Sashe 9
Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lp=13Mugun albishir Page 13 . Daga alqalamin shafi'u dauda Giwa . Tare da ni Abu ihsan bn ishak (Madugun taska) . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Bai kamata in yi mamaki ba don ta ji Tsoron shi. . Tun lkcn ban sake jin motsin Zubaida a gidan ba." da lkcn cin abincin dare ya yi Alh.Bashir da kanshi ya qwalla min kira. Na same shi a falon ta jera mashi abinci, ta shiga dakinta ta kulle. Ya umarce ni mu ci abinci tare. Ga alama Alh.Bashir yana matuqar sona. Na sa hannu na muka ci lafiyayyar sakwara da naman shanu zuqa-zuqa a daddadan miyan taushen. To amma har lkcn da muke cin abincin hankali na yana kan dakin Zubaida. Na qosa ta fito don in sake ganinta, zan so ace na sake ganin masoyiyata ba don mijinta dake zaune a falo dare da rana ba." . "..bana son a riqa kallon ta...ina matuqar son matata... . na tuno gargadin shi. . . ** . . Wannan shi ne dan taqaitaccen abin da ya faru a rana ta ta farko a gidan Uban gidana da ya dauke ni aikin tuqa matarsa, ni Kuma tsohuwar masoyiyata Zubaida. Don haka da dare yayi sai naji na kasa barci, xuciyata ta cika da baqin kishi mai tsanani , da Kuma damuwa, da na tuna cewar Zubaida masoyiyata tana cikin daki tare daki tare da wannan lanqwasasshen mutum. To amma Kuma ni menace nawa a ciki? Shin ba mijinta ba ne?" na san cewar tunanin dake a xuciyata ba qaramin wauta ba ne da Kuma shirme. Don kuwa in ba tsabar sakarci ba me zai sa in riqa jin haushin mutumin dake tare da matarshi? . To amma Kuma ya kamata ni ma fa a tausaya min, don kuwa na riga shi fara son ta. Tun muna makaranta nake nuna mata soyayya. To sai dai Kuma soyayya ta banza ce, tunda dai ni ba ni da motoci da gidan alfarma. Ita Kuma Zubaida kyakkyawa ba matar riqaqqen talaka ba ce irina. Ina ma laifi da na samu aka daukeni aikin direbanta? . Ganin cewar barci ya qauracewa idanuna, sai na fito waje cikin tsakiyar dare na zauna ni kadai nayi shiru. . Dole ne in qwace Zubaida daga hannun wannan shashashan gurgun mijin nata. . Dole ne ya sake ta ya bar min ita in aura, ko yana so ko baya so. . Tsawon lkc ina nan zaune kamar a cikin mafarki, sai naji ihun Zubaida a cikin daren ta qwala kuka iya qarfinta. Na tashi xumbur a cikin sauri jikina yana tsima, na nufi inda wagegiyar tagar falon take na leqa. A lkcn ne naga abin takaicin da har abada ba zan ta6a mancewa da shi ba." . Alh.Bashir ne riqe da bulala yake dukan Zubaida. Tana durqushe cikin ladabi akan dardumar falon tana kuka, shi Kuma a zaune dan tsurut akan kujera yana ta tsala mata bulala tana kai hannu tana karewa, tana kuka. Ya zaro mata idanu a fusace ya ce..." . "don ubanki ko mutuwa zaki yi sai na cikashe bulala hamsin din da nayi niyyar yi maki, ina lissfawa ynx talatin da uku nayi." . Ya ci gaba da tsala mata bulala tana noqewa. Ta ja da baya tana sosawa cikin tsananin azaba. Ya ce da ita. . "ki matso in qarishe Sauran bulala shida, arba'in da hudu nayi, ina lissafe." . Naji tsananin takaici ya soki zuciyata. . "shiga ciki ka kashe shi mansur..! . Wata xuciyar ta fara yi min kururuwa. Amma ina kallo Alh.Bashir ya qarishe bulalarsa a jikin masoyiyata Zubaida, Babu wanda zai ceceta. Da ya kammala kanta sai ya wurga mata bulalar yayi murmushin mugunta, ya ce da ita. . "dauki bulalar gata nan ki 6oye min ita, sai Kuma gobe idan lkcn duka ya yi. Tashi ki bani wuri 'yar iska munufukar banza." . Zubaida ta tashi tana sauri da bulalar a hannunta, a haka har ta shige dakinta ta turo qofa ta kulle. Na ji kishi da damuwa sun cika xuciyata. Na san cewar bani da hujjar da zan shiga cikin falon in ce da mijinta wani abu. Don kuwa ko me yayi mata matarsa ce..." ko kasheta yayi ba ruwana. Maimakon haka sai na tsaya jikin tagar Tsawon lkc ina xubar da hawaye. Ina tausayawa masoyiyata Zubaida. . . ** . Washe gari da sassafe na nufi falon Alh.Bashir cikin damuwa. Na same shi a zaune kamar yadda nake tsammanin zan same shi. Na durqusa cikin ladabi na gaisheshi ina kumbure-kumbure,don kuwa da baqin ciki na kwana a raina. Ya amsa yana murmushi, sannan ya ce da ni, da yaga alamar zan tashi in tafi. . "dawo ka zauna mansur, ina son muyi wata 'yar magana ni da kai, zo ka zauna." . Na juyo na dube shi cikin mamaki da Kuma fargaba, don kuwa bana son ya fahimci Akwai wata sanayya a tsakanin da matarsa Zubaida. Na dawo na zauna akan daya daga cikin kujerun falon ina fuskantarshi. Ya kanannade kamar alkaki. Ya tattara hankalisa akaina, sannan ya ce da ni. . "mansur tun lkcn da kaxo gidan nan daga jiya xuwa yau, na san cewar dole ne ka riqa ganin wasu abubuwa Suna faruwa a tsakanina da matata Zubaida, wadanda zasu daure maka kai sosai. Shi ya san nake son muyi hira in baka wani labari, don ka san ko wacece Zubaida. Sannan Kuma ka san ko ni wanene." . Na bi shi da kallo Gabana yana faduwa, don kuwa nima na fara jinjinawa tsoron wannan lanqwasasshen Tsohon mai baqin ran tsiya. To amma Kuma ni ba bulalarsa nake jin tsoro ba, ni bindiga nake tsoro, don kuwa na san cewa a 6oye a jikinshi ba a rasa shi da bindiga. Tabbas ba haka nan yake zaune a falon ba. . "mansur." . Ya sake kirana, na amsa. Ya ce da ni. . "ka ta6a yin aure a garinku ku?" . Na girgiza kai cikin mamakin wannan tambaya. . "A 'a, bani da mata alhaji, daga ni sai halin." . Alh.Bashir ya yi murmushi ya shafi busassun yatsunshi. . "kayi sa"A mansur da baka da mata, don kuwa ynx ne zan baka shawarar irin macen da ya kamata ka aura duk lkcn da ka tashi yin aure." . Ya sake gyara zaman qafafunshi, qafafun wandon suka motsa suka hadu da juna, Babu komai a cikin su." . "Sau da yawa mu maza muna da wani irin halin mansur," . Ya ci gaba da cewa. . "wannan halin kuwa shine, duk lkcn da zamu yi aure muna son mu auri mata kyawawa a duniya wadanda duk inda a shiga zamu a riqa kallonsu anan yawa." . "haka ne alhaji." . na ce dashi. Don kuwa lalla6a shi nake yi don mu rabu lfy, bananas son ya ga kamar na raina shi. . Ya yi min murmushi, sannan ya ci gaba. . "nima ina da irin wannan halin mansur....na ina son in ga na auri mace mace mai kyau a duniya nan...ka . . Lp=14Mugun albishir Page 14 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . Tare da ni . Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . . Ni ma ina da irin wannan halin mansur, ina son in auri mace mai kyau a duniyar nan. Kai bari dai in taqaice maka labari, tun ina yaro kamar ka har tsufana, ni ban ta6a son wata mace ba sai kyakkyawa. Ban damu da kowanne irin halin mace take dashi ba, in dai kyakkyawa ce to ni kam ta gama biyana komai mansur." . Ya sake dubana har cikin idanuna, ya ci gaba. . "wannan shi ne abin da ya sa na kamu da son wannan mata tawa Zubaida. Lkcn da na fara ganin ta ban tsaya wahalar binciken halinta ba, haka kawai sai naji duk duniyar nan babu wacce nake so in mallaka kamarta. Ina son Zubaida sosai fiye da yadda zan fasalta maka. Ina sha'awar in ganni tare da ita a cikin mota ta ta haske ko'ina da kyakkyawar surarta. Ni Kuma ina tuqata muna yawon a cikin jin dadi da kwanciyar hankali." . Alh.Bashir yayi ajiyar xuciya. . "Zubaida kyakkyawa ce, sai dai Kuma halinta bai zamo kyakkyawa ba mansur. Zaka yi mamaki sosai idan na ce da kai Zubaida ce ta mayar da ni gurgu. Shekara uku da suka wuce lfy ta lau, ina da qafafuwa na kamar kowa, ina so ka sani, ba qafafuwa kadai ta so ta raba ni dasu ba, raina ta so ta raba ni dashi mansur. So ta yi ta kashe ni gaba daya!" . Kisa? Na tambayi kaina a tsorace. Kamar ya san abin da nake tunani sai yayi farat ya ce da ni. . "ba lallai ba ne ka amince da labarin da nake baka mansur. Don kuwa nima a wasu lokuta da suka wuce, sanda na fara son Zubaida da aka zo min da labarinta qin amincewa nayi, sbd na mace akan qaunarta. Sai daga baya da abin ya faru gare ni sannan na gano cewar gsky ake fada. Mansur ni ne mijin Zubaida na tara, Kuma duk cikin mazan da ta aura Babu talaka, duk mutane ne masu bilyoyin kudi irina. To amma Kuma ba wannan ne abin mamaki ba, ina son ka sani cewar mazaje takwas na baya da Zubaida ta aura tuni sun riga mu gidan gaskiya. Sun mutu!" . Na sake duban motsattsen mutumin a tsorce. Ya zaro min idanu ya ce. . "qwarai kuwa mansur, sun rasu baki daya. Don kuwa duk lkcn da Zubaida ta auri namiji ba ya wuce wata hudu a duniya, wasu Kuma su kan yi tsawon rai su kai har wata shiga ko bakwa, ba ciwon kai ba na qafa sai a wayi gari a ga mutum ya mutu . To amma Kuma ni duk na fi su tsawon kwana. Don kuwa ni shekararmu uku kenan ni da ita har ynxn ban mutu ba, qafafuwa na kawai na rasa." . Ya yi murmushi kamar abin da ya fada ya burgeshi. To amma Kuma ni ban yi murmushi ba . Ku yi haquri da iya wannan. Sai gobe in Allah ya kaimu a . Page 15mugun albishir Page 15 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare