Sashe 8
Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
da suka wuce fuskarta mai cike da annuri tana nan wasai, ta qara annuri da kwarjini. Na tuno ranar farko da muka fara haduwa a makaranta. . "yaya sun ka.." Na tuno daddadar muryarta mai kama da dorewa. . Kafin in dawo hayyacina ne Alh. Bashir ya yi min dariya sannan ya ce da ni. . "ita ce matata da nake baka labarin ta mansur, Kuma gaisa mana. 'yar garinku ce, a dariya na aurota, sunan ta Zubaida!! . . Lp=12mugun albishir Page 12 . . Daga alqalamiN Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan bn ishak . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . . "yar garinku ce, a zariya na auro. Sunan ta Zubaida!!" . . . ** ** ** . . Ganin kamar a fusace take sai Alh.Bashir ya ce mata. . "Kada kina damu Zubaida wannan yaro ne mai ladabi. Don baki san shi ba ne, amma Kuma kema zaki gani da idon ki, shi ne sabon direban da na samo miki. Duk inda zaki je kina iya fadi mashi, nafi son ya riqa tuqa ki, bana son kina fita ke kadai." . Zubaida ta yatsina fuskarta sannan ta wuce ba ta yi magana ba, ta bude wata qofa dake a cikin falon ta shiga ciki. . Alh.Bashir ya ce da ni. . "Kada ka damu mansur, haka take da saurin fushi, amma zata huce ne daga baya. Kayi haquri da halinta ni ma haka nake haquri." . Nayi ajiyar xuciya, sannan na share xufar dake a fuskata, don kuwa ji nake yi kamar fatalwa na gani ko aljana. Naji soyayyar Zubaida ta sake taso min a xuciyata. Na sake tuno ranar qarshe da zamu rabu a makaranta. . "yau Kuma ranar rabuwarmu ta zo mansur, mu yafewa juna, sai wata rana..." . Da Alh.Bashir ya ga ta dade a cikin daki bata fito ba, sai ya qwala mata kira da qarfi. Zubaida bata amsa ba, ta fito cikin damuwa,,ta sauya kayan dake jikinta, ta sako wata doguwar riga fara da Kuma dogon siket mai qyalqyali kamar jikin macijiya. Ta xubo da gashin jikin ta kan kafadunta kamar balarabiya. Hakan shi ya sake tuno min da ranar da ta xo wurina ta zauna tana yi min murmushin farin ciki. Da xuwanta ya ce da ita. . "ki tafi dashi ki kai shi dakin da zai riqa kwana, ki yi sauri ki dawo ina son ganin ki." . Zubaida ta wuce gaba, na yi sauri na tashi guiwa ta Babu qwari na bi bayanta tana tafiyar a cikin taqama, muka fita daga falon, naga ta bude wata qofar, muka nufi dakin da za a saukeni. Da shigarmu dakin naga ta juyo ta dube. Muka qurawa juna idanu a lkc guda. Ta ambaci sunana da zazzaqar muryarta. . "mansur!" . "na'am, Zubaida?" . Ta sake ce min..." . "baka samu aiki ba ne tun lkcn da muka gama makaranta me kake yi?" , Nayi ajiyar xuciya, don kuwa ban san abin da ya dake in ce da ita ba." to amma Kuma ai gashi ynx na samu, Kuma na samu masoyiyata da nake ta faman neman ruwa a jallo. Muna nan a tsaye ni da ita.mun yi cirko-cirko a cikin dakin muna kallon juna, sai muka ji mijinta ya fara daka tsawa a fusace. Da yake daga cikin dakin idan mutum ya tsaya a jikin taga zai iya hango komai na cikin falon alhaji ta hanyar wagegiyar tagar falon. Alh.Bashir ya sake daka mata tsawa. . "Zubaida me kake yi ne a dakin? Ba cewa nayi ki kai shi ki yi sauri ki dawo ba? Uban me kuke yi ne a dakin?" . Zubaida tayi sauri ta fice a tsorace. Nayi mamakin ganin yadda take jinjinawa Tsoron shi sai ka ce ba gurgu ba." to amma Kuma da nay la'akari da tarin mmilyoyin kudin da ke shaqare a gidan da kayan alatu burjik a ko ina, bai kamata in yi mamaki ba don ta ji Tsoron shi. .