Sashe 11
Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Haba Aabidah ya kike magana irin wannan kamar an ce miki ko da Khadijatou ta dawo cikin rayuwar Aabid zai iya rayuwa babu ke? Ina son ki dinga tunawa da mun riga da mun kama Aabid kamu na har abada. Aabid ba zai taɓa ganin Khadijatou ba ballantana tarin sihirin da muka yi musu ya warware. Ke ina mai tabbatar maki da cewa ko da sun tuna da juna ba zamu taɓa yarda su haɗu ba;domin haɗuwarsu tafi tunawa da junansu hatsari a wajen mu."
Wani sabon kuka Aabidah ta rushe da shi sannan ta ce.
"Why me? Why meeee? Me yasa sai da nutsuwa da kwanciyar hankali ta same ni;ariziƙi na ya nunku,ina zaune da mijina lafiya wannan matsalolin za su kunno min kai? Ya Allah ka sake ara min dama ka nesanta Khadijatou da Mijina,Ya Allah ka sake raba tsakaninsu rabuwa ta har abada......
MUGUWAR MACE.
NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨âœï¸
*Za ku iya fara payment É—in littafin MUGUWAR MACE da yake akan farashin 1k ta 9031416423,ku tura shaidar biya ta 09031416423.*
PAGE 9.
Sai da Innaji ta nisa sannan ta miƙe tsaye ta mayar da zumar da ta ɗakko mazauninta. Cike da mutuwar jiki ta kalli Aabidah dake gunjin kuka ta ce.
"To yanzu ya za ki yi da maganar Boka da ya ce ki janyo wannan yaron Maheer jikinki?"
A hasale Aabidah ta ce.
"Wai ke Innaji me yasa wani lokacin sai ki dinga yin magana ba kya tunani ne? Ni yanzu ina ruwana da wani Maheer? Ai sawun giwa ya take na raƙumi Innaji, yanzu babbar damuwa ta a duniya bata wuce na san inda Khadijatou take ba,ina so na nemo ta da kaina kafin Aabii ya ganta. Ina so na kashe ta har lahira kowa ma ya huta. Wannan karon ba zan yi kuskure ba wajen aikata inda ba za ta dawo cikin rayuwarmu ba har abada."
Labule Jauharah ta buɗe ta na kallon su Aabidah. A razane Aabidah ta kai dubanta wajen da ta ji motsi,ido huɗu suka yi da Jauharah da ke a buge sai lumshe idanuwa take yi kamar mai jin bacci. Tsaki Aabidah ta ja mai ƙarfi ta kalli Innaji ta ce.
"Yaushe wannan yarinyar ta dawo gida daga yawon dandin da ta tafi?"
Hannu Innaji ta ware tana kyaɓe baki ta ce.
"Yanda kika ganta haka na ganta,dan ba a gidan nan ta kwana ba. Ai ita da wancan da'un ba za ki taɓa sanin lokacin shigarsu ba ballantana fitar su. Ke! yaushe kika dawo gidan?"
Cikin tafiyar Æ´an maye Jauharah ta isa kujera mafi kusa da ita ta zauna tana lumshe idanuwa. Cikin muryarta mai kama da ta matan da suka tsufa suna busa sigari ta ce.
"Yanzu Mine ta ajiye ni ta tafi. Babbar Yayaaa na ji kina wata magana akan waccan mujiyar, a ina take na aika yara a kawar miki da ita cikin sirri? Kin san yanda kike bani farinciki dole ne nima na rama wa kura a niyarta."
Tsaki Aabidah ta ja mai tsawo kafin ta ce.
"A hakan ne za ki yi min abinda zan mora Jauharah? Allah ya wadaran rayuwar da kika jefa kanki a ciki. Ke kan ki baki taimaki kanki ba ballantana ki taimake ni. Na kashe kuɗaɗena a banza akan ku,na ɓata lokaci na da energy na duk akan ku,daga ƙarshe kun zamo marasa amfani. Tashi ki bar nan kafin na huce takaicin dake cikin raina akan ki."
Tsuke baki Jauharah ta yi ta tashi tana tangaɗi ta shige ɗakinta ta rufe ƙofa. Tsaki Aabidah ta ja ta dafe kanta tana ci gaba da kukanta wanda take jin sanyi a ranta a duk saukar hawaye ɗaya daga idanuwanta. A wannan rana a gidansu ta kai azahar saboda tsoron kada ta koma gida Aabid ya sake bijiro da zancen Khadijatou ba ta jin zuciyarta za ta iya ɗaukan jin kalmar sunan babbar maƙiyyarta a bakin mutumin da ta fi so sama da kowa a rayuwarta. A duk bugawar sa'a ta agogo sai gaban Aabidah ya faɗi. Ta kasa ci ta kasa sha saboda damuwa da zullumi. Innaji kuwa Laure ta sa ta dafa mata abinci mai rai da lafiya da naman kaza ta ci ta ƙoshi ta kora da lemo. Ganin yanda Innaji ke warkajaminta ba tare da jimamin halin da Aabidah ke ciki bane ya sanya Aabidahn ɗaukan makullin motarta da mayafinta ta shuri takalmanta babu ko sallama ta bar gidan. Kai tsaye gidan ƙawarta kuma aminiyar cin mushenta ta nufa. Tin daga bakin gate mai gadi ya san yau Hajiya Aabidah bata cikin hayyacinta;duba da irin tuƙin da take yi. A gaggauce ta kashe motarta ta buɗe ta shiga gidan Hajiya Zaitunah. Zaune ta ga Hajiyan ita da yaranta suna kallo. Kallo ɗaya yaran suka yi wa Aabidah suka kawar da kawunansu suka ci gaba da kallon su, yara ne da aka sangarta suke jin kansu,dan haka ko gaisuwa bata haɗa su da kowa sai wanda suka ga dama. Ganin irin halin da Aabidah ke ciki ne ya sanya Hajiya Zaitunah wadda ta girmi Aabidah da shekaru takwas a duniya miƙe wa ta bi bayanta zuwa ɗakinta. Su na shiga Aabidah ta zauna a bakin gado ta rushe da kuka. Cike da matsananciyar damuwa Hajiya Zaitunah ta dafa bayan Aabidah ta ce.
"Ah ah Ƙawata lafiya kike irin wannan kukan? Me ya samu Aabii ɗin naki? Ina fatan dai ba sakin...."
"Allah Ya kiyaye Aabii ya sake ni. Ai ni da shi mutuwa ce za ta raba mu,walau ya binne ni ko kuma ni na binne shi. Ƙawata matsala ce mai girma ta taso min wadda muka jima da haƙa rami mai zurfi muka binne. Sai kuma gashi ta ɓullo a lokacin da bamu yi zato ko tsammani ba."
Waro ido Hajiya Zaitunah ta yi tare da dafe ƙirji ta ce.
"Kar dai ki ce min wannan mayyar ta dawo cikin rayuwarku?"
"Wai ke me yasa ba kya faɗan alkhairi ne? In dai boka na raye na yi imanin Khadijatou ba za ta taɓa dawowa cikin rayuwarmu ba."
"To meye zai É—aga miki hankali haka bayan kin san ba dawowa za ta yi ba? Ko dai kema kin fara fuskantar irin matsalar da nake fuskanta ne?"
Ajiyar zuciya Aabidah ta sauke tare da goge majinar da ke shirin gangarowa a hancinta da tissue ɗin dake gefen gadon Hajiya Zaitunah. Cike da damuwa ta labarta wa ƙawar tata abinda ke faruwa. Salati Hajiya Zaitunah ta yi sannan ta ce.
"To ai wannan maganar taki daidai take da dawowar Khadijatou cikin rayuwarku Aabidah. Abu ne fa da muka riga muka sani amma muke take sanin,shi asiri lokaci ne da shi komai daɗewarsa a jikin bawa. Idan har kika ga bai karye ba to fa mutumin da aka yi wa asirin ya mutu,ballantana Khadijatoun da na sani mai taurin rai ce da kafiya,kada fa ki manta abubuwan da muka ƙulla mata a baya amma yarinyar nan sai da ta tsallake su. Dan haka ni dai shawarar da zan baki shine,ki koma wajen Boka ya sake maimaita sihirin da aka yi a can baya,ni kuma na yi miki alƙawarin yawata wa cikin garin kano da kewaye dan taya ki neman wajen binnewa kamar yanda muka yi a wancan lokacin."
Hawaye ne suka zubo wa Aabidah a karo na babu adadi. Muryarta na rawa ta ce.
"Wannan lissafin naki duk ba mai yuwa bane inji Boka. Domin kuwa da faɗa ma muka rabu,dubi nan ɗina,shi ne ya shaƙe ni ya buga da jikin gini har sai da wajen ya kwaile."
"Da dikkan alamu hannunsa ya fara yin sanyi gaskiya shi yasa lamuranmu ke ta taɓarɓarewa. Yanzu ina so ki shirya zuwa jibi zan kai ki wajen wani sabon boka da na ji labari wajen su Zinariya dan ni ma ina buƙatar a sabunta min aikina,gaba ɗaya cikin kwanakin nan bana gane kan Dad...."
Da ƙarfi aka buɗe murfin ƙofar ɗakin da su Aabidah ke ciki. Wani ƙaƙƙarfan mutum ne ya shiga ya tsaya a bakin ƙofa yana kallon su cikin tsananin ɓacin rai. Hannu ya ɗaga yana nuna Aabidah da ta yi sororo tana kallon yanda jikin Hajiya Zaitunah ke rawa. Kallon mutumin Aabida ta sake yi wanda a baya suke sakawa aiki har da ɗebo musu ruwan sha ta ga yanda yake huci kamar wani zaki,nan da nan jikinta yayi sanyi ta miƙe ta saɓa jakarta a kafaɗa ta bar ɗakin. Kai tsaye motarta ta nufa ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi kamar wadda ta yi tseren gudu. Tana tada motar ta mai gadi ya wangale mata gate ta bar gidan a guje. A hanya babu abinda take tunawa da ya wuce sauyin da ta gani a gidan Hajiya Zaitunah. Nan take tsoro da fargabar dake cikin ranta suka nunku. Murya na rawa ta ce.
"Shin me yake faruwa a rayuwarmu ne? Lallai dole ne na samarwa kaina mafita,domin kuwa ba zan taɓa yarda Aabii ya dawo cikin hayyacinsa ba kamar yanda mijin Hajiya Zee ya dawo cikin hayyacinsa."