Sashe 4
Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ace Kullum aka zo gidan nan yin sallama da kaI sai ka ce ace baka nan...ka ynx mutane ashe ba rahama bane mansur....ina amfanin wannan shashancin da kake yi a gidan nan?" . Na riqa na saba da halinta, in Sau dari za ayi sallama da ni, in har tana gidan to ban isa in ce bani nan ba." to amma Kuma a zahiri irin wannan ziyara da Maman bose mai shago ta kawo man Babu alheri a cikinta, ba rahama ba ce, don kuwa na dade ina yi mata qarairayi ina amsar bashin kayanta dake a shagon layinmu. Babu shakka yau ta gaji ne shi yasa ta biyo sawu na. . . Ina jiran tarin comment dinku kafin in watso page -6 mugun albishir Page 6 . . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan bn ishak . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba. . . Wata qila yau ta gaji ne shi ya sa ta biyo sawuna har gida don ta tsare ni in biyata kudinta, gashi Kuma tsawon wunin yau ko qwandala ban gani ba ballantana in mallaketa a Aljihuna. Don haka ya rage nawa in san yadda zan da wannan mafadaciyar bayerabiyar dake a qofar gida tana jira na. Na ci sa'a ma da ba ta shigo har cikin gidan namu ba." don kuwa bana son kakata juma ta san halin da ake ciki. . Na tashi gabana yana haduwa na tsallake rikodar da nake gyarawa, na fita waje ina wasi-wasi ni kadai. Na wuce juma tana alwala tana surutai ita kadai. . "in ba lalata ba." a kira ka amma ka ce wai a ce baka nan. Baka san alherin da yasa aka xo neman ka ba, iirin wannan ke sa mutum ya 6arar da qoqon furar arziqinsa da kan shi bai sani ba." . Ni dai ban ce mata komai ba, don kuwa abin dake damuna a raina ya ishe ni. Wani lkcn na kan biye mata mu wuni muna jayayya ni da ita. To amma ban da irin wannan lkcn da Maman bose ta xo ta ritsa ni. . Da fita ta qofar gidan na same ta a tsaye tana ta kumbura tana sacewa, kamar anan qara mata iska da fanfon mota, kumatunta sun kumbura kamar kwallon kafa . 'yar gajera ce dunqulalliya wacce ba Kowanne qato zai iya kayar da ita ba idan za ayi kokuwa. Na tsaya baya na jingina da qofar zaurenmu, sannan na lalubi wani murmushi na musamman Wanda yawanci bana yin irin sa sai rana ta 6aci in an zo an tsare ni in biya bashi, ni Kuma bani dasu. To amma Kuma a wannan karon murushin nawa bai yi rana ba, don kuwa matar bata saki ranta ba." Maimakon haka ma sai ta sake hade fuska kadan ake iya ganin idanunta dake 6oye a cikin loko. Na ce da ita. . "Maman bose manyan gari ...ashe ana ganin Ku haka..." . Ta daka mani tsawa a fusace ta dakatar da ni ba tare da na shirya ba." . "kada ka raina min hankali mansur ni ba wannan ya kawo ni ba..na zo ne ka biya ni kudina, na gaji da qarairayi da kake man. Kwanaki da na ganka ka ce min shekaran jiya zaka bani. Shiru-shiru baka zo ba, jiya Kuma ina hangenka ka zagaye baka biyo ta qofar shago na ba don Kada in tamvayeka. To ynx na biyo ka gida Tunda baka da niyyar biyana, ko an ce maka ni a banza nake debo kayan a kasuwa? . . Ku yi haquri da iya wannan. Sai mun hadu a page 7Mugun albishir Page 7 . . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa .