← Book details Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 30

Sashe 24

Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Labule Salma ta ɗaga ta leƙa kanta ta ce.

"Sai dai na ga alkhairi da yardar Allah."

A zuciye Hasiye ta ɗauki plate ɗin tasar da ke kusa da ita ta jefi  Salma da shi ta na zagin ta. Salma kuwa ɗaki ta koma ta na jin faɗan da Gwaggo Kande ke yi mata akan ta dena biye wa Hasiye kafin ta sake ƙulla mata wani sharrin. Hijabinta ta ɗauka ta sa ta tada sallah,ta na idarwa ta yi wurgi da hijabin ta kwanta tare da juya wa Gwaggo Kande baya ta na tunanin makomarta. Gwaggo Kande kuwa sai ta zuba wa bayan nata ido kamar mai karantar wani abun a tattare da yarinyar.

Su na nan zaune shiru Malam Bala ya shiga gidan hannunsa riƙe da wata leda sai nason maiƙo take yi. Kai tsaye ɗakin Gwaggo Kande ya shiga ya samu gefen gado ya zaune ya na washe baki ya ce.

"Ohh Kande ashe haka yaron nan Abdulwahabu ya bunƙasa ya tunbatsa a Kanon? Ai ni yau na ga abun arziƙi Kande,yaron nan haka ya sa aka kawo mana abinci da nama zuƙu-zuƙu a ciki. Da zan tafi ya jimƙo kuɗi a aljihunsa ya yi min hasafi,a ciki na yi na motar dawowa na kuma siyo miki wannan kilishin ki ɗan taɓa.

A sheƙe Kande ta kalli mijin nata da take mugun ganin baƙinsa a yanzu ta ce.

"Idan ka gama cinyewa sai ka ƙara gaba,in kuma a can ɗakinka ko na makwaɗaiciyar da ɗoraka a keken ɓera za ka ci ka tashi tun yanzu ka ƙara gaba bana buƙatar komai daga wajenka."

Cike da takaici Malam Bala ya kalli Kande ya miƙe tsaye ya ce.

"Ke fa na ga alama a ƴan kwanakin nan ba a abun arziƙi da ke,amma wannan bai dame ni ba,taimakon da na sa a gaba ba zan fasa ba,zan ci gaba da yi na ceto bawan Allah'n da bai taɓa aure ba a rayuwarsa."

Ledar hannunsa ya É—auka ya nufi inda Salma ke kwance ta na binsa da kallo idanuwanta na zubar da hawaye. Baki ya washe ya ce mata.

"Ƴar salamemen Baba ga wannan ki motsa bakinki ko? Na kula a kwanakin nan kin saba da cin daɗi a gidan Yayanki."

Salma dai ido ta zuba masa bata motsa ba,kuma bata amsa ba. Ganin haka sai Malam Bala ya ajiye ledar zai fita. Har ya kama labule ya É—aga ya tsaya ya kalli Gwaggo Kande ya ce.

"A shirya ta zuwa dare Rabi'u zai zo ya ga amaryarsa su ɗan tattauna ya ji ko akwai wani shagalin da take son ta gabatar,da yardar Allah gobe za a kai ta ɗakinta itama kamar yanda aka yi wa ƴar'uwarta Samira. Ai cewa ya yi ma kada mu damu da siyan kayan gado duk ya zuba mata ɗazu,shi dai matarsa kawai yake da buƙata ba komai ba."

Murmushin takaici ne ya ƙwacewa Kande ta ce.

"An zo wajen. Na tabbata siyawa Salma kayan ɗaki na daga cikin abinda ke damunka a kaf faɗin duniyar nan Malam. A al'dance idan mutum ya riƙe yarinya aka tashi aurenta shi ne zai yi mata kayan ɗaki,to kai gashi ba za ka iya cire kuɗi ka yi wa Salma kayan ɗaki ba. Da ka sani Malam da baka jefa rayuwar ta a cikin haɗari ba saboda kayan ɗaki. Ko ka manta har yanzu ɗan'uwanta na juya mata dukiyarta? Ka manta shi kanshi yana da arziƙin da ba zai bari ka sha wahala ba a duk lokacin da bikin Salma ya tashi? Malam...."

Cike da borin kunya Malam Bala ya É—aga wa Kande hannu ya ce.

"Dakata Kande! Wai kina nufin ni Malam Bala Maji Daɗin Manoman garin Kura ni ne zan kasa yi wa Salma kayan ɗaki? To albishirinki,har kuɗin kayan gado na bada,da jin labarin zan kai na kujeru Rabi'un da kansa ya zo ya ce kada na yi ya riga ya yi. Yanzu gobe zan je na karɓi kuɗin gadona a yi wata hidimar da su. Wai me kika ɗauke ni ne Kande?"

"Marar riƙon amana da tausayin marainiya. Malam na tabbata da ka kai kuɗin gadon nan kamar yanda ka ce to da ka karɓo su yanzu,dan kai ba mutumin da yake wasa da dukiyarsa bace musamman idan ya ji banza ta faɗi."

Cike da borin kunya Malam Bala ya dinga faɗa,ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Sosai ran Kande ya ɓaci dan haka sai ta biye masa suka dinga musayar yawu har sai da Salma ta ƙwalla ƙara ta na kuka tana basu haƙuri. Cikin kuka ta durƙusa a gaban Kande da ke hawaye ta na masifa ta ce.

"Don Allah Gwaggo ki dena sa'insa da Baba domin ba halinki bane,tinda nake a gidan nan ban taɓa ji ya faɗa kin mayar masa ba. Idan har akai na ne kike faɗa da shi na yi alƙawarin yi wa Baba biyayya akan duk wanda ya aura min. Don Allah ku dena faɗa bana so,zuciyata zafi take yi min bana so."

Kuka sosai Salma take yi numfashinta na yankewa kamar mai cutar asma. Duk taurin rai irin na Malam Bala sai da jikinsa ya yi sanyi,da sauri ya ja labule ya bar ɗakin. A tsakar gida ya tarar da Hasiye ta na kaye-kayen kwanika,da dikkan alamu sana'ar tata ta laɓe ta yi musu,jin fitowarsa ne ya sa ta bar wajen ta hau kwashe kwanuka. Malam Bala na fita Kande ta rungume Salma a jikinta ta ce.

"In Sha Allahu ba za ki auri mutumin da ya isa yin jika da ke ba. Za ki girma ki auri saurayi kyakkyawa kamar yanda nake yi miki fata a koda yaushe. Baffanki Aƙilu zai je Kano gobe ya samu Yayanki ya sanar da shi duk abinda ke faruwa."

Girgiza kai Salma ta yi,dan jikinta na bata wannan auren fa ya gama ɗauruwa kenan sai ta je gidan Malam Rabi'u ko tana so ko bata so. Hana ta magana Kande ta yi ta ce ta je ta kwanta ta huta,dan ta ji jikinta ya ɗauki zafi,alamar zazzaɓi na sanɗarta.

Har su Kande suka yi sallar Isha'i basu yi wani shirin tarbar Malam Rabi'u ba. A ɓangaren Hasiye kuwa tini ta haɗa farau-farau a kwanon shanta sabo dal,sannan ta fito da tabarmarta sabuwa ta jingine ta na jiran zuwan baƙon nasu. Har ɗakin Kande ta shiga da sallama ta na washe baki kamar wawiya. Cike da mamaki Kande da Salma suka ɗaga kai suna kallon matar da ko ciwo Kande take yi bata shiga ta gaishe ta,ballantana ta yi mata sannu. Duk lokacin kuwa da ta ɗaga labulen ɗakin Kande to fa masifa da bala'i ne ya kai ta ba arziƙi ba.

Zama ta yi ta na dariya ta ce.

"Ah ah Ƴata salma har yanzu ki na nan kwance baki shirya ba bayan Babanku ya faɗa miki za ki yi baƙo anjima kaɗan?"

Ko motsi Salman bata yi ba ballantana ta tanka mata. Kande ce ta gaji da jin nacin da Hasiye take yi wa Salma ta ce.

"Kin ga kanwa uwar gami don Allah tashi ki bani waje,ki je can ki tarbi baƙon tinda dama ke kika haɗa duk wani tuggu da makircin da auren ya ƙullu. Ban san menene ribar ki ba na yin wannan zalunci,amma Allah Ya fiki,kuma a gobe ɗan'uwanta zai zo da jami'an tsaro dan a kama duk wani mai hannu a cikin wannan auren rashin ƴancin da kuka ƙulla."

Cikin Hasiye ne ya kaɗa har ƙarar ta ziyarci kunnuwansu Kande. Cike da tashin hankalin jin an ambaci hukuma a lamarin ta hau rantsuwa tana kumawa akan bata da hannu a haɗin auren Salma da Rabi'u. Kafaɗa Kande ta ɗaga ta ce.

"Jami'an tsaro ne kawai za su tabbatar da hakan idan sun zo."

Jiki na rawa Hasiye ta bar É—akin ta wuce nata tana ta safa da marwa. Cike da tashin hankali take jiran Malam Bala ya dawo su san abinyi. Sai dai abun takaicin Malam Bala na zuwa Hasiye ta labarta masa duk abinda Kande ta ce,sai ya ja tsaki ya ce.

"Da yake an faÉ—a mata jami'an tsaron mahaukata ne ba sa bincike ko? Ai auren nan ya riga ya É—auru kenan Hasiye,dan haka ki ma dena jin tsoron kowa da komai."

Kafin Hasiye ta buÉ—e baki ta ce wani abu,sallamar yaro ta karaÉ—e tsakar gidan. Mairo ce ta amsa tare da ce wa yaron.

"Kai Tsalha maye ka ishi mutane da sallama?"

Baki yaron ya murguÉ—a mata kafin ya ce.

"Malam Rabi'u ne ya ce na yi masa sallama da Babanku."

Da sauri Malam Bala ya fito ya na gyara rawaninsa ya ce.

"Ka ce masa ya shigo zauren gata nan fitowa."

ÆŠakin Kande ya nufa ya É—age labule ya ce.

"Salma ki na ina? Fito ga angonki ya iso."

Cikin sauri Kande ta ce.

"Malam na fa faÉ—a maka babu inda Salma za ta je."

Ganin za su fara faɗa sai salma ta bi ta bayan Malam ta fita sanye da hijabinta. Hasiye da ta ci burin shimfiɗawa Malam Rabi'u sabuwar tabarma sannan ta bashi farau-farau na jin fitar Salma ta lafe a ɗaki saboda tsoron jami'an tsaro. A zauren gidan Salma ta tarar da Malam Rabi'u ya sha sabuwar shaddar sa fara tas sai sheki take yi. Durƙusawa ta yi har ƙasa ta gaishe shi cikin ladabi da girmamawa. Murmushi Malam Rabi'u ya sakar mata wanda ya fitar da tsantsar kyawun fuskarsa. Sosai Malam Rabi'u yake da kyawun fasali,domin kuwa a zamanin samartakarsa ya na daga cikin kyawawan samarin garin Kura. Shi yasa ma jinkirin aurensa ya janyo raɗe-raɗin cewa aljana ce ta aure shi a lokacin da suke yawan shiga daji farauta da iyo.

Gaisuwarta Malam Rabi'u ya amsa sannan ya gyara tsayuwarsa ya na kallon yarinyar dake gabansa cike da ƙaunarta a ransa. Sai da ya yi gyaran murya sannan ya ce.
Chapter 24 · 0% Book details