← Book details Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 21

Sashe 16

Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

zan fito komai dadewa, ina fatan zata riqe min alqawarin ta jira .ni. Zubaida ta yi min murmushin Kada in damu. Zan jiraka masoyina, komai dadewa ina nan ina jiranka. Na gode sosai da soyayyar da ka nuna min, ka fansar da rayuwarka a kaina. . 'yansanda suka buga min ankwa a hannuna da qafafuwana, suka iya qeyata suka raba ni da masoyiya ta Zubaida da muke kallon juna, suka yi waje da ni suka bude mota suka ingiza ni ciki. Motar ta fara tafiya da ni xuwa wata duniya ta mutanen da basu da 'yanci a rayuwarsu. Har tayi nisa xuciyata cike take da farin ciki. Don kuwait a qalla ban tozarta masoyiya ta Zubaida ba." shekaru goma Kuma basu kai shekaru talatin yawa ba, na san cewa Zubaida tana so na Kuma zata jira ni in gama zaman gidan yarin in fito muyi aure. . Motar ta wuce da ni saitin wata makaranta inda wasu yara qanana ke wasan qwallo cikin farin ciki, Suna sanye da kayan makaranta iri daya. Yaran suka dagowa motar hannu kamar sun san ina ciki ina kallon ta ggilashi. Duk da yake basu ganni ba, sai da na daga masu hannu nima na ce dasu a xuciyata . "allah ya kare Ku da sharrin soyayya idan girma yara." . . *************************** . Bayan shekara goma. . Wata azababbiyar bulala dake kama da Fatan giwa ta ratsa gadon bayana. Na farka a gigice babu shiri, a lkc ne na ganshi a tsaye a kaina riqe da doguwar bulalarshi kamar Kullum. . Na dube shi a fusace bayan na wartsake daga barcin, yana tsaye yana murmushin mugunta da yamutsattsiyar fuskar mai kama da fasasshen tumaturi. . Da azzalumin gandiroban ya ga na tashi sai ya mayar da hankalinshi akan sauran abokan kwanana da muke cunkushe a daki daya mu shida kamar kifayen gwangwani. . Lp=25Mugun albishir Page 25 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." , Da azzalumin gandiroban yaga na tashi sai ya mayar da hankalinshi akan sauran abokan kwanana na da muke cunkushe a daki daya mu shida kamar kifayen gwangwani. Haka gandiroban ya bi su daya bayan daya yana tsala masu bulalar Suna farkawa a furgice, don kuwa idan ya fara dukan mutum in har ba farkawa yayi ya tashi ba, to ko bulala dari zai yi masa ba zai gaji ba, duka ne dashi tamkar Zazza6i. . Bayan mu duka mun farka daga barci, sai azzalumin gandiroban ya dube mu a lkc daya, sannan ya ce. . "na san cewar ynx kun gama wartsakewa." . Muka gyada kawunanmu cikin fushi kamar qadangaru. Don kuwa duk da yake xuciyarmu ta bushe sbd wahalar gidan, to hakan bai hanamu tsoron wannan gandiroban ba, Wanda a shekara goman da nayi a gidan yarinn, tun xuwa na shi yake bin dakunan fursinoni yana tashin su daga barci idan safiya tayi. . Wannan gandiroban da yake tashinmu daga barci ya fi duk Sauran ma'aikatan gidan yarin baqin jini a wurin mu. Don kuwa duk lkcn da muka kwanta barci bamu son wani abu ya tashe mu, sbd wuni muke yi muna shan wahala tun safe har dare. A haka muke kwantawa barci a gajiye da tsamin jiki, muna cikin barci Kuma babu zato babu tsammani sai mu ji saukar duka, da zarar mun ji haka mun san cewar gari ya waye kenan. . Gandiroban ya nannade doguwar bulalar ya sa6ata a kafadar shi kayan qato guda, ya ce da mu. . "ya kamata wanda zai yi sallah ya je ya yi, wanda Kuma ba zai yi ba ya je ya dauraye fuskar shi, yau tun da wuri zamu fita aikin fasa dutse." . Ya fice ya bamu wuri, mun yi shiru muna tunani, muna jin shi ya shiga wani daki Wanda yake kusa da mu. Muka ji qarar saukar bulalar shi a kan wasu irinmu da tsautsayi ya fado mawa suka xo gidan yarin, ko da yake wasu ba za a ce tsautsayi ya kawo su ba, wasu ganganci ya kawo su, da Kuma hadama da neman duniya. . Sauran abokan kwanana su biyar da muke kwana tare a cunkushe shekara da shekaru, sun bani labarin abubuwan da suka yi aka kawo su gidan yarin. Bangis da Gambo riqaqqun 'yan fashi ne da suka dade Suna daukar rayukan bil'adama. Sada dan damfara ne, Dumfama Kuma safarar miyagun qwayoyi yake yi. Jabiru shi ne mai dan dama-dama a cikin su, satar mitar wutar lantarki ya ce yana yi a gidajen mutane kafin dubun shi ya cika. . Ni kadai ne azal ta fado mawa, a lkcn da na basu lbrn cewar ni wata masoyiya tawa na fanshi laifinta don Kada a yanke mata hukuncin kisa, gabaki daya shu'man mutane biyar din da na taras a dakin sai da kowa ya yi min mari goma-goma. Bangis ne ya riqe ni da tsiya suka yi layi Suna wanke min fuska da busassun hannayensu dake kama da bayan Kada. Bayan sun gama kumbura min fuska sai Bangis ya ce da ni. . "ka san abin da ya san muka hora ka?" . Na girgiza kaina cikin tsoro, don kuwa a lkcn ni baqo ne ban saba dasu ba." Bangis ya ce. . "ka 6ata mana rai mansur,don kuwa mu biyar din nan da ka gani, mu duka jarumai ne....! kowa akwai gagarumin laifin da yayi aka kawo shi nan... Amma kai ka rasa abin da zaka yi na arziqi sai soyayya? Akan mace za ka zo gidan yarin?" . Na ce dasu. . "ina matuqar sonta ne shi yasa. Bana son wani abu ya same ta...." shi ya same na gwammace ni a yi min hukuncin da za a yi mata.." . Ragowar'yan fursunan suka kashe da dariya. Dumfama ya ce da ni. . "lallai kam baka da hankali mansur. Baka san halin mata ba." domin kuwa duk da wannan halaccin da ka yi, to zai yi wahala ta riqe maka alqawarin. Can zata je ta sami wani ta aura ta mance da kai, kana nan kana shanta wahala. Ka yi kuskure mansur." . Jabiru ya ce da ni. . "Sau daya na ta6a yin soyayya a duniya mansur....na wata bebi ce dake a layinmu, wacce muka yi alqawarin aure ni da ita. Na sha wahala ina nemo abin da zan aureta, har garinmu na bari. Amma lkcn da na dawo Bayan na samo abin da zan aureta, sai na sami labarin ta kaI wata biyu a dakin mijinta. Tun daga lkcn na daina soyayya a rayuwata."
Chapter 16 · 0% Book details