← Book details Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 21

Sashe 13

Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zata iya rabuwa da mijinta ba sai lkcn da ya mutu shi Kuma ba zai mutu ba sai ya qara shekaru talatin a duniya, shakka Babu rayuwata tana cikin hadari . Ba zan iya tsayawa ina kallonshi har nan da shekara talatin ba ina kallonshi . "ba wani lkc mai tsawo likitoci suka ce zai qara ba, sun ce ba zai wuce nan da shekara talatin a duniya ba...." . Na sake tuno maganar Zubaida. Ban san lkcn da hawayen baqin ciki ya fara sartu akan fuskata ba." . . Lp=20mugun albishir Page 20 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Ban san lkcn da hawayen baqin ciki ya fara sartu akan fuskata ba. Na yi ajiyar xuciya sannan na motsa jikina dake a bushe tun tafiyar Zubaida. Na koma na nufi gado. Da zaunawata sai na kwanta cikin damuwa na qurawa sararin samaniyar dakin idanu, ina tunanin hanyar da ya kamata in dauka don mallakar Zubaida. To amma Kuma tsawon lkc ban gano wata sahihiyar hanya mafi sauqi da zan bi in auri Zubaida ba." sai shekaru talatin masu xuwa. . Shin mene ne jin dadin rayuwa idan har xuciyata bata cikin sukunni? na san cewa idan har ban auri wannan masoyiya tawa ba, har abada ba zan sake samun sukunni a xuciyata ba." gashi Kuma ba ni da wata hanya da zan bi in aureta. A halin ynx matar wani ce, Kuma ba zai iya sakinta ba har abada, ita ma ba zata iya bijire masa ba su rabu, sannan Kuma ana tsammanin ba zai mutu ba sai nan da shekaru talatin masu xuwa. Kuma zai iya kasancewar in zauna in jira shi har xuwa lkcn, daga baya Kuma ya xo bai mutu ba, wa ya sani ma ko wataqila ya qara shekara saba'in a duniya? Ko Kuma ya mutun, ta auri wani daban ba ni ba? Sai tsoro ya sake kamani sannan Kuma takaici mai tsanani ya sake mamaye xuciyata. . Dole ne in sake dabara! . Na tabbatar wa kaina. Ya zama dole in bi duk hanyar da zan bi don in samu nasara idan har ina son in auri wannan tauraruwar mace mai qyalqyali kamar daimon. . A lkcn ne mugun tunanin da ya zamo musabbabin ruguza tarihin rayuwata ya fado min a xuciyata. Wannan shi ne karo na farko da na fara tunanin kashe mutum. ' tabbas ya zamo mani dole in kashe Alh.Bashir!' . Na yi mamaki da na ji cikin qanqanin lkc xuciyata ta gamsu da wannan tunani mara kyau. Don kuwa a rayuwar da nayi a can baya ni mutum ne mai tausayi da Kuma tsoro. Ko kiyashi bana iya kashewa, to amma sai gashi ynx zamani ya xo, sbd wata mace guda daya har na fara tunanin kashe mutum ba ma kiyashi ko dan tsako ba." xuciyata ta ci gaba da ingiza ni tana yi min kururuwar shaidan . 'yi sauri ka je ka kashe shi mansur! Idan har ka barshi a raye to har abada ba zai ta6a rabuwa da Zubaida ba." Kuma ba zai mutu ba sai ya qara shekara talatin a duniya, ka yi sauri ka je ka kashe shi don ka mallaki kyakkyawar masoyiyarka wacce ka ke so shekara da shekaru. . Tunane-tunane barkatai mara san kyau suka cika min qwaqwalwa. Na tuno zazzaqar muryarta da Kuma kyakkyawar surar jikinta. Xuciyata ta wassafa min lkcn da za a ce gashi an daura aurenmu ta zama mata ta. . "idan har mijina ya mutu ba zan sake aurenmu wani mai kudi ba." na gwammace in sami wani saurayi sabon jini Kuma yaro dan zamani wanda zamu yi soyayya . Wannan shi ne albishir din da Zubaida ta yi min, Kuma na sannan cewar da ni take. Bata so ne ta fito fili ta sanar da ni, sbd tana jin kunyata. To amma Kuma Babu komai na gane hakan da kaina. In dai saurayi take so dan zamani, idan ba kudi da motoci take so ba....to ta samu abin da take so. Ynx kam ya rage nawa in yi sauri in je in kashe mijinta. Don wannan albishir da tayi min ya zama gsky. . Na tashi xumbur, kamar Wanda aka cakawa allura na sauko daga kan gadona, na bude qofar dakin na fice waje a fusace, xuciyata na tafarfasa na nufi falon da Alh.Bashir gurgu yake babu alamar tsoro ko fargaba a tare da ni, don kuwa na qosa in ga ya mutu. . . Lp=21 Mugun albishir Page 21 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Na nufi falon Alh.Bashir gurgu Babu alamar tsoro ko fargaba a tare da ni, don kuwa na qosa in ga ya mutu. Babu motsi ko sautin wani abu da ake iya ji a cikin gidan face kukan tsuntsaye da ke wasanninsu akan bishiyoyin dake a can wajen gidan da Kuma wadanda ke shigowa Suna guje-guje akan qananan shuke-shuke. . Na san cewar tuni Zubaida ta kwanta ta yi barci, da wahala ta ji motsina a lkcn da na shiga falon. Na rage saurin da nake yi na fara tafiya Sannu a hankali ina sanda a cikin daren, kamar 6arawon tantabaru. Na tura qofar gilashin falon a hankali ta bude ba tare da tayi wani motsi Wanda zai iya farkar dashi daga barci ba, na shiga cikin falon, duk an kashe qwayayen babu wani haske, hakan bai hana ni ganin inda alhaji ke kwance ba akan doguwar kujerar dake a falon inda yake kwana ya wuni a zaune. . Na san cewar barci yake yi, to amma Kuma duk da haka idan nayi motsi qwaqqwara me yiwuwa ya tashi a firgice, Kuma idan har na sake ya farka ya ritsa ni, a cikin dare irin wannan a falon shi, to kashina ya bushe, domin ina zargin ba za a ta6a rasa shi da bindiga a 6oye ba." Kuma kai tsaye zai harbeni, don kuwa ya san cewar in dai har ina da gsky to Babu abin da zai san in shigo falon ina sanda da qarfe kusan biyu na dare. . Da nayi wannan tunanin sai nayi sauri na qarisa inda yake kwance ya miqe ya bi tsawon kujerun kamar matacce, ko numfashi baya yi, to amma Kuma ni dai na san cewar barci yake yi. . Ban tsaya jiran komai ba sai nayi tsalle na cafi wuyansa da kanshi, cikin sauri na murde wuyansa ya karye, naji sautin karyewar qashi kamar an 6allah sillan kara. Nayi mamaki sosai da naga bai motsa ba, Kuma bai farka ba yana a kwance kamar mushen zakara. To amma Kuma wannan bai karya min guiwa ba, ya riga ya mutu. Da wahala a karya wuyan mutum Kuma ya qara shekara talatin a duniya . Na yi sauri na ja da baya na fara shirin ficewa daga falon, xufa na kwararo min ta ko ina a jikina. Don kuwa nayi abin da ban ta6a yi ba a duniya. Sannan Kuma abin da ban ta6a tsammanin aikatawa ba." . Na kashe mutum!! . Nayi saurin bude qofar na fice xuciyata tana rufdugu kamar ana daka lura a cikin ta. Na koma dakina na shiga na rufe qofa na zauna a bakin gadona ina mayar da numfashi. duka-duka abin ya faru ne a cikin dan lkc qanqani, xuwan Zubaida dakina da Kuma ficewarta, sai Kuma xuwana falon, kashe mijinta da Kuma dawowata. Abin kamar aikin bude idanu. Ko shakka babu abin da ya faru ya faru. Na kashe mijin Zubaida Alh.Bashir mutumin da ya daukeni aiki. Kuma yayi alqawarin zai kyautata min a rayuwata in har na riqe mashi amanar matarsa. Haqiqa ban yi amana ba, Kuma ban riqe alqawarin ba." wannan wani abu ne Wanda zai zauna min a xuciyata ya yi ta bi na a duniya yana damuna shekara da shekaru masu xuwa. . Da naji zafi ya dame ni sai na kashe wutar dakina na zauna a cikin duhu, nayi tagumi. Ni kaina na san cewar nayi abin da baiwa dace ba." nan da nan naji tsoro ya kamani, da na tuna cewar a halin ynx muna tare da gawa a cikin gidan. Duhun da nake ciki da Kuma talatainin daren da ake ciki su suka sake taruwa suka iza wutar fargabar da nake ciki. . Na san cewar Babu wani maganar barci, don haka sai na ci gaba da zama ni kadai a cikin daren ina wasi-wasin halin da abin da na aikata,sannan Kuma a lkc guda ina addu'ar allah ya mallaka min wannan masoyiya tawa da nake ta so shekara da shekaru wato Zubaida. Gara in roqi allah, don Kada in yi wannan mugun aikin a banza. . . ** ** . . Wani zakara mai zaqin murya ya kwantsama cara iya qarfin sa ta karade kusan ko ina a unguwar. A daidai lkcn ne Kuma na jiyo daddadar muryar Zubaida ta kwantsama tata carar ta 6urari ita ma iyakar qarfInta . "wayyo allah na shiga uku na lalace....alhaji...?" . Na ji gabana ya fadi ina zaune nayi tagumi, na san cewar asuba ta yi. Zubaida ta fito zata yi alwala kenan Kuma ta tsinci gawar mijinta a falon yayi kwanan Keso. . Na san cewar idan har ban tashi na je na ga abin da ya faru ba, me yiwuwa ta zargeni, sai nayi sauri na tashi na bude qofar dakina a cikin sauri na nufi falon, daidai lkcn ne na ci karo da mai gadi ya shigo cikin gidan a guje riqe da kwari da baka a hannunsa, kamar Wanda zai je farautar ragon maza. Muka fada cikin falon a lkc guda ni da shi. A lkc ne muka samu Zubaida ta durquusa a gaban gawar mijinta tana kuka kamar ranta zai fita. . "hajiya lfy? Me ya faru?" . Dan Tsohon dake gadi ya fara tambayarta a tsorace. Zubaida ta ce dashi tana 6urari. . "alhaji ne ya rasu, yi sauri ka yiwa 'yansanda waya su zo falalu." . Dan tsohon ya saki kwari da bakar hannunsa yana kyarma, yana qoqarin motsa baki . Wataqila Kuma yana
Chapter 13 · 0% Book details