Sashe 3
Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
. "allah yasa muyi aure in zama maTarka." . Sai yaushe Zubaida zata sanar da ni wannan kyakkyawan albishir na so da qauna a duniya? . . . ** ** . . Sannu a hankali sai na fahimci Zubaida tana da matsayin da aji da ko kusa ni ba Abokin rayuwarta bane, don kuwa da xuqa-xuqan motoci take xuwa na milyoyin kudade, sannan Kuma da wahala ta sanya kayan a jikinta ta sake maimaita su. . . Lp=4Mugun albishir Page 4 . . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan bn ishak Madugun taska "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar wannan shafin ba." . . . Kullum kayan da take xuwa dasu kala daban ne na alfarma, wadanda yawancinsu lesuka ne na manyan mata da Kuma manyan atamfofi masu tsadar gaske. na san cewar ko sarqoqin da take yawa sun ishe ni hidimar karatu a rayuwata. don haka Zubaida ta fi qarfin, amma Kuma Kullum qara son ta nake yi, Kuma Kullum ina addu'ar ta zama matata, idan so samu ne. . Kwanaki suka yi ta xuwa Suna wucewa, watanni Suna biyo Bayan su, shekara daya Bayan daya har muka yi shekara uku a haka tare da Zubaida Kullum da sonta nake kwana nake tashi a xuciyata. Amma Kuma ita bata sani ba." wani abin takaici Kuma shi ne a cikin shekaru uku da muka yi tare da Zubaida an samu raguwar alaqar mutuncin da muke yi ni da ita. Sau da yawa sai mu hadu da ita a wani lkcn ma ko kallon inda nake ba zata yi ba, sai dai ni da nake binta ina yi mata magana, don kuwa na fadi maku duk ranar da ban ganta ba, Babu Sauran kwanciyar hankali a xuciyata . Sannan Kuma a cikin shekaru uku da muka yi ban san takamaimen gidansu ba, Kuma Babu Wanda nake tsammanin ya sani a cikin daliban ballantana in tambaye shi. Don kuwa Zubaida bata cika baiwa mutane fuska Suna doguwar magana ba." Babu Wanda zai ce ya san gidan su, ko Kuma ya ce ya san ko ita "yar wace ce a birnin zariya. . Rayuwata bata sake fadawa a cikin xullumi da tagayyara ba sai da lkcn jarrabawarmu ta qarshe ya xo. daga ranar Kuma shi kenan mun yi bankwana da juna, mun gama makaranta, ba zamu sake xuwa mu hadu da junanmu ba, sai dai Xiyara. Dalibai 'yan kwana Suna ta farin ciki da xuwan ranar qarshe, zamu gama jarrabawarmu amma Kuma ni baqin ciki nake yi, don kuwa lkcn rabuwa da masoyiya ta yayi. . Na san cewar idan muka rabu shi kenan, wata qila Kuma har abada ba zan sake ganin Zubaida ba." me yiwuwa ma ba zamu sake ganin juna ba." idan Zubaida tayi kwana daya bata xo makaranta ba, ranar rashin lfy nake yi sbd ban ganta ba, gashi Kuma ynx zamu rabu rabuwa ta har abada. Anyya kuwa zan iya rayuwa ba tare da wannan masoyiya tawa ba?" . Da ranar kammala jarrabawarmu ta zo ban yi barci ba, kwana nayi a zaune ina xullumi Wata xuciyar tana raya mani cewar ya kamata in cire fargaba in sanar da ita cewar ina sonta. Don kuwa idan muka rabu ban sanar da ita ba, ban san inda zamu sake haduwa ba." . Ka shaida mata kana sonta mansur, ko banza dai yafi ace ka bar abin a iya xucyarka ba tare da ta sani ba." koda kuwa ace ba zata amince ba, ta san cewar dai kana sonta, Kuma duk inda take a duniya ita ma zata riqa tunaninta a matsayin masoyinta. . Da wannan shawarar na tafi makaranta a raina, ina ta mamakin irin wannan soyayya da ta cafi xuciyata.tun a ranar farko da muka fara karatu na fara sonta, gashi Kuma ban sanar da ita ba sai ynx a ranar mu ta qarshe da zamu rabu. Shekaru uku cur ina tfama da ciwon son ta a raina, Babu Wanda ya sanin ballantana ya taimaka mani ya jefi-jefi ya sanarwa kyakkyawa Zubaida . Bayan mun fito jarrabawarmu dalibai Suna ta gaisawa da juna, kowa yana neman dan uwanshi don a yawa juna Tunda dai rabuwa ta zo, ni Kuma sai nayi sauri na garzaya na bi Zubaida a guje, da na hangeta ta kama hanya ta tafi inda motarta take zata tuqa ta tafi. Na sha gabanta ina numfashi da qyar kamar raina zai fita. Muka hada ido ta yi mani murmushi sannan ta ce da ni. . "mansur ban ganka ba sai ynx, yau Kuma ranar rabuwa ta zo, mu yawa juna sai wata rana." . Na tuno ranar da muka fara haduwa a makaranta, shekara uku da suka wuce, sannan na sake tuno magana da ta sanar da ni da ke 6oye a dodon kunnena tsawo lkc. . "sannunka. ga alama kaima irina ce baka son yawan surutu, shi yasa ka zo ka zauna...." . Na ji hawaye sun tarar mani a idanuna, qwalla ta cicciko mani, nayi sauri na share hawaye na ce da ita cikin qarfin hali. . Yawan comment dinku shi ne kuzarina wajen sanqamo Page 5mugun albishir Page 5 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan bn ishak . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba. . Naji hawaye sun taru a idanuna, qwalla ta cicciko min nayi sauri na share hawaye na. Na ce da ita cikin qarfin hali . . "haka ne Zubaida yau ce ranar mu ta qarshe a makarantar nan, daga yau Kuma sai yaushe kenan zamu sake haduwa, ko kina nufin mun rabu kenan har abada? . Zubaida tayi dariya, ga alama bata fahimci irin matsanancin halin da rayuwata ta shiga ba." tayi mani farin da fararen idanunta sannan ta ce da ni. . "gsky mansur bana tsammanin zamu sake haduwa har abada . Tayi shiru tana tunanin wani abu. A yayin da ni Kuma na qarawa kyakkyawar fuskarta idanu. Wata xuciyar ta fara yi mani kururuwa. . "ka fadi mata kana sonta mansur, kayi sauri ka sanar da ita, sbd daga yau ta ce ba zaku sake haduwa ba a duniya har abada!!! . Kafin in dawo hayyacina in ce da ita wani abu ne, sai ta ce da ni cikin farin ciki. . "Akwai wani albishir mai dadi da zan sanar da kai mansur, Wanda ba kowa ne ya sani ba a makarantar nan, na san cewar zaka yi farin ciki, ina nufin zaka taya ni farin ciki. . Naji farin ciki ya kama ni. . ...."wane irin albishir ne Zubaida fada min..." . Na ce da ita cikin zaquwa, don kuwa ni a shirme na tayi tsammanin ina matuqar sonta ne, shi yasa ita ma zata sanar da ni cewar tana sona. . Zubaida ta duba agogo sannan naga ta dan 6ata rai. ta ce da ni kai tsaye. . "kai kada in 6ata maka lkc mansur, nima sauri nake yi, dama ba wani albishir bane, so nake yi dama ka taya ni farin ciki, ina gayyatarka xuwa daurin aurena a wannan asabar din mai xuwa. Na sami miji zan yi aure." , Naji kamar ta watsa min garwashin wuta a fuska. . . . ~~~~~~~{ mugun albishir }~~~~~~~~ . . . Kowanne dan adam a duniya Akwai abubuwa da dama da suka fi bashi sha'awa a rayuwarsa. Alal misali wani shi a rayuwarsa yafi so yaga an yi ruwan an dauke, ni'ima ta wadaci ko ina a duniya, ana busa sassanyar iskar damina. . Wani kuma shi a nasa 6angeren yafi son ya ji ana zafi, don kuwa a irin wannan lkcn yafi walwala da nishadi tare da Sauran bani adamu. Wani kuma yafi son ya wuni yana yawo bashi a nan bashi a can. Wani kuma shi in har zai samu ya kwanta ya wuni yana barci, to duniya ta yi masa dadi koda kuwa bai samu abin da zai jefa a bakin salati ba." . Ni kaina ina da irin wannan buqata kamar Kowanne dan adam. To amma Kuma Babu mamaki ni a nawa 6angaren abin da nafi so ya banbanta da na Sauran mutane. Na san cewar mutane da dama zasu sha dariya idan na shaida masu cewa a rayuwata nafi so in zauna a daki ni kadai tun safe har dare ba tare da nayi magana da kowa ba." . A cikin irin wadannan ranakun da na samu wannan gara6asar ta zama ni kadai a yammacin wata lahadi ba zato ba tsammani sai naji sallamar wani yaro mai qirar wayayyu dan kimanin shekaru bakwai a dai dai qofar dakina. Tun kafin in amsa sallamar ya sa hannu ya yaye tsumman labulen dakina Wanda yayi fata-fata kamar kallabin mahaukaciya. . Muka hada ido ni da yaron, ina zaune ina gyaran wata tsohuwar rikoda tawa, wacce Kullum sai na dirka mata dundu Sau ba iyaka, sannan nake samu in ji labaran duniya. . : "wai an ce ka xo ana kiranka a waje." . Na dubi yaron cikin damuwa, ganin irin kallon da nayi mashi naga ya dan jawo baya a tsorace. To amma Kuma wata qila ba kallon da nayi mashi bane ya tsorata shi, Babu mamaki tsohuwar rikodar tawa ya gani ya furgita, don kuwa ko ina a taskar dakina kayan cikinta ne falle-falle kamar an fede akuya. Amma Kuma duk da haka sai faman 6urari take yi da tsuwa a natalie tsammanin waqar fina-finan hausa take yi. Na ce da yaron. . "wane ne ke kira?" . Ya ce da ni. . "maman bose ce. . Maman bose? Na tambayeni kaina. Lallai Babu lfy. Don kuwa na san abin da ya kawota. na xurawa yaron idanu. Na ce dashi. . "ka ce da ita bani nan...ka ce da ita baka ganni ba." . A dai-dai lkcn da nake yiwa yaron burga ne, kakata ta fita daga dakinta dake kusa da nawa, tana dauke da bata zata yi alwala. Ta ce da yaron. . "kai je ka ce gashi nan xuwa ka ji ko? . Yaron ya garzaya waje da gudu bayan ya ce. . "to." . Nan da nan ta fara yi min sababin da ta saba tana cewa. . "sakarai, mutumin banza, kai dai mansur ba zaka ta6a jinjinawa nasiha ba."