← Book details Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 21

Sashe 12

Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi tafiyar tun da sassafe muka shirya muka shiga mota muka tafi. Ganin cewar ni na san garin, sai na amshi tuqin motar shi kuma mijina ya zauna a daya 6angered. Muna tafiya muna hira, har barci ya kwashe shi, na ci gaba da tuqin ni kadai ban tashe shi ba." . Zubaida ta jawo numfashi cikin damuwa sannan ta ci gaba . "ina cikin tuqa motar sai na ji fitsari ya kama ni mansur, nan da nan sai na rage gudu, nayi fakin na tsayar da motar a gefen wani qaton rami mai kama da rafi a gefen titi, sannan tsabar matsuwar da nayi sai na mance na fito ban bar motar a giya ba, Kuma ban sanya birkin yin fakin ba." gashi Kuma a saman tsauni ne, ban sani ba a lkcn da na juya baya na tsuguna ina fitsari ashe motar ta fara gangarowa tana komawa baya,sannan Kuma ba wani waigi da zai tare ta a gefen titin." . Muryar Zubaida ta fara rawa, sannan Kuma ta fara shassheqar kuka. Na qura mata ido ko qiftawa bana yi, a lkcn ne ta ci gaba da bani labarin. . "ban ankara ba mansur, sai na hangi motar ta tunkari qaton ramin dake a bakin titin, ta fada ciki. Ina kallon lkcn da motar tayi qundunbala Sau biyu ta fada qasa ta hadu da duwatsu ta tarwatse. Ba zan ta6a mancewa da irin mugun sautin da na ji ba a lkcn da motar ta tarwatse a cikin ramin. Mijina yana ciki yana barci. Na taso a tsorace ina kururuwa ni kadai a cikin naji mansur, Bayan motoci sun tsaya mutane sun taru, sai aka ciro motar aka bude aka fito da mijina jina-jina bai san inda yake ba, amma Kuma mun yi sa'a, bai mutu ba." da aka kai shi asibiti ne suka yanke masa qafafuwa don kuwa sun yirugu-rugu. Bayan ya yi watanni yana jinya sai muka dawo gida. Tun daga wannan lkcn bamu sake zaman lfy ba a gidan nan. Kullum sai ya ci min zarafi ya zazzage ni, Kullum sai ya dauki bulala ya dake ni akan abin da ba laifina ba ne....! A haka muke zaune tsawon shekaru biyu da suka wuce..." . Ta fashe da kukan baqin ciki, Wanda wannan shi ne ya tilasta mata dakatar da labarin da take bani. Ta sunkuyar da kai tayi tagumi, daga inda nake zaune ina iya hango hawayen dake cinye gudu a kumatunta. Na ji tausayinta ya kama ni fiye da Kowanne lkc a rayuwata. Sautin kukan ta ya ci gaba da fita Sannu a hankali a cikin daren ina zaune ina saurarenta. Takaici da baqin ciki ya sake kama ni, don kuwa na san cewa Zubaida masoyiya ta tana cikin wani qangin rayuwa, Wanda in har da gasske ina sonta to ynx ne lkcn da zan nuna mata irin wannan soyayya dake a xuciyata . Ya zama dole in raba ta da wannan azzalumin mijina nata Wanda yake yake azabtar da ita dare da rana. Nayi ajiyar xuciya sannan na ce da ita . "Kada kina damu Zubaida kina yi haquri, komai na duniya yana da iyaka. Kamata ya yi kina kai shi qara a raba kina dashi, Kada ya halaka kina da irin wannan zaluncin da yake yi ciki Kullum." . Tsawon wani lkc Zubaida bata ce min komai ba, ta ci gaba da kusa kukanta kamar ba ta ji ni ba, xuwa can Kuma sai ta bani amsar maganata, ta ce da ni cikin kuka. . "Akwai lokuta da damar da nake yin shawarar in gudu in bar shi, sai dai Kuma idan nayi la'akari da halin da yake ciki sai in ga cewar bai kamata in gudu in gudu in Bashir ba." don kuwa ko ba komai ni ce silar matsalar da ta same shi har ya naqasa ya zama gurgu." . Na ce da ita cikin lallaShi . "kina daina damuwa Zubaida. Abin da ya faru ba laifinki ba ne....! . . Lp=19mugun albishir Page 19 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Ba laifinki ba ne.tsautsayi ne, Wanda zai iya faruwa da kowa a duniya, ko kina a cikin motar, idan allah ya qaddara wannan abu zai faru dole sai ya faru." . Zubaida ta share hawayen dake a idanunta, a wannan lkcn gyalen da yake rufe da gashin kanta ya sa6ule ya gangaro kan kafadunta, amma Kuma bata damu ba, a lkcn da take share hawayen ne gashin kanta ya fara qyalqyali a cikin hasken dakin. Ta ce da ni. . "na san tsautsayi ne, to amma Kuma shi har abada ba zai gane hakan ba." duk lkcn da ya hadu da mutane sai ya basu wannan labarin da ya baka. Ba komai zan ci gaba da zama dashi, har xuwa lkcn da mutuwa zata raba mu. Ba zan iya guduwa in bar shi a cikin wannan halin ba." don kuwa ni ce nake daukar duk dawainiyarsa tunda baya iya tashi ya yi wani abu da kanshi, komai sai dai in yi mashi." . Na ji kishi mai tsanani da takaici ya sake kama xuciyata. Don kuwa duk wannan baqar wahala da Zubaida take sha a wurin mijinta, ba ta so ya rabu da ita. Tana son zama dashi a haka. Naji duniyar tayi min qunci, don kuwa na fahimci babbar matsalar da zata yi min cikas wajen mallakar Zubaida ta zama matata, bai wuce wannan shashashan gurgun mijin nata ba dake zaune a falo a kan keken guragu. Nayi qarfin halin tambayarta. . "to amma ke kina jin ya dace ki yi ta zama da mijin da baya sonki har qarshen rayuwa Zubaida?" ya kamata ki yi tunani sosai, ya kamata ki yi qoqari ki rabu dashi don ki samu wani mijin Wanda yake sonki Ku yi aurenku na soyayya ba irin wannan ba." . Zubaida tayi shiru tana kallon bangon dakin tana tunani, bayan wani lkc sai ta ce da ni. . "wannan shawara ce mai kyau mansur. Idan har mijina ya mutu ba zan sake auren wani mai kudi ba." na gwammace in samu wani Saurayi sabon jinni in aura, yaro matashi dan zamani Wanda zamu yi soyayya, ni ynx ba kudi suka fi damuna ba a rayuwata na fi so in samu nutsuwa da kwanciyar hankali tare da masoyina." . Na ji farin ciki da xumudi sun kamani, don kuwa Zubaida ta ta6o layina. Ta ta6o min 6angaren da ya fi qaiqayi a xuciyata. Idan har ta amince zata auri Saurayi dan gaye, dan zamani, to babu abin da zai hana in aureta. Wannan wata dama ce a garre ni. To amma Kuma ta ce wai sai mijin ta ya mutu, sannan zata sake yin wani auren, sai yaushe wannan mijin nata zai mutu? . Nayi saurin dakatar da tunanina, na tambayata. . "Zubaida kin san lkcn da zai mutu ne da zaki fadi haka? Me yiwuwa ya qara lkc mai tsawo ba ki sani ba..." . Ta yi murmushi a karo na farko tun sanda ta kammala bani labarin hadarinsu da mijinta. Sannan ta juyo ta dubeni muka hada ido. Duk dna uban kukan da ta ci idanunta Suna nan tarwai farare. . "Kada ka yi mamaki don na fadi haka mansur, mijina ya kusa mutuwa, don likitoci sun aunashi, Kuma sun fadi mani iyakar adadin kwanakin da zai iya qarawa a duniya." . Zubaida ta miqe sannan ta jawo gyalenta ta dora a saman lallausan gashin kanta, ta ce da ni. . "zan koma daki in kwanta mansur, na gode sosai da 6ata lkcn ka da kayi ka saurare ni, Kuma na gode da shawarwarin da ka bani, sai da safe." . Zubaida ta nufi qofar dakin cikin taqama, na miqe cikin sauri na bi bayanta na ce da ita. . "Zubaida baki fada min lkcn da likitoci suka ce zai qara a duniya ba." ki fada min don allah, kwanaki nawa likitoci suka ce zai qara a duniya?" . Zubaida ta dafa qofar dakin da hannunta sannan ta juyo da fuskarta ta dubeni, ina kidime cikin qosawa, ta yi min murmushin soyayya sannan ta ce da ni. . "Kada ka damu mansur, ba wani lkc mai tsawo suka ce zai qara ba, sun yi min albishir mai kyau. Sun ce mijina ba zai wuce shekara talatin ba a duniya . Zubaida ta fice ta barni a tsaye kamar an dasa ni, naji sautin tafiyarta a cikin sauri a lkcn da ta nufi dakinta.. Har xuwa lkcn da na daina jiyo tafiyarta qwaqwalwata a rikice take, kamar Wanda aka yi wa albishir da xuwanka barzahu. . . ** ** ** . . Akwai wani zamani da ya wuce kafin in fara ganin kyakkyawa Zubaida, an sha fada min cewar soyayya ta kan san mutum ya fita hayyacinsa, idan Kuma abin yayi nisa wasu an ce har haukacewa suke yi. An sha fada min cewar Sauran da yawa akwai mutanen dake fadawa tarkon soyayya har su aikata abin da ba a yi tsammanin mutum mai hankali zai aikata irin shi na. . A zamanin da naji zantukan ban amince da su ba." ni a tunanina haukar soyayya ba gsky bane. Ban ta6a yarda cewar mutum zai iya fita a hayyacinsa ba don kawai son wata mace. . To amma Kuma a halin ynx da son wannan kyakkyawar mace Zubaida ya kama ni, bani da wani aiki dare da rana sai tunaninta, sai na fara tunanin haqiqa nayi kuskure a shekarun baya, sannan Kuma na yi wa soyayya mummunar fahimta, a halin ynx kam na san yadda soyayya take burkita tunanin ma'abocin yin ta, kamar yadda ta burkita nawa tunanin, gashi ynx idanuna sun makance Zubaida kawai nake son in gani a duniya. . Duk wannan tunanin nayi shi ne a lkcn da nake tsaye a cikin dakina ina tunanin maganar da Zubaida ta sanar da ni, sannan Kuma ta fice ta barni a cikin xullumi da wasi-wasi . Wannan maganar da ta sanar da ni ba wani albishir ba ne mai dadi. Sai dai in kira maganar da Suna [Mugun Albishir] . Haqiqa wannan mugun albishir ne, don kuwa idan har a cewarta ba
Chapter 12 · 0% Book details