Sashe 19
Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
goma a gidan yari, duk a dalilin wannan kyakkyawar mace dake tsaye a gabana tana yi min kallon mahaukaci sha-sha-sha! . . Naji hawaye sun taru a cikin idanuna, sannan Kuma naji ni kaina na tsani kaina. Na ce da Zubaida ina kuka. . "Kada ki yi min haka Zubaida. Duk duniyar nan ban ta6a jin ina son wata mace ba sai ke kadai. Ki ji tausayina Zubaida Kada ki karya alqawari." . Hawayen baqin ciki suka fara kwaranya a idanuna, Zubaida ta dube ni a yatsine cikin izgilanci ta ce da ni.ya . "kayi kuskure mansur, Tunda nake ban ta6a jin ina sonka ba, Kada ka ta6a rayawa a xuciyarka na ta6a sonka a duniya, Kuma har abada ba zan ta6a sonka ba." . . Lp=30Mugun albishir Page 30 . daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Ka yi kuskure mansur, tunda nake ban ta6a jin ina sonka ba, Kada ka ta6a rayawa a xuciyarka na ta6a sonka a duniya, Kuma har abada ba .zan ta6a sonka ba." . Muka hada idanu da ita tsawon lkc, xuwa can Kuma sai naga kamar zata fashe da dariya, sai nace da ita. . "ni dama na san cewar wasa kike yi min, kin cika son wasa Zubaida. Bai kamata ace kina yi min irin wannan wasan ba, ni na san kina sona, kina dai fadar wadannan maganganun ne don ki bani tsoro....bana son irin wannan wasan, in abin ya xo da tsautsayi sai ki ga mutum ya kamu da hawan jini." . Zubaida ta murtuke fuskarta a fusace ta ce da ni. . "wa ya fadi maka cewar wasa nake maka? To bari in tabbatar maka cewar ba na sonka Kuma ba wasa nake yi maka ba mansur." . Tana gama fadin haka sai ta daga zazzaqar muryarta ta kwadawa qartin da na baro a waje kira. . "kuna ina?" . Na ji qartin sun amsa baki daya kamar kwaduna. . "gamu nan xuwa hajiya." . Na ji sun rugo aguje kamar an koro raquma har qasa ke amsawa. Suka shigo harabar gidan suka shawo kwana kowannensu da qaton ciki kamar masaki. Da xuwansu tun kafin su huta, sai Zubaida ta nuna ni da dan yatsa sannan ta ce a fusace. . "Ku lallasa min wannan baqon har sai kun ga baya numfashi." . Tun kafin ta rufe baki babban cikin su ya daukeni yayi qoli-qoli da ni kamar ya dauki 6awon kara, ya kwada ni da qasa, kaina ya hadu da dutse, naji xogi da radadi sun soke ni, na fara ihu ina yi masu magiya. . Qato daya ya sake rarumata ya yi sama da ni shima ya sake ni na fado tim! Suka hau ni da duka kamar Suna buga ganga. Tun ina iya yin ihu har na kasa motsawa. Abu na qarshe da naji kafin in suma shi ne tattausar muryar Zubaida tana dakawa qartin tsawa a fusace tana cewa. . "ku dauke shi ku je can ku jefar dashi a bakin titi ya qarisa a can!!" . . ** . . Ban san adadin lkcn da na yi a some ba, na dai farka na samu kaina a kwana a cikin wasu ciyayi dake a cunkushe da bakin titi. Na dago kaina daqyar naji hucin wucewar motoci Suna wucewa ta Gabana a guje kamar kibiyoyi. Nayi qoqari na tashi daqyar. Idanuna sun yi min nauyi, daqyar nake iya ganin hasken sararin samaniya. Yamma tayi sosai Babu hasken rana, ga alama qarfe shida tayi na yamma. Wannan shi ya ganar da ni cewar na dauki fiye da awoyi biyar a cikin ciyayin ban san inda kaina yake ba." idan nayi la'akari da lkcn da masu gadin Zubaida suka lallasa ni a gidan ta, kafin su dauko ni su zo su watsar da ni a bakin titi kamar yadda ta basu umarni cikin fushi. . Na kama ciyayin da na tsinci kaina a ciki na fara yunqurin miqewa tsaye, hannu a hankali ina qara samun sauqi, don kuwa na fara ganin abubuwa dake kai komo a wurin da aka jefar da ni. Inda Babu kowa, ga alama Bayan gari ne....! Don kuwa Babu Wanda ya san ina kwance a wurin. Babu mutane sai jefi-jefi da gine-ginen qananuun masana'antu da aka rufe suka daina aiki a bakin titin. Wannan shi ya ganar da ni cewar babu mama a cikin mota suka xubo ni suka zo da ni suka watsar. . Na lalla6a na samu a hankali na fito daga cikin ciyayin kayana sun yi fata-fata, duk jikina a kumbure yake don kuwa na ci uban duka kamar kalangun noma. a haka na samu ina tafiya juwa na barazanar daukata ta kayar da ni a qasa, har dai na samu na kai kaina gida inda nake kwana a wani aljihun aure a gidan wani mutum da ya saba da ni Bayan na fito daga gidan yari. . Bayan na kwanta sai abubuwa masu yawa suka riqa dawo min cikin xuciyata . "ku lallasa min wannan baqon har sai kun ga baya numfashi..." . Na tuno muryar Zubaida sannan kuma na lkcn da take cewa qartin. . "Kuma dauke shi Kuma je can Kuma jefar dashi a bakin titi. Ya qarisa a can...." . Abin da ya faru ya riga ya faru! Ynx tunanin abin da ya wuce Bashi da amfani. Don kuwa tunanina bai wuce na Zubaida ba." gashi kuma ta butulce min ta yaudare ni ta cuci rayuwata. Kin zalunce ni Zubaida! Na ce a xuciyata ina kukan baqin ciki . To amma kuma nima na zalunci kaina, don kuwa tun farko da ace na haqura tun a lkcn da na fahimci Zubaida ta fi qarfina da duk wannan matsalar bata faru da ni ba." sannan kuma wannan lamarin da ya faru da ni, na san cewar alhakin marigayin mijinta ne Alh.Bashir gurgu. Don kuwa na ci amanarshi na goyawa Zubaida baya ta kashe shi. Alhakinshi ne ya fara kama ni, kuma zan ci gaba da fuskantarabubuwa da dama a gaba a dalilin wannan son xuciya da nayi na kasa mashi amanar da ya bani. . Ba zan ta6a mance lkcn da motar asibiti ta dauko gawarshi ta wuce ta gaban mu muna a cikin mota muna kallo ni da matarshi Zubaida ba." lkcn ban ta6a tsammanin zata yaudareni ba, haqiqa nayi kuskure. Kuma nayi abin da xuciyata take so na 6ata tarihin rayuwata . na san cewar ba zan ta6a daina son Zubaida ba a rayuwata. Har ynxn kuwa da ta san aka yi min wannan rubdugun dukan, ina nan ina sonta a cikin xuciyata. To amma Kuma ya zame min dole in haqura in qaurace mata. Don kuwa ruwan ba tsaran kwando bane. Babu matsala! Na ce a xuciyata. Ba ni kadai bane namiji na farko da ya ta6a samun matsalar soyayya. Akwai mutane da dama a duniya wadanda suka dade Suna neman soyayyar wasu matan, kuma basu samu goyon baya ba." . Zubaida bata qaunata! Don haka na haqura da ita!! . Na rufe babinta a cikin xuciyata. Amma Kuma duk da haka idan nayi sa'a, wata rana zata canza ra'ayinta ta xo wurina ta ce ta dawo tana sona. Zan amshi soyayyarta Kuma cikin gaggawa sannan Kuma zan yi farin ciki mai yawa a duniya. To amma kuma anya Zubaida zata so ni? . Bayan nayi kwana ina jinya kamar Wanda yayi hadarin mota, sai qarfina ya dawo na ci gaba da harkokina. A safiyar rana ta uku ne, ina zaune nayi tagumi ina sauraren qaramin rediyona ina jin labaran duniya, sai naji muryar matar dake gabatar da labaran tana cewa; . "A yammacin jiya ne jami'an tsaro suka cafke Hajiya Zubaida wacce aka kama dumu-dumu da laifin kashe mijinta alh.rufa'i, ta hanyar tuno shi daga bene mai hawa uku. Wata majiyar ta ce Zubaida ta auri mazaje barkatai sun mutu. Kuma anan zargin duk ita ce take kashe su." a halin ynx dai tana nan a babban ofishin 'yansanda na jiya. To allah ya kyauta, Kuma ya jiqan marigayi Alh. Rufa'i...." . Tun kafin in gama jin labarin nayi sauri na miqe tsaye Xumbur! A tsorace kamar Wanda aka tsirawwa allura. Wacce Zubaida Kuma 'yansanda suka cafke? Na tambayi kaina. Zubaida masoyiyata? ko shakka Babu ita ce, don kuwa sunann mijinta alh. Rufa'i! Shi ne mutumin da ya aikeni gidanshi aikin gida ramin fanfo har matarshi Zubaida ta sa aka lallasa ni.ya kwana uku fa kacal kenan da ganin mutumin, amma Kuma gashi ynx anan bayar da sanarwar mutuwarshi a rediyo. . lp=31 Mugun albishir Page 31 . (kammalawa} Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . kwana uku kacal fa kenan da ganin mutumin amma Kuma ynxn gashi anan bayar da sanarwar mutuwarshi a rediyo. . Duk da haka sai naji tausayin ta ya kamani, don kuwa ina yi mata so ne irin wanda ko me zata yi min a duniya ba zan ta6a ganin laifinta ba." bana so in amince da wannan zargi da naji an fadi a rediyo, Wanda aka dora shi a wuyan kyakkyawa Zubaida. Bana son in ji mutane Suna cewa ita ce ta kashe mazajenta. To amma Kuma dole ne in amince tunda dai ni da bakinta ta sanar min..." . Haqiqa masoyiya ta 'yansanda suka kama!! Naji hankali na ya tashi sannan Kuma tsoro ya kama ni. Wa zai taimaka mata a wannan karon don kada a yanke mata hukuncin kisa? Nan da nan naji tuni na mance da dukan da ta sa aka yi min, naji ina muradin sake xuwa in taimake ta ko da kuwa wannan shi ne abu na qarshe da zan yi a rayuwata. . Na san cewar wasu zasu ga laifinta akan wannan aikin keto da zan sake yi wa masoyiyata. To amma Kuma me zai sa mutane su ga laifina don na ceto rayuwar wacce xuciyata ke bege dare da rana? Duk lkcn da dan adam ya fada tarkon soyayya, to shi kenan rayuwarsa ta fada cikin hadurra masu yawa, don kuwa babu mamaki don ma'aboci soyayya ya sadaukar da rayuwarsa ga