Ta na fita Malam Bala ya kira ta ya ce ita da Innar Suwaiba su je ya na son yin magana da su. Babu ɓata lokaci ta ajiye ƙwaryar dusar awaki ta wuce ɗakin Malam ta zauna ta na jiransa. Ba ta jima da zama ba Innar Suwaiba da Malam Bala suka shiga ɗakin. Su na zama Malam ya yi gyaran murya ya ce.
"Ba wani abu bane ya sa na ce ku zo turakata dikan ku face ina so na sanar da ku wani abun farinciki da ya same mu. Kande dama ke ce baki san me yake faruwa ba,dan ita Babar su Suwaiba ta san komai. Ina so ki taya mu murna bana dai Allah Ya yanke wa Suwaiba zaman gida za ta yi aure."
Murmushi Kande ta yi ta ce.
"Barka barka Hasiye Allah Ya sanya alkhairi da albarka ya nuna mana lokacin da rai da lafiya."
Ta na faɗin haka ta ja bakinta ta yi shiru. A ƙufule Innar Suwaiba ta ce.
"Shikenan abinda za ki ce Yaya? Wai ni sai yaushe za ki rage wannan zafin kishin naki akai na ne? Ai a ƙalla kin taya ni murna Allah Ya yanke wa ƴata wahalar zaman gida ko?"
Cike da mamaki Kande ta ce.
"Ah ah ni Kandala É—iyar Mamman yau na ga abinda ya fi zare tsayi? To in banda abinki ai ta Malam bata wuce amin ko? Me kuma kike so na yi bayan addu'ar da na yi ta sanya albarka?"
Ƙwafa kawai Innar Suwaiba ta yi domin bata so su yi faɗa ta hasala Kande ta ƙi haɗin auren. Malam Bala kuwa ya na ganin haka sai ya ce.
"To in banda abunki Kande ya za ki tsaya sa-in-sa da surukarki?"
Kallon sa Kande ta yi cikin rashin fahimta ta ce.
"Surukata kuma Malam? Ta ina Hasiye ta zama surkar tawa?"
Washe baki suka yi a tare shi da Innar Suwaiba kafin ya ce.
"To ai Abdulwahabu shi ne angon. Kin ga kuwa idan da kara ai ke kakar amarya ce."
Miƙewa Kande ta yi ta na tafa hannayenta tare da yin salati,sai da ta gama tsaf sannan ta kalle su ta ce.
"Lallai ma Hasiye baki da kunya. Kin manta irin wulaƙanci da cin kashin da kike yi min a gidan nan saboda ni ban haihu ba? Wanne irin gori da tozarci ne baki min ba akan Suwaiba da ƙannenta? Har ta kai ta kawo gaba ɗaya yaran nan sun raina ni. Shi ne yanzu dan kun ga yaro ya yi ƙumbar susa kuke so ku bashi ƴarku ya aura,to ni dai babu ruwana a wannan zance,idan yana so a yi aure,idan baya so babu wanda ya isa ya yi masa auren dole."
Da sauri Malam ya kashe ta ya na faÉ—in.
"Haram ba bashi ita za mu yi ba,ni da kai na na fuskanci saƙon soyayyar da yake aika mata ta idanuwansa. Shi yasa na yanke shawarar haɗa su aure tinda itama ta na son sa."
"Au haka abun yake? To Allah Ya bada sa'a Ya sanya albarka."
Kande na fita daga ɗakin sai ta ƙwala wa Abdulwahab kira ta ce ya je Malam na neman sa,dan ta san halin mutanen nata muddin bata yi haka da wuri ba suka zauna waje ɗaya da Abdulwahab tsaf za su ce ita ta hana auren. Gaban Hasiye ne ya yanke ya faɗi domin ba ta haka ta so ya san da maganar ba. Dake wa ta yi ta gyara zama a turakar Malam Bala har Abdulwahab ya je ya zauna a tabarmar ƙofar ɗakin.
Wani irin kwarjini Abdulwahab ya yi musu,sai dai son abun duniya ya rufe musu ido. Dan haka Malam Bala ne ya fara gabatarwa da Abdulwahab buƙatarsu na auren Suwaiba. Da sauri kuma ba tare da jin nauyi ko kunya ba Abdulwahab ya ce.
"Baba ai ni ina da wadda nake so da aure har mun tattauna da Gwaggo ma akan hakan jiya. Dama ina jiran ka gama kari ne na zo maka da maganar dan har na sanar da Kawunaina da Baffanina,sun kuma amince za su zo su ɗauke ka ku je nema min auren Layuzah ƙanwar abokina da muke kasuwanci tare wato Mudassir."
A guje Suwaiba ta fito daga ɗaki ta na gursheƙen kuka duk hodar ta ta caɓe domin maka ta ta yi da kyau,ga baƙin kwalli duk ya dame mata fuska. Kallonta Abdulwahab ya yi ya ji dariya ta zo masa. Malam Bala da ya ɗaga labule ya ce.
"To idan baka son Suwaibar murmushin uban me kake yi mata É—azu da ta kawo maka kunu? Sannan yanzu ma dariyar me kake yi mata?"
Ƙunshe dariyarsa Abdulwahab ya yi ya ce.
"Baba wannan kwalliyar ta fuskarta kaÉ—ai ta isa ta firgita duk wani wanda ya zo neman aurenta ai."
Baki Hasiye da Malam Bala suka buɗe suna kallon Abdulwahab da ke ci gaba da dariyar kukan Suwaiba. Dawowar Kande daka wajen awakinta kenan ta ga yanda Suwaiba ke mulmula a ƙasa ta na kurma ihu tare da faɗin ta shiga uku ta lalace. Da sauri ta nufe ta za ta ɗaga ta Hasiye ta riga ta ta ɗaga ƴarta ta na sharar kwalla ta ce.
"Ni dama na jima da sanin ai ba kya ƙaunata ni da ƴaƴana a gidan nan,shi yasa kika hana Abdulwahab auren Suwaiba. To ki je ke da Allah,kuma muna nan zaune Suwaiba za ta auri wanda ya dame Abdulwahab arziƙi da kyau da nasaba."
"Ba na yi mata baƙin cikin samun nagari,domin ni ma ina bin dare na yi mata addu'ar samun miji na gari inda za ta huta wani nata ma ya huta;wanda bana jin a matsayinki na uwarta kin taɓa bin dare kin yi sallah kin roƙar mata miji na gari. Tinda ku dai a kullum baku da buri sai auren mai kuɗi."
Cike da takaicin wulaƙancin da Abdulwahab ya yi musu Malam Bala ya ce.
"Ke É—in ma ai auren kuÉ—in ki kai da ni. Amma dai komai ya wuce,tinda ya ce baya son jinina ya je can ya auri duk wadda ta yi masa,amma ba da yawu na ba."
Haƙuri Abdulwahab ya dinga ba wa Malam Bala amma sam ya ƙi haƙura ya riƙe shi a ransa. Daga ƙarshe sai ya shuri takalmansa ya bar gidan. Ya na fita ya hau yayata cewa duk alkhairin da ya yi wa Abdulwahab da ƙanwarsa amma ya ce zai haɗa shi aure da Suwaiba ya baɗa masa kasa a ido. Nan take mutane ƴan bani na iya suka hau zagin Abdulwahab su na tsine wa dukiyar da ya fara tarawa albarka.