Sashe 6
Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan an kashe motar an bude qofar sai kawuna alh. Badamasi dake a kaduna ya fito yana murmushi. Muka hada idanu, naji farin ciki ya kama ni don kuwa allah ya kawo min kudi a lkcn da nake neman su ruwa a jallo. Yana sanye da fararen kaya shadda riga da malum-malum. Dan matashin dattijo, mai kimanin shekaru hamsin a duniya, Wanda ko kusa a tarihin rayuwarsa bai shafi'u wata wahala ba." shi ya sa siffarsa babu alamun gajiya ko tsufa. . Da fitowarsa na tar6e shi cikin farin ciki . "sannu da xuwa alhaji." . Ya kama hannuna ya riqe yana dari. . "mansur manyan samari." . Muka kama hanyar zamu shiga cikin gida, Maman bose dake tsaye tana kumbure-kumbure ta ce a fusace. . "baka bani kudina ba, za Kuma ka shiga ciki." . Na juyo a fusace na harareta. . "amma ai sai ki bari sai naxo shagon, ko baki gani mun yi baqo ynx?" . Ta ce da ni. . "ni gsky ban yarda ba sai ka biya ni kudina." . Kawuna ya kallon, sannan ya kalli matar cikin damuwa. . "me yake faruwa ne?" . Ya tambayata. . "wane kudi zai baki?" . Maman bose tace dashi. . "bashi nake bin shi wata daya kenan ya hana ni. Shagona ya xo ya amshi tab..." . Jin zata tona min asiri yasa na hanzarta daka mata tsawa, na ce. . An tambayeki abin da naxo na amsa ne mara mutunci? Ki fadi kudinki mana a biya ki." . Kawuna ya ce da ita. . "ynx dai ke kudinki nawa ne malama?" . Maman bose ta ce dashi cikin ladabi. . Dari hudu ne da tamanin alhaj." . Kawuna ya zaro dari biyar a dunqule ya miqa mata. Tayi sauri ta miqo busassun yatsunta ta warce kudin. Ta ce dashi." . "na gode alhaji, gashi Kuma bani da canji, zan baka naira ashiri." . Alh. Badamasi ya ce da ita. . "jeki kawai abin ki, an bar maki." . Ta yi murmushi. Na sake hararta na ce. . "ba ki ci bulus ba, zan xo in amshi cannjina ke ma kin sani." . Kawuna ya janye ni muka shiga cikin gida, bamu zame ko ina ba sai dakin kakata, Kada ka tambayeni inda iyayena suke, don kuwa mahaifina qaramin ma"aikacin hukumar aikin gona ne a qaramar hukuma..yana can zaune a gidan ma"aikata tare da mahaifiyata da Kuma Sauran qanne na uku. Da yake kakata juma ta saba da ni, bata son rabuwa da ni, shi yasa bata amince in zauna a gidan mahaifina ba na ma"aikata. Duk kuwa da irin fafatawar da muke yi da ita, Fadan safe daban, na rana daban, haka na maraice, to amma ai duk laifinta ne, tunda dai ita ba zata iya gani ta yi shiru ba, sai dai Kuma da ace ta san ina shan tabar a 6oye aniya kuwa zata amince ta zauna tare da ni? . . . ** . . Minti goma bayan haka muna zaune a dakin kakata tare da Kawuna da ya kawo min ziyara yana yi min fada cikin fushi. . "ina amfanin irin wannan rayuwata takalmi mansur? Ace kai kenan Kullum naxo gidan nan sai na sameka a cikin masala. Ba ka da wata qwaqqwarar sana"a sai rigima da mutane akan kudi, kana jin wanna ita ce rayuwa mai kyau?" . Na sunkuyar da kai ban ce komai ba." . Kakata ta ce. . "Tunda ynx kaxo ka fada mashi, wata qila kai yaji maganarka. Amma ni da yake ya raina ni yaushe zai ji Fadan? Nayi juyin duniya da yaron nan ya samu sana'a, tunda dai aikin gwamnatin ya qirga samuwa, ya qi sbd girman kai. Wai shi tunda dai yayi karatun book bai ga dalilin da zai sa ya yi aikin qarfin ba." wai sai dai ya ci a huce." . Kawuna ya yi tsaki, ya ce. . "to ina maganarka hutu a qasar nan? Ai babu hutu mansur, haka nan zaka dake ka nemi na kanka ka hucewa kanka takaici da wulaqancin mutane." . Ya dan saurrara sannan ya ce da ni. . "Tunda abin ya xo a haka, ina ganin abin da zamu yi shi ne....! Ka shirya mu tafi kaduna tare.sai in samar maka aiki a can. . . Lp=9Mugun albishir page 9 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan bn ishak (Madugun taska) . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba. . . Ka shirya mu tafi kaduna tare, sai in samar maka aikin yi a can. Dama Akwai wani abokina da yake neman doreba, Kuma ni ya baiwa alhakin in nemo mashi yaro nutattse, don kuwa mutumin gurgu ne bashi da qafafuwa." . Na dago kai cikin damuwa na dubi Kawuna . "amma Kawuna sbd allah idan ma tuqin zan yi sai in rasa wanda zan riqa tuqawa sai musaki mara qafafu?" . Kawuna ya fashe da dariya, sannan ya ce da ni. . "ka cika gajen haquri mansur, in banda abin ka ai sai ka tsaya kuna in yi maka bayani. Kada ka raina wannan gurgun, duk da kasancewar sa musaki ina son ka san cewar duk fadin birnin kaduna babu hamshaqin mai kudi kamar sa. Idan har ka amince zaka bi ni ka riqa yi mishi tuqin to ka gama hayewa mansur....don kuwa a qalla duk wata zai riqa biyanka ladan duba talatin." . "dubu talatin?" . Na tambayi Kawuna cikin xumudi. . Ya ce da ni yana fara''a, . "qwarai kuwa. Bayan haka shi zai baka muhalli, shi zai dauki nauyin abincinka safe da rana ko da yaushe." . Nayi shiru ina tunani don kuwa arziqi ya soma qwanqwasa min qofa. Nayi saurin lissafa dubu talatin Sau goma sha biyu, naga cewar kudin sun kai har naira dubu dari uku da sittin. a shekara daya fa kenan kawai. To idan Kuma na kai shekara goma milyan nawa kenan? . Naji xufa ta fara kwararo min, Kawuna yana kallona yana murmushi. . Haqiqa arziqi ya samu!" . Abu na farko da na fara rayawa a xuciyata shi ne, aure Zubaida. abu na biyu Kuma shi ne yadda zan yada zango a qofar shagon Maman bose cikin isa da qasaita a duk lkcn da nazo garin. In fito daga cikin mota ta mai shegen tsaya in more. Kawuna ya ci gaba da cewa. . "ya kamata tun ynx ka fara tunanin abin da zaka yi da kudin da zaka samu mansur....bana son almubazzaranci, ya kamata ka yi aure nan ba da jimawa ba." don kuwa in kana da aure zaka fi zama mutum nutattse mai kamala a idon mutane." . Aure! naji Kawuna ya sake budo min wani babi mai cike da damuwa a xuciyata. Kullum in aka yi min tadin aure sai na tuno da abar begena Zubaida. har ynx ina son Ku san cewar tun lkcn da nayi bankwana da Zubaida a ranar mu ta qarshe a makaranta har ynxn qaunarta tana nan daram a xuciyata. Kamar aikin sihiri, Kuma tun daga lkcn ban sake jin labarin inda take ba a duniya. Ban san a inda tayi aure ba, to amma Kuma xuciyata ta kasa jurewa in haqura da son ta, har ynx ban sake jin ina son wata mace ba a duniya. Bani da tamkar Zubaida. Kuma ba zan sake samun tamkarta a duniya ba." don kuwa ita kadai ce mace da xuciyata take so da qauna. Kuma Kullum idan na kwanta barci sai na ganta a mafarki. Wani lkcn in ganta a cikin damuwa, wani lkcn Kuma in ganta cike da annashuwa. Amma Kuma duk sanda nayi mafarkinta bata tsyawa muyi hira, sai dai in qura mata ido tana tsaye. . A haka nake ta bin rayuwar wannan masoyiya tawa, na san cewar ita tana can tuntuni ta mance da ni a rayuwata. Amma Kuma ni gashi ta barni ina ta fama da ciwon sonta shekara da shekaru. "sai yaushe wannan ciwon mai tsanani zai rabu da xuciyata, don in samu sukuni a rayuwata?" . Nayi murmushin qarfin hali na cewa Kawuna. . "alhaji ai ni tuni na haqura da aure a duniya." . "sbd me mansur...a qanne dalili?" . Na kalle shi, sannan na waiga gefen da kakata juma take na ce dasu cikin damuwa. . "tun lkcn da na rasa wata masoyiya tawa a makaranta mai Suna Zubaida. Tun lkcn na haqura da batun aure a rayuwata. Don kuwa ita kadai ce macen da nake so Gashi kuma ta tafi ta barni." . . ** . Tun lkcn da na sauka daga tasin da ta daukoni daga gidan Kawuna na fara hango katafaren gidan Alh. Bashir Gurgu. farin sol dashi daga nesa kamar an daukoshi daga birnin sin. Na tsaya akan titi ina kallon gidan xuciyata cike da mamaki, don kuwa duk tagogin gidan da Kuma qofofin duk na gwalagwalaine. Sannan Kuma ga shuke-shuke nan burjik sun zagaye gidan cike da furanni jajaye da farare masu ban sha'awa. . Bayan na gama kallon ne sai na kama hanya na tunkari faffadar qofar shiga gidan. Daga nesa ina iya hango wani tsohon mai gadi a zaune riqe da bulala a bakin qofar. Kwana biyu kenan da xuwanka kaduna tare da kaduna tare da Kawuna. A cikin kwanaki biyun suka gama shirya komai da alhaji bashir gurgu, ynx xuwana kawai ake jira in xo in fara aiki, Kuma gashinazo. . Kafin in qarsa inda mai gadin yake sai da na sake tsayawa na dubi kayan dake jikina, kafin in baro gidan Kawuna na daukar cewar kayan da na sako na qure adaka zasu fitarku da ni kunya. To amma Kuma a halin ynx da naxo naga yanayin gidan, sai Kuma naji kwalliyar da nayi ba ta gamsar da ni ba." na dubi takalmina mai kan ,.kura, Wanda shi kadai ne abin arziqi a kayan jikina. Bana shekara takalmin shiga kenan a wajena, a wurin wani tsohon dan sanda mai ritaya na sayen shi. Kada ka so jin Sauran kayan dake jikina, don kuwa kodadden wando ne shudi Wanda ya sha faci manya-manya kamar tamfol din fyadin masara. Sai Kuma baqar riga mai kwala da Kuma shudiyar hula hana-sallah da na ta6a ciyota a wajen caca. . Na sake duban katafaren gidan naji tsoro