← Book details Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 30

Sashe 25

Muguwar Mace Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina fatan magabatanki sun sanar da ke duk abinda ya kamata ki sani game da wannan auren? Don Allah ina so ki kwantar da hankalinki,dan ni da kika ganni mace bata gabana,surutu da zarge-zarge irin na mutane ne ya jawo ra'ayina har na ji na yarda na amince zan yi aure. Sai dai kuma na samu rashin sa'a a ranar da aka je É—aura aure na a ranar matar da danginta suka ce sun fasa auren. Wannan dalilin ne ya sa Babanku tausaya min ya aura min ke. Ina fatan za ki zamo yarinya mai biyayya."

Kai kawai Salma ta É—aga masa ta ci gaba da wasa da gefen hijabinta. Murmushi ya sake yi a karo na babu adadi,wanda hakan ya zamo É—abi'arsa.

"To yanzu wanne irin taro ko shiri za ku yi ke da kwayenki?"

Shiru Salma ta yi bata ce komai ba. Kamar daga sama suka ga Mairo ta ci damara ta zo gaban Malam Rabi'u ta cake. Washe baki ta yi ta ce.

"Ai Salma ba za ta ce maka komai ba,mu dai kawayenta mu ne za mu yi party a ranar da za a kai ta da yamma."

Da jin haka sai Malam Rabi'u ya zira hannu a aljihu ya debo kudi ya ba wa Mairo ya ce.

"To gashi a sha party lafiya. Ni zan wuce sai da safe ko amarya?"

Kai Salma ta gyada masa ta juya za ta tafi. Kiranta ya yi sai ya ga Mairo ta ja ta tsaya. Hade fuska ya yi ya ce.

"Ki je ke na sallame ki ai ko?"

Washe baki ta yi tana sosa kai ta juya ta shige gida. Kai tsaye dakinsu ta shiga ta miƙawa Hasiye kudin da aka bata. Cikin sauri Hasiye ta karbe kudin har ta manta da abinda Kande ta fada mata na zuwan jami'an tsaro,sai da ta kirga su cas sannan ta zabga guda ta ce.

"Sufa dif za a kulla a yi fanke ba shikenan ba an sallami kowa?"

Dariya suka fashe da ita sannan suka ci gaba da tsara yanda komai zai kasance a washegarin.

A bangaren Salma kuwa;duk yanda Malam Rabi'u ya so ta karbi kudin da ya bata ki ta yi,daga karshe sai ta yi masa godiya ba tare da ta karbi komai daga gare shi ba ta shige cikin gida. Hakan da Salma ta yi sai ya sa Malam Rabi'u ganin mutuncinta,nan take ya tabbatar ba halinsu daya da iyayenta ba da ke ta nuna zalama da maitar abun hannunsa.

Washegari.......

MUGUWAR MACE.

NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️

PAGE 18.

Washegari da asuba har an shisshiga masallaci a wasu wuraren Salma ta tashi ta ɗauki wani abu a gefenta ta ƙudindine a rigarta,kallon Gwaggo Kande da bata rintsa ba ta yi tana saman sallaya ta na sallah,sai ta durƙusa inda suke ajiye butocinsu a bakin ƙofar ɗakin ta ɗauki butarta ta tafi banɗaki. Ta na shiga ta fito da hijabin Gwaggo Kande ƙato da ta ɓoyo a rigarta ta zumbula tare da tattare shi ya tsaya daidai tsawonta. Ƙaramar katangar banɗakin ta kama ta ɗale,ba tare da jinkiri ko tunanin komai ba ta dire ƙasa ta zura da gudu ta yi gaba abunta.

A can tsakar gida kuwa Hasiye ce zaune a saman bokitin ƙarfe sai zabga hamma take yi ta na jiran Salma ta fito daga banɗaki ta shiga. Jin shirun ya yi yawa ne ya sanya ta miƙe wa a hasale ta nufi bakin ƙofar shiga banɗakin ta ce.

"Wai in ce dai ko kashin danƙo kike yi Salma?"

Waje ta samu ta tsaya riƙe da buta ta na jijjiga jikinta cike da matsuwa. Ta jima a wajen bata ji ko da motsin ruwa ba ballantana na mutum,ba tare da ta sake yin magana ba ta leƙa banɗakin tare da haska fitila. Gani ta yi babu kowa a ciki sai butar da Salma ta shiga bayin da ita yashe a ƙasa,sawun ƙafar Salma ta bi ta ga inda suka tsaya,nan take ta fahimci abinda ya faru,sai kawai ta kurma ihu ta na kiran mutanen gidan tare da faɗin.

"Yeeee kuwa jama'a ku kawo mana agaji amarya Salma ta gudu."

Gwaggo Kande da ke lazimi na jin haka gabanta ya yi mummunan faɗuwa,da sauri ta tashi tsaye ta na riƙe da carbinta ta nufi hanyar waje. Ta na fita ta tarar da Hasiye tsaye da ɗaurin ƙirji ta na ta kwarmaton ɓatan Salma. A gigice Gwaggo Kande ta ce.

"Wai wace Salman ce ta ɓata Hasiye?"

"Yo in banda abunki Yaya Salma nawa muke da ita a gidan nan?"

Da jin haka sai Kande ta bazama cikin banɗakin da gudu tana ƙwalawa Salma kira. Tana shiga butar Salma ta gani yashe a ƙasa sai ta ɗakko butar ta fito ta na kuka,a daidai wannan lokacin ne Malam Bala ya dawo daga masallaci hannunsa riƙe da carbi ya na mui-mui da baki. Kamar jira Hasiye take ya dawo ta kalle shi tare da fasa kukan munafurci ta ce.

"Shikenan Malam yau mun shiga uku Salma ta gudu me za mu ce wa Malam Rabi'u?"

Karkace kai Malam Bala ya yi yana bin Kande da ke ta rusa kuka da kallo ya ce.

"Ban gane Salma ta gudu ba;ko dai an haɗa baki da munafukai ƴan hana ruwa gudu an ɓoye ta? To idan ma wani wajen kuka kai ta kuka ɓoye ina mai tabbatar maku da ku fito da yarinyar nan tin muna shaida junanmu da ku."

Ƙanƙance ido Kande ta yi ta ce.

"Me kake nufi da kalaman ka Malam? Za ka fita nemo min yarinya ne ko ni na tafi neman abata tinda dama ku baku da asara idan wani abu ya same ta?"

"Ke Kande ki shiga taitayinki,ina so fa ki sani ƙyale ki da kika ga ina yi kina cin karen ki babu babbaka a gidan nan ba wai tsoronki nake ji ba. Kawai ina yi ne saboda biyayyar da kike yi min a baya,amma yanzu tinda kema kin bijire mu zuba ni dake shege ka fasa. Na baki daga nan zuwa azahar a ga yarinyar nan idan ba haka ba igiyar auren ki tana lilo a gidan nan."

Ƙirji Kande ta dafe ta na zaro ido waje,daga baya ta hau nuna kanta tana faɗin.

"Malam ni za ka kalla ka ce igiyar aure na na lilo a gidan nan? Ni fa ake zalunta a gidan nan. Da na san riƙon marainiyar Allah zai dawo haka da ban karɓi amanarta ba,Salma ina kika shiga ne don girman Allah?"

Wuce Malam Bala Kande ta yi ta nufi ƙofar ɗakinta ta kulle da makulli sannan ta bazama waje neman Salma. Hasiye kuwa ji ta yi ina ma kada a ga Salman rashin ganinta ya zamo a bakin auren Kande kamar yanda Malam ya faɗa. Ta rasa me yasa duk tsawon shekarun nan da suka yi a tare take jin matsanancin kishin Kande da ƙinta a ranta.

Gida-gida Kande ta dinga bi ta na neman Salma amma babu bayani. Cikin kankanin lokaci labari ya baza gari Salma ta gudu,da misalin tara da rabi na safe Malam Rabi'u da Yayansa Malam Jamilu suka zo gidan Malam Bala dan jin karin bayani game da batan Salma. Haƙuri Malam Bala ya dinga basu yana yi musu alƙawarin nemo ta kafin ƙarfe sha biyun rana ya cika. Su na nan suna tattaunawa Baffah Aƙilu ya ƙaraso gidan hannunsa riƙe da na Salma dake ta sharɓar kuka a cikin runtumemen hijabin Gwaggo Kande. Salati Malam Bala ya sanya ya ce.

"Dama wajenka ta gudu Alhaji? Ka ganni nan yanzu nake shirin zuwa wajen Malam Mai Jigidar Bala'i ya binciko min inda yarinyar nan take a yi mata kiranye ta dawo gida. Domin kuwa aure dai an riga da an É—aura shi dole ne ta zauna a É—akin mijinta babu fashi."

Kallon Salma Baffah Aƙilu ya yi ya ce mata.

"Maza shiga gida."

Sum-sum-sum ta shige cikin gidan kamar mara gaskiya kanta a duƙe ta na satar kallon Malam Rabi'u da ya kafe ta da ido cike da tausayawa. Sosai ya ji tausayin Salma ya danne yanda yake tausaya wa kansa na zama babu aure har na tsawon wannan shekarun,babban abinda ke ƙara ɗaga masa hankali bai wuce yanda duk kyawunsa da abun hannunsa ba mata ke gudunsa. Zuciyarsa ce ta fara gasgata zargin mutane a kansa. Ya na can duniyar tunani ya ji muryoyin Malam Bala da Baffah Aƙilu a sama su na musayar yawu. Babu jimawa Gwaggo Kande ta dawo gidan ita da Kawu Sale. Kai tsaye cikin gidan Kawu Sale ya raka Gwaggo Kande da ke jin numfashinta ya na yi mata wuyar fita. Ta na shiga ta ga Salma a rakuɓe a ƙofar ɗakinta ta na gyangyaɗi Hasiye na ta kaiwa da komowa ta na kwaɓa fanke mai uban yawa a babbar roba,gefe ɗaya kuma tulin kayan miya ne a baho da naman a wata roba,sai rabin buhun shinkafa ƴar gwamnati. Waƙarta take ta yi ta habaici tare da faɗin.

"Aure dai ya riga ya ƙullu,kuma dole ne ango ya sha man amarya."

Wani kukan kura Kande ta yi sai gata ta dirga a gaban Hasiye,shaƙe mata wuya ta yi ta hau kirɓarta kamar an aiko ta. Cike da azaba Hasiye ta hau ƙoƙarin ƙwatar kanta daga riƙon da Kande ta yi mata ta na faɗin.

"Ki sake ni Yaya bana son ƙarasa gawar da ba tawa ba,kada ki hasala ni na yi miki naushin da zaki baje a wajen nan."

Jikin Kande ne ya hau rawa saboda gazawa da yake ƙoƙarin yi sakamakon tsufa,yunwa da gajiya da suka haɗu suka yi mata yawa. A daidai wannan lokacin Malam Bala da su Baffah Aƙilu suka shigo gidan. Saura ƙiris Gwaggo Kande ta kai ƙasa Kawu Sale ya taro ta yana faɗin.

"Subhanallahi,Gwaggo lafiya? Me yake faruwa ne a gidan?"

Hasiye ta na haki tana danne kukan da ke shirin taso mata na azabar da ta sha ta ce.

"Me yake faruwa kuwa banda wannan tsohuwar da ta kama ni tana duka kamar za ta kashe. DaÉ—in abun dai bani na kar zomon ba rataya aka bani."
Chapter 25 · 0% Book details